← Book details Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 114

Sashe 66

Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   A matuƙar tashin hankali Alh. Sulaiman ya isa asibiti. Sai yay dai-dai da isar su Hon. Nakowa da sukaje duba Tajuddeen. Shi baima lura da su ba. Sai dai ganin yanda ya fita a mota a rikice yay cikin asibitin ya sa su tambayar drivern sa ba'asi. Shima ba sani yay ba. Sai dai ya tabbatar musu maybe jikin Tajuddeen ɗin ne. Jin haka suma sukai cikin asibin dan dama tafiyar sun yita a sirrance ne shiyyasa babu wani tare da su sai su ukun. Sun iske kam abubuwa sun ƙwaɓe matuƙa, Hajiya Turai da Alh. Sulaiman rungume da Tajuddeen suna kuka. Sam sunma ƙi bari likitocin suyi aikinsu. Hakan ya bama su Alh. Baita yin ruwa da tsaki akan komai. Dan take anan suka shiga ciku-cikun ganin amma fita da Tajuddeen a ƙasar ta wayoyi duk da sun san shima Alh. Sulaiman ɗin duk yana da wannan alfarmar. To da ace lafiya lafiya ne ko jirgi sukutum mahaifinsa yay niyyar nema dan akai Tajuddeen wata ƙasa neman lafiya hakan ba komai bane. Dan da gasken gaske Alhji Sufi Ado Garko ya tara dukiya irin wadda shi kansa bai san adadinta ba. Alhmdllh burinsu kam ya cika, dan zuwa yamma an kammala komai na fita da Tajuddeen, haka uwar da uban suka wuce batare da sun nema kowa a family ɗin ba. Ita kanta amaryarsa Hajiya Abasiyya sama-sama ya mata bayani lokacin da suka koma gida domin shiryawa......

       ★★★......

   Duk wani abinda ke faruwa har barinsu ƙasar Alhaji Sufi Garko ya sani sarai. Sai dai yaƙi yin ko tari akan hakan dan ransa a ɓace yake matuƙa da ɗan nasa. Babu irin haƙurin da matarsa bata bashi ba amma bai saurareta ba. Sai ma gargaɗin karta sake masa maganar Sulaiman a gidan yay mata. Tare da balbale ta da masifar cewar duk wata fitina da ke a tsakanin ƴaƴansa ai itace tushenta. Dan sakacinta ne saboda kasancewarta mace mai masifar son ƴaƴa. Badan shi tsayayyen mutum bane da kaf ƴaƴansa zasu tashi ne a lalace cikin fanɗararriyar tarbiya. Dan tabbas Hajiya Attine bata tsawatarwa yaranta tun ma da ƙuruciya. Komai yaro ke so shi yake yi, ba'a isa kuma ace yay ba daidai ba sai ta kareshi. Yanzu haka akan auren nan na Mawaddat sai da ta haura sama sosai da mijin nata. A cewarta ai itama tanada hakki akan Mawaddat tunda itace ta haifi uwarta. Ita bata yarda Lulu ta auri talaka ba kamar yanda uwarta ta auri ubanta da ga ƙarshe suka kashe mata yarinya dan suci dukiya. Shiko kasancewarsa jarumi mai tsayawa a gidansa ya ce idan ta isa taje ta warware auren mana. Sun haura sama ƙololuwa koma ace har yanzun a saman suke, dan taso fita duba Tajuddeen nan ma yace idan ta fita a bakin aurenta. Wannan kalma ta matukar girgiza mata zuciya dan bata taɓa tunanin fita da ga bakin mijin nata da suka ɗauki tsahon shekaru kusan saba'in tare ba. Ta san kuma zai aikata dan shi baya magana biyu. Dole dai ta haƙura da fitar tunda suma yaran har ma da jikoki ya tabbatarma duk wanda yaje asibiti duba Tajuddeen sai ya koya masa darasin rayuwa.....

        _______________★

  A cikin gida koda Nasreen taje da Deen a wajen Mubarak suke jin baƙin da sukazo duba Smart ne sukazo da shi. Babu wanda ya damu da sanin da ga ina, duk da dai zuciya na raya musu ko dangin matar tasa ne. Dan yaron dai da ganinsa kasan ɗan gidan madara ne. Kuɓul-ƙubul da shi. Sai dai abinda ya birgesu da yaron yanda duk da ƙanƙantar shekarunsa sai da ya gaidasu. Fuskar Ammah da murmushi ta ɗaukesa ta ɗaura saman cinya tana tambayarsa sunansa. Yako bata amsa da cewar Deen shalelen aunty Luu.. shalelen aunty Luu da ga faɗa ya sakasu darawa, abinka kuma da yaro shi ko'a jikinsa, sai ma janye ra'ayinsa da Nasreen tayi suka kama wasansu batare da ya sake tunawa su Aunty Lu zasu iya tafiya su barsa anan ba. Bayan sallar azhar Smart ya shiga cikin gidan. Sunta jera masa sannu da yaya jiki? Dan sun barsa ne dama saboda maza da keta faman shigowa ƴan nan cikin anguwa dubashi tun safe. Zaune ya kai yana amsa musu da Alhmdllh. Yaji daɗin ganin Deen nata wasanshi, sannan koda aka zuba musu abinci shi da Nasreen babu wani janjeni yaron ya zauna sukaci. Shine ya sake musu bayanin daga inda yaron ya fito, sai dai ba gaya musu harda amaryarsa akazo ba. Anan ya ɗan sake shan kunun gyaɗa kaɗan ya kwanta a doguwar kujerar Ammah yana sauraren tsare-tsaren biki da suke tayi, dan shi sai yanzu ma yake jin wai aunty Bilkisu da Hawwah ashe sun tara masa uban kaya na lefe da suketa saye a hankali da shirin dama duk randa ya tashi aure sai dai a ƙarasa abinda ba'a rasa ba. Idanu kawai ya tsirama ƴan uwan nasa yana jin matuƙar ƙaunarsu a cikin ransa. Suko sunata dariya da tsokanarsa. Shima dole yay murmushi yana haɗiye abubuwa masu dama da ke a ransa. Anan ne Ammah ke masa bayanin shawarar da ta yanke akan inda zasu zauna. Sun gama shawara da ƙanwarta Sa'adah zasuyi magana da Abba a gyara masa gidan da suka gada kasancewar su biyu ne dama ke da shi ta ɓangarensu dan suma sunada ƴan uba. Sai yay zamansa, za'a tashi ƴan hayar gidan.
       “A'a Ammah kar ayi haka. In dama ace babu kowa a gidan ne, amma bazan so saboda ni a tashi mutanen da ke a gida tsahon shekaru ba kuma a ƙurarren lokaci irin wannan. Kudai bani lokaci ina kan nazari in sha ALLAHU za'a sami mafita. Dan dama zance kodai a musu magana su kai tarewan zuwa sati biyu haka ko wata ɗaya”.
      Ammah ce ta katsesa da faɗin, “A'a Hydar kar ai haka. Tunda mutanen nan sukace sati ɗayan kawai mu amsa ayi a wuce wajen. ALLAH shine zai rufama kowa asiri. Dan kaga dai a ɓangaren lefe Alhmdllh matsalarsa kamar ta ƙare zance. Ga dai Hawwah nan da Bilkisu zasu shiga kasuwa da kuɗin da ke hannunsu tun da sunyi alƙawarin dai sune zasu haɗa lefen nan. Ko a yanzu ma suturar da suka tara ɗin fa tafi arba'in tunda kowa na saye ta ɓangarensa. Gashi Alhamdullah duk manya ne kamar sun san inda auren naka zai faɗa dama. Kaga yanzu kam kokawarmu ai ta wajen da za'a zauna ne kawai sai kuma kai ɗan ɗinkunan da zakai amfani da shi na angwanci”.
        “Kai Ammah ni sai nayi wani sabon ɗinki?”.
    Hararar sa ta ɗan yi da faɗin, “Oh da haka kake son shiga angwancin. Haba Babangida, ai lokacin abu ayisa kaji. Kasan kuwa a irin farin cikin da nake ciki tsakanin jiya da yau. Ko auren su Maryam bai damuna kamar yanda zamanka babu mace ke cimun rai. Na gaji da jin gori da habaici akan zaman nan naka babu mace har ma da sheri. Amma Alhamdullah ga iyaka ALLAH ya kawo a gaɓar da bamuyi zato ba sai kuma muƙi nuna godiyarmu garesa.”
         “Hakane Ammah. Amma ai inata sakaku wahala. Sam ba haka naso al'amarin nan yazo ba. Ban so ɗaura nauyin aurena a kanku ba, domin nine ya kamata nai muku hidima bawai ku kucigaba da min ba bayan tun ina ciki kuke min har zuwa yau ɗin nan”. Yanda yake maganar cikin damuwa ya sa Ammah sakin murmushi da miƙewa tana faɗin, “Shi komai lokaci ne da shi. Haƙuri akan jarabawa kuma cikar kamala da imanin ɗan Adam ne. Idan aka cigaba da jurewa duk komai zai cigaba da zama labari tamkar bai faru ba, ko a yanda auren nan ma yazo ai babbar aya ce. Fatana ni dai ka kasance da iyalinka fiye da yanda nake zatonka da tsammani. Ka kuma riƙe mutuncinka dan kar zuciyarka ta ɗora maka cewar dan su masu shi ne shikenan zaka zauna su zame maka rijiyar tatsar abin duniya. Babu ruwanka da dukiyarsu ka tashi ka nema na kanka ka ciyar da ƴarsu ka tufatar da ita da kare mata dukkan wani hakkinta da ke a kanka. Kar ka yarda ka bada wata ƙofa ta amsa da ga garesu da sunan wai kana auren ƴarsu. Duk da dai bana kokwanto a kanka Aliyu. Ina dai sake tunatar da kai ne dan dukiya shu'umar abuce mai shiga rai da jinin ɗan adam harma da ɓargo.”
     Sosai nasihar mahaifiyar tasa ke ratsashi matuƙa. Tana ƙara masa ƙwarin gwiwa akan nasa ra'ayin kuma da ƙyakykyawar manufa.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣2️⃣
Chapter 66 · 0% Book details