← Book details Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 114

Sashe 5

Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ɗakinsa yanzu ciki ya shiga ɓangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huɗu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ƙalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ɗan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ɗauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ɗaya ya amsa musu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..
         Daga ɓangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ƙasan carpet ɗin da aka saka a gaba ɗaya falon kalar blue. Basu da kuɗi, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haƙuri sosai, sai dai bata son raini ko kaɗan ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita ɗin jinin zazzagawa ce.
       “Ammah barka da yamma”.
   Ya faɗa cikin muryarsa mai sauƙin amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya ɗakko wasu da yawa ga mahaifinsu ma.
      “Baka da lafiya ne?”.
Gajeren murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. “Lafiya lau nake Ammah, na ɗan yi barci ne”.
   “Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba..”
  Ta ƙarashe faɗa a hankali cikin damuwa. Gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarƙe ya ce, “Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai”.
         Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya ƙarya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko ƙarfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun ɗazun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi. Fitowar ƙannensa biyu ƴammata Maryam da Asma'u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. Ƴammata ne ƙyawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai ɗan turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. Ɗauke kanta tai, dan gaba ɗaya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu.
     “Yayamu ina yini”
Suka haɗa baki wajen faɗa a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana ƙaunar ƙanensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al'amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a ɗakinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga ƴaƴan gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne..
      “Babu wata damuwa ko?”.
   Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buƙatu, sai dai sun san koma sun faɗa tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason ɗakinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai ƙarfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma'u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha...........✍️

*_Humm rikitata-rikitata kenan. Masu karatu ina faɗa muku Bama a fara komai na fa, dan ko shimfiɗar labarin bamu kammalaba balle shiga cikinsa. Littafin FURAR DANƘO...!! Labarine da yazo muku da nashi salon na musamman. Babban abinda ke addabar al'ummar mu a wannan lokaci a cikin gidajenmu da ma wajen gidajenmu da rayuwar ƴaƴanmu mata da maza dama na gidan aure duk ya taɓo fiye da inda kuke zato._*

*_Ga dai Uncle Smart a matsayin drivern Lulu ƙamshi, yarinyar ƴar ƙwalisa mai tsananin wayewar rayuwa. Ƴar gata kuma ƴar hamshaƙan masu kuɗi. Uncle Smart matashin saurayi ɗan talakawa dake cikin jarabawar rayuwa kala-kala. Ya taso cikin gida mai yawan zuri'a da kowa kansa ya sani. Shin ta ina muke tunanin labarin waɗan nan mutane biyu zai kamanceceniya da juna?_*

_Minene abinda Lulu ƙamshi ke ɓoyewa na rayuwarta?_

*Minene ke faruwa a rayuwar Aliyu Hydar (Uncle Smart) da ke taɗe rayuwarsa da ga cigabansa?*

_Baku ba, hatta da ni kaina ina son sani. Dan haka ku garzayo domin kasancewa da ZAFAFA BIYAR ɗin nan naku abin alfaharinku. Ƴan amanarku, akoda yaushe labaransu masu gamsarwane a gareku._

*_Ki daure a matsayinki na mace mai kima da daraja, musulma da ta san muhimmancin hakki da son cigaban nata kasuwancin ko aiki kizo ki saya domin karanta halak ɗinki, karki bari ki ɗorama kanki nauyin da zaki iya yin kaico da sakacin ɗaukar watarana saboda ruɗi da ɗaukar komai a ba komai ba ƴar uwata._*

_ALLAH ya ƙarama rayuwa albarka, duk wanda ya tsare domin ALLAH shima ALLAH ya tsare masa kasuwancinsa ko aikinsa. Alkairin ALLAH ya kai gareku a duk inda kuke a duniya masoya. Muna sonku irin trillions ɗin nan. Duk wanda ya somu domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka shi da zuri'arsa baki ɗaya. ALLAH ya gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi baki ɗaya😭🙏😘😘❤️❤️❤️❤️😘_.

Garzaya ki biya naki kar a baki labari gasu nan da ɗumi-ɗuminsu suke👇😀😘.

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09018600202

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇

+22799643131

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣

.......Shiru kawai yay yana kallon takarda da key ɗin motar da sakatariyarsa ta kawo masa na tsawon lokaci, kafin ya furzar da huci mai kauri ya tashi zaune sosai da ga kwanciyar da yay a kujerar office ɗin nasa. Wayarsa mai ƙyau da ɗaukar ido ya ɗauka. Har yay dailing number da akai saving da _Yaya Isma'il_ sai kuma ya katse yana ɗan girgiza kansa. Dan ya san halinsa, wani lokacin ba gane abubuwa yake ba birkitaccen mutum ne. Wata number ya sake lalubowa yay dialing, ring biyu aka ɗauka.
        “Uncle You.. Good Afternoon”.
Aka faɗa daga can, muryarsa a sauƙaƙe ya amsa da “Afternoon dear! How are you?”.
    “Am good Uncle”.
“Haka ake so. Lulu ta dawo ne?”.
   “Yes Uncle tun ma ɗazun. Sai dai tanata masifa wai Uncle Smart ya barta a airport. Amma Deen ya ce ta masa ihu ne a gaban mutane kuma bai mata komai ba kadai santa. Yanzu kuma Daddy ya goya da bayanta wai zata walaƙanta shi ta koreshi. Uncle ALLAH ni bana so sumasa haka, shi ɗin mutum ne nutsatstse”.
        Wani ɗan murmushin takaici yayi da gyada kansa kamar yana a gabansa. “Karka damu Son! bazan bari su aikata hakan ba insha ALLAHU. Kuma zai dawo aikinsa”.
    Sosai yaron ya shiga ihun murna daga can. Shi kuma ya katse wayar yana mai jin takaicin hali irin na ɗan uwansa. Yanda yake training rayuwar Mawaddat na ɓata masa rai. A rayuwa ko ɗa namiji ne bazakace komai ya nema sai ya samu ba duk arziƙinka da matsayinka. Balle mace da wataran aure zatayi ta koma ƙarƙashin ikon wani. Wanin da ba lallai shi ya iya ɗaukar waɗan nan ɗabi'un nata marasa ƙyau ba. Da wannan ɓacin ran yabar office ranar. Kai tsaye gidansa ya nufa dake anguwar ta Hotoro GRA shima. Sai dai ba street ɗin su ɗaya da gidan yayan nasa ba. Da gudu ƙyawawan yaransa guda uku masu kama da shi sukazo tarbarsa. Murmushi yayi cike da jin daɗi, gaba ɗaya ya haɗasu ya rungume a jikinsa bayan sun gaidashi. Yana ƙoƙarin miƙewa da ƙaramin Deen da sukaje ɗaukar Lulu airport mai wayon tsiya a hannunsa idonsa ya sauka akan matarsa. Ƙyakykyawar mace ƴar duma-duma. Murmushi ya sakar mata kamar yanda take masa itama, ya miƙa mata hannu alamar tazo itama. A hankali ta ƙaraso ta shige jikinsa, rungumeta yay da sumbatar goshinta kamar yanda ya saba. Ko'a jikin yaran dan sun saba ganin hakan ga iyayensu, basa aikata wani abu dazai lalata musu tarbiyyar yara, amma su tarbi juna yayin da wani yay ɗan nesa da gida kona yini guda ne sun nunama yaransu hakan ba komai bane face ƙauna, kuma ya halatta miji yayma matarsa, idan sunga hakan ko'a wani waje ba haramun bane ba. Shiyyasa suma yaran suke kallon hakan a normal ne.
Chapter 5 · 0% Book details