Sashe 104
Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanaki sun ƙara shiɗawa, dan a lissafin Lulu dai next week ne rabuwarsu da Smart. A week ɗin daya wuce ya kaita gidansu da gidan Uncle Yousuf, daga nan ta samu ƙafar zuwa duk bayan kwana biyu haka idan ta fita aiki takan leƙasu duk da dai daga Daddy har Uncle Yousuf ɗin ma dai sunyi tafiya basa ƙasar ma. A ranta a duk sanda ta ƙiyasta tana jin farin cikin komawarta free dan ta fara jin ƙosawa da tsakurarsa musamman ta saka hijjabi da tafi cimata zuciya da rai fiye da komai. Sai dai wani sashe na zuciyar tata na mata kamar babu daɗi musamman idan ta tuna Ammah da ƴan uwansa. Takan faɗa dogon nazari akan hakan, amma idan taje duba jikin kakanta Alhaji Garko da har yanzu dai babu lafiya suna ma shirin fita da shi ƙasar ne duk da yana turjewa sai da Dada taita mata fanfo da zugeta. Wani lokacin Lulun kan nutsu ta saurareta, wani lokacin kuma tace “Kai Dada dan ALLAH wai miye matsalarki da Aliyu ne? Miyay miki?”. Dadan kan zazzageta wani lokacin ko balbaleta da faɗa dan masifaffiyar mata ce. Wannan faɗan da take takura mata da shi yasa kwana biyu Lulu bataje gidan ba, sai dai tai kira a waya taji yaya jikinsa. Hakan sai ya fara damun Dada, dan a ganinta wani asirin Smart ya sake tafkawa Lulu...
A ranar Juma'a da Lulu ke cika kwanaki uku rabonta da zuwa gidan Smart ya wuce Legos, Maryam da Asma'u aka kawo mata su tayata kwana, sai Mubarak da zaizo da dare, sai su Afrah suma da taje da kanta ta ɗebo. Nan fa shafta ta buɗe. Wucewar su Maryam ya ƙara zafar Umma, tai shiri ta nufi gidan aminiyarta Hajiya Naqiba rai ɓace. Bayan ta gama labarta mata Hajiya Naqiba tace tashi muje yau ayita ta ƙare. Sun je gidan mai ƙunshi da tace zatai musu rakkiya. Daga can suka tafi gidan Alhaji Garko. Sosai Umma ta sake girgiza da dukiyar waɗan nan mutane, nan fa zuciyarta ta ƙara ƙaimi wajen ƙulle-ƙulle na ganin auren Smart da Lulu ya gundile. Sunyi zama fin na awa ɗaya kafin hamshaƙiyar tsohuwa mai ji da kuɗi da hutu ta fito cikin isa da izzarta. Ai sai su Umma sukai saƙale suna kallon ikon ALLAH, dan Dada ta tsufa sosai kawai dai abinka da jin daɗi ne. Cikin girmamawa suka gaisheta tana amsa musu da ƙyar a yamutse. Mai ƙunshi ta mata bayani duk da dama ta fara sanar matan. Amma tsohuwar nan saita dubi su Umma a watse cike da isa ta ce, “Ku tabbatar duk abinda zai fito bakinki bazai zama wuƙar yankaku ba, dan bana son munafunci ni da kuke gani na anan”.
Muryar Umma na rawa ta ce, “Wlhy Hajiya a duk abinda mukazo miki da shi nan babu munafunci. Yaron nan asiri yayma ƴarku. Idan kuma baki yarda ba kisa malamai su bincika muku zaki fahimci gaskiyarmu. Amma kuyi da sauri dan yanzu haka yayi tafiya wai Niger da abokinsa kin san kuma yanda suka iya asiri bana raba ɗayan biyu wani bala'in zai sake haɗo muku (😂 Niger akacema su Umma Smart ya tafi raka Ahmad sayen shanu).
Mai ƙunshi da yake itama makirar mace ce tana kuma son sake samun fada a wajen Hajiya Dada sai ta sake taƙarƙarewa tana taya su Umma. Harda cewa zata raka Dada wajen wani malami a duba musu ɗan uwanta ne a Zuru yake. Amma batai maganar hakan ba sai da su Umma suka fito bayan an sallamesu. Hankalin Dada ya tashi, dan haka ta sallami su Umma tace mai ƙunshi tazo ta sameta gobe idan ALLAH ya kaimu bayan an wuce da Alhaji Garko dan zasuyi gaba ƙasar London ita sai nan da sati ɗaya zatabi bayansu. Cike da farin ciki su Umma suka fito da ƙyautar naira dubu ɗari kowa hansin-hansin. Mai ƙunshi kuwa ma basu san mi aka bata ba. Ta kumace dole su cire mata kasonta a ciki dan bazata rakosu a banza ba. Da ƙyar suka bata goma-goma suna ƙunƙuni. Tace oho dai shegu ai ni kunzo min da hanyar samun kuɗi, naci a wajenku, naci a wajenta, naci a wajen malamin da kukace aje.
Washe garin asabar aka wuce da Alhaji Sufi Garko ƙasar London dan likitoci anan gida Nigeria sun tabbatar poising ɗinsa akayi. Ba'a fahimci hakan ba kuma sai a tsakanin kwana biyun nan da gubar ta bayyana kanta, dan sun bashi wadda bata bayyana kanta da wuri har sai tayima jiki illa ne. Duk da wannan tashin hankalin da ake ciki hankalin Dada nakan Lulu da itama dai yau tazo gidan har da su Asma'u da su Afrah. Sai dai taƙi yarda ko sau ɗaya su zauna da Dada har sanda ambulance ta ɗauki Baba itama sai taja ƴan rakkiyarta suka bisu har airport. Basu baro ba sai da jirgin da za'a ɗauke sa a ciki shi kaɗai sai yaransa maza biyu ƙannen Alh Sulaiman da zasuyi gaba ya tashi. Kowa ya bisu da addu'a kafin yaje. Suna baro airport ɗin jirgin da ya ɗakko Tajuddeen da Alhaji Sulaiman (Tsule🤣) ya sauka shi kuma. Ya samu sauƙi sosai koma muce a zahiri ya warke, sai dai a zuciya kam babu abinda ya ragu na soyayyar da yakema Lulu. Ya samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyane kawai bisa alƙawarin da mahaifinsa yay masa na sai ya mallaka masa Mawaddat ya kwantar da hankalinsa. Wannan dalili ne ya sashi jin ƙwarin gwiwar biyosa suka dawo. Manyan aminansa na yanzu duk da dama can aminan nasa ne matsaloli suka rabasu Alhaji Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau ne sukaje tarbarsu. Dan kaf Family na Garko babu wanda yasan da dawowar tasu a yau.......✍️
_(🤔Tofa! Alhaji Sufi Garko ya tafi jiyya a dalilin poising nashi da akace anyi. Alhaji Sulaiman Sufi Garko ya dawo tare da ɗansa Tajuddeen Sulaiman Sufi Garko daya tashi a jiyyar soyayya babu wani damuwa tattare da al'amarin su. Anya kuwa babu wani abu a ƙasa? Humm kumu dai je zuwa to🚴)._
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣2️⃣
_____________
Do you really need a scholarship? want to relocate to Canada, Qatar, or Oman, to Work? Study? Or work and Study? And how to get a scholarship?
Ina masu son tsallakawa ƙasashen ƙetare don Samarwa kai aikin yi bisa tsari da ƙa'ida💃🏻 tun daga.
*WORKING VISA?*
Tare da masu neman *SCHOLARSHIP (samar da karatu ƙyauta)*
Kamar ƙasashe haka👇🏻:
*-QATAR*
*-OMAN*
*-CANADA*
*-USA*
Da Sauran su .
To ga babban dama yazo maku wanda za'a dama ,zaku iya tuntuɓar wannan number domin ƙarin bayani 👉 08144147273
👉Join WhatsApp group https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA
Muna samar da Qatar 2 years working visa a kwana 7 insha Allah.
____________
.......Dada tayi tunanin Lulu zata sake dawowa gidan, amma bayan duk ƴan rakkiyar Baba sun dawo sai gashi babu ita, sai ma sanar mata da akai ta wuce gidan ta. Hakan ya sake girgiza Dada ta kuma tabbatar da eh lallai da alamar ƙamshin gaskiya a zancen mutanen nan asiri yaron nan yay ma jikarta. A take ta dannama Fulera mai ƙunshi kira, batare dako amsa gaisuwar ta ba tace ta sameta yanzun. Fulera ido a kuɗi tuni tai tsalle tayo waje da ga gidan su, dan dama dai zawarci take kusan shekara tara kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gata a Garko house. Ta sami Hajiya Dada tare da mai aikinta dake mata irin waɗan nan ayyukan na sirri, dan Dada tunda jajayen sawu ƴan hannun bin malamai ne kam. Cikin gurfana Fulera ta miƙa gaisuwa, Dada ta amsa cike da isa. Babu wani jan lokaci ta sanar musu abinda take son a mata. Zasuje wajen mutumin da tace mata a Zuru ita da mai aikinta. Ba haka Fulera taso ba, amma dai babu damar musu dan haka ta amsa da to. Mota Dada ta bada akaisu tare da kuɗin amma sai ta damƙawa mai aikin nata. Nan ma Fulera taji zafi, ta dai danne, damar fara fita data samu kafin mai aikin Dada ta kimtso ta samu ta dannama Hajiya Naqiba kira ta sanar mata komai. Dariya Hajiya Naqiba tai da faɗin, “Kai tsohuwar nan mayyace akwai shegen wayo. Barta ai inta san wata bata san wata ba. Kwantar da hankalinki bari na kirashi kafin ku isa.”
Haka kuwa akai hajiya Naqiba tai kiran malam na-zuru, duk yanda suke so haka ta tsara masa, shima da yake shegen kansa ne yace karta damu. Abinka da lafiyayyar mota basu sha wahala ba, dan bayan azhar kaɗan suka isa zuru saboda gudu na masifa da drivern yayi. Malam na-zuru da yake yasan da zuwansu kafin ma su faɗi abinda ya kawosu ya shiga zayyane musu wai ai ya gani ne a cikin aikinsa. Tuni mai aikin Dada ta ruɗe ta danna mata kira, nan ma fa sukai magana da malam Na-zuru ya sake fanfa Dada da kalolin sharri wa Smart dangane da auren Lulu, harda cewa ai asiri Smart ɗin yay musu dan yaga kuɗi. A yanzu haka ma yana Niger yaje anyo masa wani babban ƙulli, zaita kwantar musu da kai ya nuna shi na ALLAH ne sai anan gaba kaɗan zai bayyana halayyarsa da mugun nufinsa. Tsaf Dada tahau ta zauna saboda tayi imani da malaman tsubbu matuƙa gaya. Malam na-zuru ya haɗa musu kayayyaki suka sake ɗakko hanya....