← Book details Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 114

Sashe 53

Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an idar da salla kusan a tare suka fito. Uncle Yousuf ya dakatar da Smart da ke sallama da su maigadi akan ya jira su wuce tare. Kamar zai ce a'a sai kuma dai yay shiru dan kiran da Abba yay masa suna ƙoƙarin shiga massalaci akan idan ya dawo gida ya sameshi falonsa yanzun nan. Yasan maganace da Abban, shi kuma da yayi niyyar bama masu bin san nan a baya dama dan ya tabbatar ba haƙura sukai ba su kamashi dan yana son yin magana da koma waye ya turosun. Babu yanda ya iya dole yabi Uncle Yousuf ɗin, shiko ya ƙaunaci ALLAH ya kaisa har gida yau. Tunda suka fito kuma yaga motar nan sai dai ba napep ɗin yanzu, motar dai ce ke cigaba da binsu yanzu ma. Suna isowa titin anguwarsu yaga sun dakata cikin takaici direban motar na kaina sitiyari duka alamar ba haka sukaso ba. Sai dai kuma abinda bai sani ba shima Uncle Yousuf ya san da su shiyyasa ma ya ɗakkosa ya kawo har gidan.
       “Alhaji yau na saka ka aiki, Nagode sosai”.
    Murmushi Uncle Yousuf da idonsa ke kan mirror yana kallon mutanen nan ya saki, tare da faɗin, “Har yanzu dai ina a Alhaji na? A tunani na na zama Uncle yanzu tunda ƴa zan bayar duk da auren wucin gadi ne”. Yanda Uncle Yousuf ɗin ya ƙare maganar ne ya saka Smart kallonsa, sai kuma ya ɗauke kansa yana sakin murmushi ya ce, “To ayi haƙuri Uncle”.
       “Shike nan na haƙura, dan dama ba'a san iyaye da fushi da ƴaƴansu ba.  Ina fatan zaka samu Abba da maganar yau ko?”.
     “Da wuri haka?”.
Smart ya faɗa da mamaki yana kallon Uncle Yousuf ɗin.
              “Dole ne muyi da wurin, dan ɗazun Baba ya sake kirana akan zuwan M Atik Kumo shima yana nemawa ɗansa aurenta, sannan Alhaji Sulaiman da ɗansa sun gama ƙulla matakin da zasu ɗauka a gobe idan ALLAH ya kaimu.....” tsaf ya zayyane masa komai shima. Mamaki ne ya sake lulluɓe Smart, yayinda a ƙasan zuciyarsa yake ta lissafi akan yanda zai canja salon wasan a yanzu tsakaninsa da Alh. Sulaiman. Kafin yanzu shi bai wani ɗauki zancen da muhimmanci ba, dan har ya gama ƙulla yanda zai kuɓuce wa al'amarin, sai dai a yanzun nan ya canja sabuwar shawara. Duk da bai san minene dalilin Alh. Sulaiman ɗin ba ya kamata ace ya nuna masa shima tsageran kansa ne a wannan gaɓar. Bai damu da zancen MM Atik Kumo ba.....
       “Aliyu kayi shiru!”
   Uncle Yousuf ya katse masa tunani. Iska ya ɗan furzar kaɗan sai kuma ya fuskanci Uncle Yousuf ɗin. Cikin sake furzar da wata iskar ya ce, “ Please Uncle kozan iya sanin yaya kuke da shi Alh. Sulaiman ɗin?”.
    “Yerh babu damuwa Aliyu. Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko ɗane ga Alhaji Sufi Ado Garko. Sannan Yaya ga mahaifiyar Mawaddat uwa ɗaya uba ɗaya. A shekarun baya ɗan uwana mahaifin Mawaddat abokai ne da Alh. Sulaiman na ƙut-da-ƙut, dan sun haɗu ne tunkan ya auri mahaifiyar Mawaddat ɗin adalilin shi Baba da ya ja Yayana jikinsa. Sai dai a yanzu ba haka bane, dan bamu san minene ya shiga tsakanin wannan amintaka ba abokan biyu suka zama maƙiyan juna ta yanda ko inuwa ɗaya basa sha. Iya tambaya na yima Yaya amma yaƙi faɗa min komai. Shi iyakarsa fita harkar Sulaiman, amma shi Sulaiman a bayyane yake nuna tsanarsa garesa da mu ma ahalinsa gaba ɗaya shiyyasa Yayana yay ruwa yay tsaki wajen hana aure tsakanin Tajuddeen da Mawaddat dan yace akwai manufa. Wannan shine iya abinda na sani gaskiya”.
       Kai Smart yake jinjina wa cike da gamsuwa. Sai da Uncle Yousuf yay shiru sannan shima ya bashi labarin kamasan da Alh. Sulaiman ɗin yayi a randa yazo shi da Ahmad suka roƙesa ya koma aiki, ya kuma sanar masa aikin da yace ya koma yay masa tare da nuna masa motar yaran Alh. Sulaiman da ke tsaye a bakin layinsu kasancewar suna iya hango su da ga nan ƙofar gidan su Smart ɗin da ke a bakin titin.”
      Sosai al'amarin ya girgiza Uncle Yousuf ɗin, ya kuma tabbatar masa da shima dalilinsa na kawoshi gida yanzun. Dan tunda suka kammala waya da Baba yaji a ranasa Alh. Sulaiman zai iya ɗaukar mataki kowane iri ne akan Smart shine ya saka wani ɗan sanda zuwa office ɗin Lulu ya saka masa ido, ɗan sandan ne ma a Napep ashe, sai ko gashi bayan tahowarsu gida ɗan sandan ya tabbatar masa ana binsu... “Wato Aliyu idan na fahimta tun fara aikinka da mu Alh. Sulaiman na biye da lamarinka kenan? Kuma bana raba ɗayan biyu a wajen Tajuddeen ya sani. Lallai ya kamata musan dalilinsa danni zuwa yanzu har Tajuddeen ɗin ma na saka masa alamar tambaya”.
      “Sanin dalilinsa abunne mai sauƙi Alhaji, yanzu dai barshi na fara masa duka a ciki, bayan cikin ya ƙulle zai amayar da duk abinda ke a ransa da kansa. Sannan Tajuddeen bai zama lallai yasan komai ba, zata iya yiwuwa amfani uban keyi da shi batare da shi ma ya sani ba”.
    Murmushi Uncle Yousuf yayi tare da bubbuga kafaɗar Smart, dan tsaf ya fahimci inda zaurancen nasa ya nufa game da duka a ciki. Murmushi shima Uncle Smart ɗin yayi tare da buɗe motar yay masa godiya ya shige gida, shi kuma yaja motar yana ƙara jin ƙaunar yaron har tsakkiyar ransa. A rayuwa yana matuƙar ƙauna da son jarumin mutum. Musamman ma matashi irin Smart mai tsayyar zuciya. Wannan nagartar tasa ya fara hanga a filin ƙwallo ya shige masa zuciya, faruwar ƙaddarar data nema dakushesa da ga cikar burinsa ta fara sakashi jin tausayinsa da laluben hanyar da zai iya taimaka masa. Bayan yin dogon nazari ya yanke shawarar kusantosa gefensa domin ƙara tabbatar da halayensa kafin ya ja hannunsa hanyar da ya gama shiryawa domin kaisa ga cikar burin nasa. Sai kuma ga al'amarin ƴar ɗan uwansa ya gitta a cikin labarin tamkar bakangizo a tsakiyyar gagarumin hadarin da ke gab da zubda ruwa. Fatansa kawai ta kasance bakangizo mai amayar da ruwan da ta shanye bamai haɗiyewa ba har abada.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣2️⃣

.......Bai samu ganawa da Abba ba sai bayan sallar isha'i ya samesa a falonsa. Bayan sun gaisa cikin dakewa Abban ya ce, “Aliy!”.
    Ya amsa da “Na'am Abba”.
  “Aliy!”
Ya sake ambata. Shima sake amsa masan yayi kamar farko. Malam Mika'il bai gajiya ba ya sake kiransa a karo na uku shi kuma ya amsa masan dai kamar yanda yay na farko da na biyu.
         “Na kiraka sau uku ko?”.
    Kai ya gyaɗa masa alamar eh.
“Na kiraka badan tisa maka sunan da ni na saka maka ba ne, na kiraka ne domin a yau zan tabbatar maka da magana ta ƙarshe ne akan aurenka. Dan duk maganganun da Yahanasu ta faɗa ɗazun akanka sun sosama mahaifiyar ka da nima kaina zuciya. Kuma mun ɗauki alƙawarin bazaka sake rufa wata anan gidan babu matar aure ba. Dan haka a yanzu ina son jin ta bakinka, idan kana da wadda kake so sai ka faɗeta, idan kuma babu mahaifiyarka ta maka mata, nima kuma na maka sai ka zaɓi guda a ciki.”
       Sai da ya ɗan rumtse idanunsa da jan numfashi, sannan ya ɗago a hankali ya kalli mahaifin nasa. Sai kuma ya sake maida kansa ya duƙar. “Kuyi haƙuri Abba duk ni ne na ja muku, amma insha ALLAH komai yazo ƙarshe, ba sai kun nemomin mata ba ni da kaina ma na samota”.
     Wata irin ajiyar zuciya Abba ya sauke a hankali, sai dai cikin dakewar san nan ya ce, “Wacece? Ƴar wanene? A ina kuma ta ke?”.
           Duk da yawan tambayoyin bai gazaba wajen amsasu ga mahaifin nasa. Ya ce, “Yarinyar da nake aiki gidansu. Ɗiya ga Alhaji Isma'il Jiƙamshi. A yau suma kuma suka buƙaci na turo iyayena dama in har na shirya”.
      “Alhamdullahi. Aliyu Hydar ka daɗe baka faranta min rai irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Ya yaye maka dukkan damuwarka. Ya ɗauraka akan maƙiyanka. Ya kawo maka mafita ga al'amuranka. Na amshi zaɓinka badan ta kasance ɗiyar Alhaji Isma'il Jiƙamshi ba, ko dan yana da kuɗi, sai dai dan nasan kai nagartaccen mutum ne da bazai taba yin zaɓen tumun dare ba.”
     (Abba ka gafarceni wannan dai kam zaɓen tumun asubace ma ƙarewar dare) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam murmushi kawai yayi da faɗin, “Nagode Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Ku gafarceni akan dukkan abinda nai muku ba dai-dai ba kuma insha ALLAHU zan cigaba da zama a fiye da yanda kuke buƙata”.
     Sosai Abba yay murmushin jin daɗi, Aliyu na cikin ƴaƴan da yafi ƙauna a cikin ƴaƴansa, sai dai shi kansa a wasu lokutan bai san mike danne soyayyar ba yayta kyararsa da hantararsa a dalilin ƙaddarar da wani bai isa ya canjata ba. Albarka sosai ya saka masa sannan ya sallamesa. Koda yabar wajen Abba cikin gida ya shiga, sai dai kai tsaye ɗakin Ammah ya shige yau bai gaida kowa ba a matan gidan. Ya samu tana shirin fitowa kaima Abba abinci dan yau itace da shi. Ya fahimci tana cikin damuwar da ya san babu makawa akan abinda ya faru ɗazune tsakaninta da Umma. Ƙannensa kansu yau basa cikin walwala. Suna gama gaisawa Ammah ta fice, annan ne Hawwah ke bashi labarin faɗan da akai sosai ne ai yau ɗin kuma duk a sanadinta ne. Da ga ƙarshe aka ƙare da musu goron halin da yake a ciki. Sosai ya ƙara jin zuciyarsa ta Zafafa. Sai dai komai bai ce ba yay musu sallama ya tafi makwancinsa......

          *_WASHE GARI_*
Chapter 53 · 0% Book details