← Book details Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 114

Sashe 89

Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Shi da kansa ya ɗebo plates ɗin da spoons bayan ya wanke su, ya zauna a ransa yana faɗin (Bari muci girkin ƴar madara muji). Da tea ya fara, lokacin da ya kai dankali da source ɗin ƙwai bakinsa sai da ya lumshe idanunsa. Wannan fa shi ake kira kama da wane bata wane, UBANGIJI mai rahama. UBANGIJI mai jin ƙai da baya haɗama bawa zafi biyu, idan ya jarabceka ta nan sai ya sauƙaƙa maka ta can dan kaji sanyi. A duk inda kaga mutum da halayya mara ƙyau kar ka yanke masa hukunci da ɗari bisa ɗari ɗin munanan ayyukansa, UBANGIJI shine kaɗai yasan abinda ke cikin zuciya da sirrikan ɓoye ga bayinsa. Ita dai a zahirinta duk wanda ya ganta suna ɗaya zai bata, amma a baɗininta sai UBANGIJIN da ya halicceta ya san kayarsa, sai ko wanda ya ƙaddara ya santan kamar dai shi mijinta a yanzun...
      Yana gab da kammalawa ta fito, sai dai yitai kamar bata gansa ba ta zauna a falo ta ɗauka laptop ɗin ta ta cigaba da aikinta na ɗazun batare da kallon ko inda yake ba ko sau ɗaya. Shi ko dai sai satar kallonta yake time to time. Koda ya kammala sai ya ɗibo farfesun kifin cikin dauriya dan baya son kifi shi sam da tea ya nufota, ƙaramin coffee table ya jawo gabanta ya ajiye, ƙamshin kifin ne daya dakar mata hanci ya sata ɗagowa, harararsa tai ƙoƙarin yi yay saurin faɗin, “Ni dai tausaya min da hararar nan gidan ma zan bar miki karki lashe ni Ammah ko yaye ni batai ba”.
     Hararar tasa dai tai ta ɗauke kai, sai kuma ta sake ɗagowa ta dubesa, karan farko ta saki murmushin da ke bayyana beauty point ɗinta da farare haƙoranta, ga wanda ya santa a kallo ɗaya zai fahimci na mugunta ne, saboda bata murmushi sai ta so, wanda kuma bai santa ba zai ɗauka yinsa matsayin birkita kwanyar duk wanda ya kalletan ne. Girarta a sama ta ce, “Waye zai fitan? Ka manta yau a gidan nan babu shiga babu fita? Ai duk yanda ka dama haka kowa zai sha wlhy. Ta miƙe ta nufi hanyar bedrooms. Da kallo kawai ya bita na mamakinta ne ko na son ƙarin bayani akan maganar tata ne oho masa. Yana a wajen harta da dawo da keys a hannu, a kallo ɗaya ya gane na ƙofar falon ne da ƙofar kitchen ta baya. Sai da takai zaune sannan ta tura su cikin rigarta a gaban idonsa ta gyara tana ɗaukar tea ɗin da ya ajiye mata ta kai baki.
           “Idan ma wasa kike ki daina. Uncle Yousuf fa ke jirana tare da Yaya Abdull-Hameed”.
       “Oh really?”.
     Ta faɗa cike da rainin wayo. Hannu ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya kai zaune a kusa da ita cikin lallashi ya ce. “Mawaddat Please seriously wlhy jirana akeyi, babu jimawar nan yay kirana kuma important ne zuwa 12”.
        Batama ko kallesa ba balle ta tanka masa, sai ma kifinta data fara ci a hankali tana wani lumshe idanu taba banza ajiyarsa. Rasama mi zaiyi yay, cikin son ta fahimta yay ƙoƙarin kamo hanunta ta balla masa harara. “Karka kuskura hannunka ya kai jikina. Ka kuma kiyayi yin hakan inba haka ba kasha mamakin sanin ainahin Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. Kasan bazaka iya ƙarasa wasan ba miyasa ka fara? Common ƙyaleni bana buƙatar hayaniya, ba kace da ni zaka buga game ba? Muje zuwa”.
       (Tana mun magana kamar wata lady boss) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam kansa kawai ya dafe. Abu tamkar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa har 12 tayi Lulu bata da niyyar bama Smart key ɗin nan, zuciyarsa na raya masa ya turmuzeta ya amsa amma yana gargaɗin kansa karta tada masa aljanu, dan yasan mata da iya aljanu. Sha biyu da kusan kwata kiran Uncle Yousuf ya shigo masa. Ya ɗaga ya gaida shi da mutuntawa kamar yanda ya saba. Da ga can Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu yaya dai? Kai muke jira na ga har 12:15?”.
      Ɗan kallon Lulu da ke ta aikinta a laptop tana zuba murmushin mugunta yayi, a can ƙasan maƙoshi ya ce, “Uncle ta kwashe keys ɗin ne fa, wai tunda na hanata fita nima babu inda zanje”.
           “What! Mawaddat ɗin? Kaga bata wayar Please bana son shiririta”
Maimakon bata sai ya saka a hansfree yanda zataji, kiran sunanta da Uncle Yousuf ɗin yay ya sata ɗagowa ta kalla wayar, sai kuma ta amsa da “Yes Papa good afternoon”.
       “Afternoon Dear. Miya faru kika hana Aliyu fitowa ga shi munata jiransa?”. Murmushin muguntar da take ta faman yi tun ɗazun alamar duniya ta mata daɗi ta sake saki da faɗin, “Uncle You shi ya zaɓi hakan ai, dan haka ka manta da shi kawai, dan yanda ya hanani fita sai dai mu yini tare a gidan.”
     “Mawaddat Please!!”
“Uncle please”.
         Ta faɗa itama kamar yanda yayin tana tura baki. Kai kawai Uncle Yousuf ya dafe da ga can, yayinda Coach ke kwasar dariya dan Smart ɗin kawai ya ke hangowa, kai mace daban ce, yo inba mace daban take ba Smart ɗinsa ne da ya sani mai tsaurin nan da rashin son magana za'a kullema ƙofa a hanashi fita. Aure aunre yayi. A ɓangaren Uncle Yousuf kam iyakar lallaɓa yay ma Lulu tafa ce ba gudu babu ja da baya, har ya koma faɗa amma tai biris, ba komai ke tunzurata ba kuma sai ganin yanda fuskar Smart ta fara canjawa da dauriyar da yake zuwa ɓacin rai. “Uncle bye”. Ta ce cikin siririyar dariya tana miƙewa tare da laptop ɗinta da wayoyinta tabar falon ma tana ɗagawa Smart yatsu biyu na ƙularwa ta ce, “2-1 ka shirya yin game over gaba kaɗan”.
      Wani irin bahagon iska ya furzar da ga bakinsa yana mai dafe kansa. Da ga can cikin tunzura shima Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu wai yarinyar nan tafi ƙarfinka ne da karɓar key a wajenta ya gagareka. Be a man mana Son”.
         “Uncle bazaka gane bane wlhy, yarinyar nan azababbiya ce, tafa saka key ɗinne.....”
    Sai kuma yay shiru fahimtar ɓaranɓaramar da yake neman yi. Uncle Yousuf zai sake magana coach ya katsesa da faɗin, “Kaga ƙyaleta muje mu samesa a can kawai nikam, dan amarya dai bata laifi koda ta kashe ɗan masu gida. Zakina jiramu karka damu”.
     Kafin Smart ya ce wani abu an yanke wayar, sai kawai ya girgiza kai. Wannan ma sauƙin kan na Coach ya sa yake sake jin ƙaunarsa a ransa. Mutumin nan shi na musamman ne a garesa, dan ya taka rawa kala-kala a cikin rayuwarsa da har abada bazai manta ba........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣2️⃣

.........Cikin mintuna da basu wuce ashirin ba sai gasu sun iso, jin horn ɗin su da kiran da Coach yay masa ya ce gasu sun iso ya saka shi miƙewa ya nufi bedroom da ta shige. Fuskarsa babu walwala da ga bakin ƙofar ya tsaya yana kallonta da faɗin, “Sun iso Please ki kawo naje na buɗe musu”.
      Ɗagowa tai ta ɗan hararesa da maida kanta tana taɓe baki, “Oh wai har yanzu kana tunanin amsa cikin sauƙi ko min wayo? To anƙi a bada ɗin na ƙarfi ne”.
          Kaɗan ya cije lips ɗinsa da jin jina kai yana wani ɗan murmushi, dan ya fahimci sai yayi abinda tun ɗazun yake hana kansa yi sannan. Takowa yay zuwa gaban gadon tare da kaiwa zaune cikin lallashi ya ce, “Mawaddat su Uncle Yousuf ne fa, kuma na faɗa miki magana mai muhimmanci zamuyi....”
      “Nima ai aiki da zan fita yi mai muhimmanci ne ka sani. Gara ma ka bar wani sauke murya ba badawa zanyi ba ehe”. Ta juya ta cigaba da aikinta.
       Lips ɗinsa ya sake cijewa da faɗin, “Amma kin san zan iya amsar key ɗin a duk ta yanda naso ko?”.
         A gatsine ta ce, “To ƙarɓi ɗin mana”.
    “Haka kika ce?”.
         Shiru ta masa kamar bata ji ba, sai ma faman murmushin ta take tana sarrafa system ɗin gabanta cike da ƙwarewa dan charting take yi da wata friend ɗinta ƴar ƙasar Hong kong da sukayi karatu a America tare. Laptop ɗin gaban nata ya janye gefe tare da birkitota, zabura tayi dan batai zaton zai yi yunƙurin amsar ba, sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya danneta da rabin jikinsa ya riƙe hannayenta duk biyu a cikin nasa. Rawa jikin nata ya fara yi saboda yanayin na neman maimaita kansa ne da abinda ya shuɗe, amma cikin ƙoƙarin dakewa ta ballara masa harara. duk da shima ya fahimci hakan bai bi takanta ba sai ma baki da ya taɓe da sakin murmushin nan nasa data raɗa ma suna na rainin hankali cikin kashe ido ɗaya ya ce, “Zaki bayar da arziƙi kona ɗauka?”.
Sosai ta waro idamunta da suka cika da ɓacin rai ta ce, “Saboda kai ɗan is.....”
Baki ya taɓe da faɗin, “Oh ɗan iska ko?” sai ya ƙara ƙasa da murya yana kai bakinsa jikin kunnenta ya raɗa mata, “Dole ne ma nayi iskancin nan dan banzan amsa sunan nan a banza ba”.
“Aliyu!!”
Ta faɗa tana zaburowa gaba ɗayanta sai dai har ya riga ya tura hannunsa a rigarta ya ciro key ɗin. “3-1 Madam” ya faɗa yana sakin mata hannu da ɗagata murmushin mugunta fal fuskarsa ya nufi ƙofa ya fice harda mata gwalo.. Rumtse idanunta kawai tai da masifar ƙarfi tana ƙoƙarin dai-daita numfashinta dake rawa a maƙoshi......
Chapter 89 · 0% Book details