Sashe 38
Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Duk da a yanda take jin matuƙar gajiya bata huta ba har sai da doctors suka rufu akan yarinyar nan da lamarinta ya taɓa duk wanda ya ganta a cikin asibitin. Dan hatta Uncle Yousuf tuni ya ajiye batun takaicin Lulu gefe da shi akai komai na ganin likitoci sun tsaya a kanta. Abin tausayi ita uwar ma zuciyar ta bushe ko kukan zahiri ta kasa sai na zuci. Ganin komai ya natsa dan ana neman uku na rana ma Uncle Yousuf ya kai dubansa ga Lulu da alamunta suka nuna gajiyarta matuƙa. Dan sai faman yamutse fuska take. Tausayi ta bashi, dan haka ya cigaba da kallonta a kaikaice cikin tausasawa da mata addu'ar shiriya akan halayenta marasa ƙyau. Isowar Ahmad wajen ta sakashi maida hankali garesa. Fuskarsa da murmushi yay ma Lulu magana, amma sai ta amsa masa a ɗan ɗage. Bai damu ba dan ya santa ya san halinta. Hasalima ya taɓa nuna sonta amma ta taka masa burki lokacin tana farkon dawowarta da ga Uk. Uncle Yousuf da yanda tai masa ɗin ya bashi takaici ya harareta, sai kuma ya maida hankalinsa ga Ahmad ɗin da ke faɗin, “Yaya ya farka, doctor ɗin ma ya sallamemu dan ya matsa zaije gida. Kasan Mawashi fa sam bai son asibiti.”
Murmushin Uncle Yousuf yay, cikin yanayin tsokana ya ce, “Kai haba kamar wani yaro ko mace”.
Dariya Ahmad yayi, dai-dai nan Smart ya fito a wani ɗaki da ke kusa da inda suke. Coach riƙe da hanunsa kamar wani ƙaramin yaro sai ɓata fuska yake. Dan da gasken fa bai son asibiti shi sam a rayuwarsa. Kuma bai san allura. Yanzu ma ba ƙaramar badaƙala akasha ba kafin ai masa shine ma Ahmad yay fushi ya fito. Ilai kuwa hararar Ahmad ɗin yayi tare da ɗauke kansa duk a lokaci guda, cikin rashin sa'a ya saukesu akan Lulu da tai kicin-kicin da fuska saboda kasancewar Ahamd a wajen, ita ala dole kar a kawo mata raini, dan duk wanda ya taɓa furta cewa yana sonta ko ya nuna basa ƙara shan inuwa ɗaya kuma. Ƙoƙarin janyewa yake sai kuma yay dai-dai da ɗagowarta cikin shirin miƙewa tabar wajen. Ta wani yamutse fuska fiye da yanda take sai kace wadda taga kashi. Shima ƙara tsuke tashi fuskar ya ɗanyi tare da ɗauke kansa gaba ɗaya irin bai ganta ɗin nan ba ma....
“Ga Aliyu nan babu lafiya sai ki masa sannu. Dama ina son ki gama da wannan kai kawon ne muje ki dubashi ashe ma zasu sallamesa yanzu”. Uncle Yousuf ne yay maganar cikin katse hanzarin Lulu dake niyyar barin wajen abubuwa masu yawa na mata kai da kawo musamman ganin drivern nata a nan. Dakatawar tai, sai dai ta kasa cewa komai sai ɗan hararsa da take ƙasa-ƙasa.
“Wai nikam bada Mawaddat nake ba?!”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin ɗan kaushin murya dan ya san taurin kanta na tsiya da gadara. Sosai taji haushin hakan, amma babu yanda zatai dan Uncle Yousuf ne. Ta ɗan sake ɗagowa ta kallesa, a taƙaice ta furta, “ALLAH ya bada lafiya”.
Coach ne ya amsa da “Amin”. Cikin murmushi. Shi kam a zuciya ya amsa mata. A zahiri kam ya ɗauke kansa gefe kamar bai san da shi take ba. Sosai ta sake tunzura da salon rainin nasa. Tana mai tabbatar ma kanta a zuciya sai ta koya masa hankali da sauke masa wannan girman kan nasa. Batare da ta sake kallon kowa ba ta ce, “Uncle You ni na koma Office. Uncle Hameed ka gaidamin Aunty Rukayya sai nazo gaisheta”.
Coach yay ɗan murmushi da faɗin, “Zan sanar mata idan da gaske kike Daughter. Dan na sanki ke da sabgoginki marasa ƙarewa.” karan farko da ta saki sassanyan murmushinta da kan ƙawata ƙyawun fuskarta, sai dai batayinsa sai ta gadama. Kai Ahmad da zuciyarsa tai wani irin tsargawa ya ɗauke gefe. Dan Lulu cikakkiyar mace ce da kan iya jan hankalin mafi yawan maza musamman irin matasanmu na yanzu masu fifita ƙyale-ƙyale ga mace fiye da nagarta. Sai kuma ka kwasa ka kai gida ka samu fanko ce ko addininta bata sani ba sai duniyar kawai aka saka a gaba da son birge al'ummar cikinta....
Suma a tare suka fito su huɗun, Coach da Ahmad da Smart suka shiga motar Ahmad da ya koma ya ɗakko. Uncle Yousuf kuma ya shiga tasa motar dan Lulu kafin su fito ma har ta bar asibitin. Babu wanda ya sake bi takanta. Godiya Smart yay ma Uncle Yousuf sosai tare da su coach ɗin ma gaba ɗaya. Da ga haka kowa yaja motarsa. Har gida suka kaisa. Ahmad yay masa rakkiya har cikin ɗakunan kasancewar ba baƙonsa bane ɗakin dama. Bai wani zauna ba saboda Yayansa dake jiransa a mota. Yay masa ALLAH ya ƙara lafiya ya tafi.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣
.......Bayan yay sallar la'asar barci ya sake sha har kusa da magrib batare da kowa yasan yana a gidan ba. Dan sanda su Ahmad suka maidosa basu ga kowa a ƙofar gida ba. Wanka yay da alwalar magrib ya fito. Yanayin yanda yake jin jikinsa babu ƙarfi ya sashi yin sallarsa a ɗaki. Bayan ya idar ya fita zuwa cikin gidan. A kallo ɗaya zaka iya fahimtar baida lafiya ƙarfin hali ne kawai. Sai dai hakan bai hanashi leƙa duk ɗakunan gidan ya gaida su Mama ba. A ɗakin Umma ya samu babban yayansu Salim yazo gidan shima. Sama-sama suka gaisa Salim ɗin na wani cika da batsewa shi adole mai naira a gida. Ko'a jikin Smart dan shi ba wannan shirmen ne a gabansa ba. Yana juya baya zai fita Salim ɗin da Umma suka raka bayansa da harara. Oho baima san sunai ba shi dai.
A falo ya samu ƙannen nasa duka. Sai Nasreen dake ta faman tsalle-tsalle ita da autar Aunty Amarya. Gaisheshi suka shigayi, ya amsa yana zama tare da ɗan dafe kansa da har yanzu bai gama saki ba. Ammah da tun shigowarsa take kallonsa ta ajiye littafin addu'oin da ke a hanunta da faɗin, “Baka da lafiya ne Hydar?”. Hannun ya janye da ga goshinsa ya ɗan furzar da iska. “Kaina ne ke ɗan ciwo kaɗan kawai Ammah, na kuma sha magani ma. Ina yini”. Maimakon amsawa sai ta cigaba da kallonsa cike da nazari. Ganin yanda ta kafesa da ido ya sashi duban Hawwah cikin son kauda hankalin Ammah ɗin ya ce, “K babu wata damuwa dai ko?”.
Kanta ta jinjina masa itama da ɗan damuwar ganin yanayin nasa. “Ba komai Yaya Hydar. Sai dai kamar ba ciwon kan bane kawai ke damunka. Ka wani zabge a lokaci ɗaya kamar wanda ya kwanta ciwo.”
Baiyi mamakin jin furuci nata ba. Dan a duk lokacin da ciwon ya bugesa ba ƙaramar fyaɗa yake masa ba. Ya ɗan sake furzar da iska yana tashi zaune da ƙyau da kamo hannayen su Nasreen. “Ciwon kai ne kawai kin san bai min da wasa”. Badan sun gamsu ba dai suka yarda da hakan. Maryam ce ta kawo masa abinci da faɗin, “Ko sai kayi sallar isha'i”.
Nan ma iskar ya ɗan furzar da duban kular abincin. Yasan dai shinkafa ce dan ya ga Salim na ci a wajen Umma. Shi kuma sam shinkafa bata da farin jini a wajensa sai dai kawai ya cita dan yunwa. “Ai banama jin zanci abincin nan ɗauke kawai. Ko kuna da ƙullin kamu ki ɗan dama min kaɗan”.
“Eh akwai. Dama na kunun gyaɗa da Ammah tasa aka markaɗo ɗazun ko shi za'a dama makan”.
“Yauwa dama min shi ɗin kawai bara naje massalaci na dawo”...