← Book details Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 114

Sashe 4

Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

      Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ƙofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ƙasan maƙoshi har yanzu zuciyarsa na masa ƙuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika'il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ƙasƙantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ƙarfin ƙwanjinsa amma ba ƙasƙanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ƙarƙashin takalmin kowa ba. Da'ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ƙasusuwa ya zubar da ita a airport ɗin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ƴa mace.....
         “Ɗan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faɗa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ɗin maimakon amsa, ya zaro ɗari biyu a cikin aljihunsa ya miƙa masa. Bai jira mai napep ɗin da ke faɗa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..

       *_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ƙasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuƙar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ɗa na bakwai a gurin Malam Mika'il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huɗu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuƙar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ƙwallon ƙafa. Ya iyata matuƙa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ɗinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ƙwallo sai ya yanke jiki ya faɗi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al'amarin da asiri, sai dai shi yaƙi ɗaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara ƙwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana'a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ƙanƙanin lokaci al'amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ƙoƙarin kamo can idan nan taƙi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ƴan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika'il Idris Mawashi huɗu ne cif, hakama ƴaƴa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ƴammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09018600202

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇

+22799643131

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣

_Free pages end_

.........Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko'ina mulmule yake da suminti.  BQ ɗin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki iyayensu mata,  baya can ƙarshe sashen mahaifinsu Malam Mika'il Idris Mawashi. Sam baya buƙatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ɗakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ƙanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ɗakinsa. Dan a yanzu haka akwaima ƙanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula ƴar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faɗan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ƙwallar ɓacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ƙwaƙwƙwarar sana'a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba ɗaukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taɗe rayuwarsa haka. Duk inda ɗa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko'a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.
     Ɗakine ɗan babba mai ɗauke da kafet maroon color mai laushi, sai ƙatuwar katifa irin wadda ba'a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ɗan yi teburin karatu da kujerarsa. Ɗakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ƙamshi kamar ba ɗakin namiji ba. Uniform ɗin da aka sharɗanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ɗakin ƙwara ɗaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ɗaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaƙi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ƙona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ɗinkin fidda surar jikinta baƙin ciki yake ji balle wannan da gaba ɗaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ƙarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al'amurin ma yaƙi barinsa yin barcin da yake buƙatar yin ko zai samu sassaucin baƙin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ƙyar ya samu barcin ya ɗaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la'asar. tashi yay da ƙyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miƙe ya shiga toilet ɗin ɗakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za'a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ƙofar gidansu yake, dan baifi gida huɗu ba ne tsakaninsu....
Chapter 4 · 0% Book details