← Book details Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 114

Sashe 57

Furar Danƙo Part 1 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

    Ƙololuwar ɓacin rai Alh. Sulaiman ya shiga sakamakon kiransa da akai masa cewar ga Tajuddeen a asibiti sakamako auren Lulu da mahaifinsa ya ɗaura yau da shegen tsageran yaron nan da yakema kallon abin alhaki. Abu mafi ɗaure masa kai shine ta yaya Baban yasan da shirinsa har yaje ya ɓata masa shiri haka? Ya san dai da ga shi sai Tajuddeen suka ƙulla hakan. Dan ko mahaifiyar Tajuddeen ɗin bata san komai ba akai. To kodai cikin waɗanda ya aika sumasa waliccin auren ne? Kai bayajin hakan zata kasance ai. Dan Kawu Laminu mutum ne makwaɗaici yasan kuɗin da ya shaƙa masa bazai barsa buɗe baki ya faɗama wani ba. To ko Tajuddeen ɗinne yay ɓaranɓarama a gaban wani? Shima dai hakan bai kama hankali ba gaskiya dan yasan yanda Tajuddeen ke son auren nan bazai taɓa bari wani ya samu ƙofar rusa masa shi ba. Tattare komai yay ya ajiye gefe yabar maɓoyar tasa zuwa asibiti. Dan yazo nan ɗin ne ya ɓoye saboda Baba har sai ƙura ta lafa zuwa gobe kamar yanda ya tsara idan an ɗaura aure da Tajuddeen. Lokacin da ya isa ya samu Tajuddeen ko farfaɗowa baiyi ba ma. Ga shi labari yazo masa su baba na government house ana liyafar cin abinci bayan a gabansu Jikansa ya faɗi amma ya shure saboda bai ƙaunarsa shi da ɗansa. Sosai zuciyarsa ke ƙara tafasa, yayinda yake saƙa abubuwan alkaba'i da zai rusa rayuwar Smart da duk wanda ke tare da shi. Dan a ganinsa duk shine ya ruguza masa shirinsa, sai yanzu ma yake nadamar bayyana masa fuskarsa a waccan ranar... Farfaɗowar Tajuddeen babu jimawa mahaifiyarsa ta iso, sai dai daga zuri'arsu kaf babu wanda ya leƙo asibitin dan Baba ya hana. Ya kuma tabbatar musu duk wanda yaje sai ya ɓata masa rai fiye da yanda yake zato ko tsammani..........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣5️⃣

.......Shigowar Abba da Asma'u ta fita ta kira da sauran ƴan uwansa maza da basu kai ga fitaba yasa matan darewa. Tallafosa Abba yay da ga jikin Ammah da ke tofa masa addu'a a nutsenta, duk da a rikice take amma a zahirinta babu alamar ruɗewa dan mace ce kamila mai tarin nutsuwa akan komai. Faisal ne yay hikimar matso da fanka kusa da su yana faɗin, “Ku ɗan matsa a kansa yasha iska mugani”. Fita duk matan sukai a ɗakin, sai Ammah da su Umma da suka shigo. Aunty Amarya ta ce, “Ko dai a masa hayaƙin maganin nan dan yanayin nasa kamar na matsalar can ne da ke bugunsa”. Cikin gamsuwa Gwaggo Sa'adah ta ce, “A kawo ɗin sai a gwada a gani. Rushin wuta Hawwah ta ɗibo, Maryam ta ɗakko maganin a ɗakin Ammah aka saka masa, yayinda Ammah da Abba ke cigaba da tofa masa addu'a su da sauran ƴan mazan gidan. Kusan minti talatin ana abu ɗaya kafin ya fara motsawa. Sai kuma ya fara wata irin atishawa mai ƙarfin gaske. Yayi tafi sau bakwai sai kuma ya dafe kansa yana mai ambaton sunan ALLAH da faɗin, “Ammah kimin addu'a kaina kamar zai fashe. Wayyo Ammah kaina kimin addu'a”.
      Da ƙyar Ammah ta danne hawayen da suka cika mata idanu, ta kamo hanunsa cikin hannunta ɗayan kuma ta ɗaura a saman goshinsa da faɗin, “Kayi haƙuri Hydar gani nan kusa da kai ina maka addu'an in sha ALLAHU zai bari, kai dai cigaba da ambaton ALLAH”. Addu'a ya cigaba da yi a ransa, tare da sake kai hannunsa saman goshinsa ya ɗaura kan na Ammah data dafe masa... Cikin amincin ALLAH a haka aka samu barci mai nauyi ya ɗaukesa kusan gab da magrib. Abba ne ya saka ƴan mazan ɗaukarsa aka maida ɗakinsa dan zai fi samun ƙarancin hayaniya a can ɗin kasancewar nan akwai yara (jikokin gidan). Aunty Bilkisu da Hawwah ne sukaje can suka zauna da shi. Itama Ammah bayan ta idar da salla sai ta nufi ɗakin nasa da ruwan addu'oi da tayi a kofi ita da Gwaggo Sa'adah dan su Aunty balikin su samu suzo suyi salla suma......

         ★...........
Chapter 57 · 0% Book details