← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Next Day
Ashobe saida Tasleem ta biya 25k kafin aka bata nude fitted gown codelace harda na makeup...gidan bikin akwai varieties of food koh mai kk so deba za kayi Inkai mai ci ne saide ka barke da zawo.. Da misalin Karfe hudu aka fara shirin tafiya dinner, tun safe Alhajee mai kudi ke kiran ta yaji ya za ayi, bayan sun gama shirya ta kirashi da yazo, bata son heavy makeup light akayi mata, brown skin color ta sai glowing yakeyi, a fuska dai ba ta wani hadu ba amma in ajiki ne ba a magana, ko ke mace sai kin kalla kin kara, ta kowa ta keyi a natse irin mai daukar hankalin mai kallo harta isa inda yay parking,

Alhaj was really astonished by her coz she looks so alluring.. Ganin yadda yake kallon ta yasa ta fara gyara gyalen jikinta tace Inawuni tayi magana adan tsorace Wanda hakan ya kara mata kyau.. Da kyar ya iya saisaita numfashi sa yace, Godiya ya tabbata ga ubangiji talikai wanda yayi ki daban acikin sauran matan, walhy Tasleem ke din ta daban ce komai naki daban ne Gimbiya sarautar mata..

Cike da kunya Tasleem ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers, shigo man Gimbiya yay magana yana bude mata car, tsaye yayi yana Kare mata kallo he couldn't believe his eyes..yace daman haka take? Rufe kofar yayi zauna mazauni driver, Tasleem let's get to know each other kafin a fara tafiya, kanta nakasa cikin Melodious voice tace ok, yace tell me everything about you I mean everything...

Well ina zaune agun kakata a Layin namorike dake Samaru zaria, iyayena ALLAH yayi masu rasuwa da a Lagos muke rasuwan iyayena yasa muka dawo Zaria..

Alhj yace ALLAH ya jikan su ya gaffarta masu, ta amsa da Amin kafin yace mai kakan ki keyi na gani ta rike ku?

Tasleem tace tana tuyan kose da safe,
What? Kina numfi iyayenki basu bar maki kome ba? Ina dangi ku suke?
Tasleem tace kakata tace bata so ina tambaya, wai insa a Raina mu kadai ne, shuru yayi kafin yace toh karki damu fito da wani kudi yayi Wanda akala yakai 50k yace kudin manni,

No ka barshi wanca daka bani bai kare ba tayi magana without looking at him, amshe Jakarta yayi sa mata kudin, sune na karshe a jerin motoci da aka wuce gun dinner.. Biki yayi biki, Anci an sha anyi rawa, sai wajan 12pm aka watse, duk aka nufa gidan Amarya, mamaki Alhajee ta keyi gani bai koma gida ba, tace Alhajee family Ka fa? sun tafi family trip Dubai ya bata amsa dakalce..

Shuru ne yadan biyo baya, can tace zan shiga ciki gida karsu rufe kofar, toh idan sun rufe sai mu kwana a nan yay magana yana kallon fuskar ta, ganin yanda yake kawo fuskar sa daf da nata yasa tace ka bude min zan fita,
A hankali yace bakya son Ku fita daga kunci rayuwa? Inason na baki sabon rayuwa da zaki ji kije duk inda kk so a fadi duniyar nan...

Ba tayi mamaki ba daman tun farko haduwar su ta gane hakan,sai kawai ta wayince tace ban fahimce ka ba? Murmushi yayi kafin yace nasan daman ba zaki gane ba yayi magana yana shafa fuskata, tayi saurin ture hanunsa tace mai haka?

Sorry Tasleem kyaun ki ke rikita ni, ke baki ga yanda na kasa na tsare ba?zan iya baki 500k for one night.. Fashewa tayi da kuka tace Don ALLAH ka bude min motar ni banso kudin ka, na zabi na zauna cikin tallauci.

Haukace mata yayi a car din, ya dinga lashe mata fuska da kyar ta samu ta wanke shi da Mari ya dawo cikin hayacin sa, tace ka bude min motar nace..unlocking yayi ta fice daga motar tana danasani....

Tana fita Shiko yace walhy bazan taba barin ki ba harsai na lasa zumanki, "daga gani ta danya ce shagwab koh nawa sai na kashe don na malleke jikin ki yana fadin haka yaja motar ya wuce... "

Tunda take ba ataba mata haka ba sai yau, bata taba ji ta tsane namiji ba sai yau, nan take tasa numbers a blacklist don bata so ta sake ganin fuskarsa.. Daren rana wuni tayi tana tunanin abinda wannan tsohon banza yayi mata,
"Na fada mai gaskiya thinking zai ji tausayina ya canza mumunar kudirin sa akai na aman ina sai ma kokari Idar nufinsa yake Mtchews"

Washe Gari da safe as early as possible ta baro gidan biki ta koma gida, ji ta keyi kamar bata da lafiya...ko bi takan Inno ba tayi ba ta shige dakin ta, tayi kwanciyar ta.. "

Inno ta shigo dakin tace Talatu lafiyan ki kuwa? Kin dawo ba zaki iya zuwa kice min kin dawo ba? Ko dai wanni abu akayi miki acan? Taso na gani tayi magana cike da tsoro...

Turo baki Tasleem tayi tace ba abinda akayi min Inno kaina ke min ciwo.. Inno tace Ayo ai harkin sa gaba na, na fadi,taso muyi magana Talatuwa na, mikewa Tasleem tayi ta zauna,

Inno tace wannan Alhajee yana ta sintili zuwa nace saikace wanda kk yi mai alkwarin wanni abu?Kwalo idanuwa ta waje Tasleem tayi,tace Inno awara yake so ai,

Inno tace Ayo,yanzu magana da nake son nayi shine ya maganar walima? Idan da hali yau nake so na shiga kasuwar kauye na siyo shinkafa da kuma dan bunsuru koh ya kk gani?

Bunsuru kuma Inno? Haba mana Inno Ina laifin tunkiya koh rago?... Uwar rago Kinji koh nace uwar rago za a siya, to na gaya miki wannan ma Bunsuru da za'a siya kawai zanyi ne sabida ke amma in tani ne kowa a bashi shinkafa man da zobo Inno tayi magana cikin takaici...

Tasleem tace Nagode Inno Sosai, nide abinda nake so kiyi min shine waina da miyan tantakwashi, ni zanji da sauran abubuwa..

Ban gane zaki ji da sauran abubuwa ba Talatuwa?indai ce ba kudin shiga ABU za kiyi anfani dashi a walimar ba? Murmushi Tasleem tayi kafin tace, Maimuna ne tabani wasu kudi wai Wanda zata aura ya bata, toh dashi zan hada da kudin da mam Nazeef yace zai bani... Shuru Inno tayi tana nazari can kuma tace waina tiya nawa za muyi kinsa ni da jama'a fa? Inno ko tiya biyar ai yayi koh? Tasleem tayi magana tana kallon expression inta,

Inno tace hobdijam tiya biyar? Tasleem ta Kyalkyalce da dariya tace to Inno ko Baba Buhari baze nuna miki yawan masoya ba..

Ɗuma mata dundu Inno tayi tana dariya tace ki shirya yau akwai tuya, dan ni ban gane tuyan asiya kwatakwata kudin a gantale take kawomin..

Tasleem tace Inno ya kamata mu samu mai tuya kinga idan na fara karatu nida ki gani sai sati sati koh wata.. Inno tace toh tunda baki fara ba, base kici gaba da tuyan ba? Tasleem za tayi magana kenan wayar yafara ringing, duba wayar tayi taga unknown number ke kiranta, Inno tace ki daga man?

Murmushi da bai kai Zuciyar ba Tasleem tayi tace ba kira bane sako ne,

Inno tace Ayo bara na shiga gun yar baiwata naji koh zata kasuwar?. Tana fadin haka ta baro dakin, wayar ya sake ringing a fusace tayi picking kawai taji voice din.....

Thanks
MissDmk✍🏻
09074267236
[11/24, 07:49] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 9

Kawai taji voice din Alhajee Maikudi harda za ta yanke sai taji yace gani nazo ki fito... Jan wani uban tsuka tayi tace nadawo gida...

"What? Kina numfi kin koma gida? Shine baki gaya min ba Tasleem? Tasleem tace eh sabida banso abinda yafaru jiya ya sake faruwa, Don ALLAH daga yau karka sake kirana niba yar iska bace kuma ina da wayo na, kudi baze zama barazana agareni ba.. Nagode tana gama magana ta yanke Kiran,

Haka ya dinga kira ba ta dagawa daga karshe ya tura mata text kamar haka, yace am sorry Tasleem, I didn't know what came over me I was possessed by you please lemme make it up to you and I promise you it won't happen again.. " Jan tsaki tayi tace Hmmm zako ka sha mamaki na Alhajee idan naso wanke ka, zan yima wanki babban bargo, can tayi reply da okay na hakura.. "

Sake kiranta yayi yace yanzu kina ina? Tace ina shirin zuwa islamiya kasan walimar saukar mu rana Sunday ne... Alhajee yace Masha ALLAH to ta ina zamu hadu?tace Kasan jama'a hospital? Da ka zo ka kirani Yanzu haka ina hanya, amsawa yayi da to kafin ya yanke Kiran, murmushi tayi tace Old man kenan zaka gane baka da wayo..

Shiryawa tayi cikin hijabin makaranta, ta fice daga gidan ta shiga gidan Mai waina ta gaya ma Inno ta wuce Islamiya, minti Ashirin ta isa gun, tun daga nesa ta hango car insa aman sai tayi pretending kamar ba ta ganshi ba, saida ya sake Kiran ta,ta daga kafin tazo gun car din, ki shigo man ya fada yana bude kofar.. Makale kafada tayi alamar A'ah..

Haba Tasleem bana baki hakuri ba? Please ki shigo man walhy bazan miki komai ba, da kyar dai ta shiga tace ina kwana? Ya amsa kafin yace kinga sabida ke ban samu naje gun aiki ba yanzu dai ki rubuta min list abinda kk bukata..

Tasleem tace A'ah kabar shi, Inno ta rigada tayi min kome, haba Tasleem idan kk ce haka zan ga kamar baki yafe min bane? Don ALLAH kiyi min list yanzu ki turamin.. Tasleem tace midin na amsa abu a hanunka walh Inno kasheni za tayi tayi magana kamar za tayi kuka... Alhajee yace ya hakuri toh bani account number ki yanzu nasan ai wannan bazata sani ba koh? Shuru Tasleem tayi dan wani lokaci kafin ta bashi, nan take taga anyi crediting inta da 100k cike da mamaki take, kasa magana tayi tana rufe baki tan cike da farinciki tace Nagode Sosai Alhaj aman ai kudin yayi yawa...
Chapter 8 · 0% Book details