← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 25

Sashe 19

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsawa tayi da eh ba tare da wani tunani ba, sai kallon wayar ta keyi, salama sukayi ta nufa gidan su Meems da ihu tana murna ta nuna mata wayar.. Ihu suka dinga yi da yasa kannen Meems fitowa suna kallon su...

Yar Baiwata iPhone 14 ne walhy gaskiya ke din ta daban ce..

Tsabar murnan Tasleem ta kasa cewa komai sai rugume Meems da tayi, tace Meems bara na koma gida za muyi waya tana fadin haka ta dauki jakar ta, ta wuce gida da murna ta issa gida taci karo da Habi tayi tsalle ta rugume ta,

Habi da ta so ta fece a guje amma rikon da tayi mata yasa ta tsaya, tana sakin ta Habi ta sauke ajiyan zuciya tace ikoh sai Allah yau kuma abin akaina ya zo kenan Talatu?

Tasleem tace yau ina cikin farinciki ba Habi, har walima sai na maku kunci kun sha warr...

Oh ohni Habi na bi ina naga haske? Talatu Anya yau kalau kk? Suna cikin haka Inno ta shigo, Habi tayi saurin cewa yar baiwa tawa kizo ki bincike t..bata karasa ba Tasleem ta rugume Inno harda mana mata kiss a kumatu kafin ta nuna mata wayar... Da madaukacin mamaki suke kallonta, Inno tace a ina kk samu wayar?

Inno Suhyma ta siyomin bana gayamiki cewa suna da kirki da kudi Sosai ba? Tayi magana tana shiga cikin dakin, Habi ta matso kusa da ita tace gaskiya ban yarda da yarinyar ba, kinsa yanzu ance matan ma bin yan uwan su ma... Inno ta katse ta da cewa auzubillah Allah ya rabamu da mugun ji da gani, za tayi magana su Asiya da suwaiba suka shigo gidan, Habi na ganin ta, tace Yo hauka ma akeyi da zan ci abinci duk tofi? To saide mutum yaje yaci kayan sa, gaishe su Suwaiba tayi ta wuce daki da kyar..

By 7pm
Tasleem tayi karyan shiga school karatu kamar yadda ta Saba, suka hadu da Alhaji direct Suya spot suka wuce, tana zaune yace ta fadi abinda take so, ta gaya masa yana barin gun sai ga Yasir,

Yace Wow! Look we got here? Gold digger! Yau kuma wa aka samo ne?

Banza tayi dashi kamar ba da ita yake yi ba...

Ya kara da cewa ina watching moves na ki, kiyi ta adu'a kar na samu sa'a akanki yarinya, ganin Alhajee na tahowa yayi maza barin gun..

Alhaji ya zauna yana murmushi yace, naji dadi da yanzu kk sake dani, gaya min kina da wani matsala?

Tasleem tayi shuru can tace No,

Feel free with me Tasleem and trust me..!

I do trust you, shiyasa na amsa wayar ka...

Are you sure you trust me?

Tasleem tace yes..

How much do you trust me? Yayi magana yana kallon ta, za tayi magana waiters suka iso gun suka fara arranging table, suna zaune har 9pm kafin suka wuce ya kai ta gida,tsabar farinciki Yau har gida ta kai shi,

These where I live, tayi mai pointing gidan, sauke ajiyan zuciya Alhajee yayi, yace Alhamdulillah naji dadin da yau kk kawo ni kofar gidanku, wannan yana nuna kin fara trusting ina,

Lemme see your hands?

Da mamaki take kallon shi kafin tace why?

Baki yarda dani ba kenan?

Mika mai hannun ta tayi tana kallon sa, sai kawai taga ya fizgo ta ta fado jikinsa, da kyar ya sake ta, she voice out of cry tace please ka bude min kofar zan tafi gida,

Please I'm so sorry baby, I didn't know what came over me, please forgive me bazan sake ba..

Kasa cewa komai tayi, sai kuka ganin ba daina kukan za tayi ba yasa ya bude car din ta fita, a guje ta shiga gidan direct daki ta nufa sai kuka, tana mamaki abinda ya faru yanzu? Yau itace bakinta cikin na Alhaji? Sake fashewa da kuka tayi ta dinga tirzan lebenta...

Shikam Alhajee blaming kansa ya dinga yi wai yayi gajen hakuri da ya bita a hankali harta sake dashi Sosai kafin ya fara diban garabasa.. Rai bace yabar kofar gidan..

Inno dake dakin Habi suna kirga kudin awara, taji alamar shigowar ta, tace Yar Baiwa tawa bara naje na duba kamar talatuwa ce ta shigo, Habi tace to saida safe..

Yadda Inno ta same ta yasa ta buga uban salati da yasa Habi shigowa aguje, tana tambaya ko lafiya?

Ganin yadda Tasleem ta cire kayan jikita sai birgima ta keyi kamar wadda ta hau bori yasa Habi cewa ce suwaiba ta baki miski ta kawo min ta gaya ma Asiya, kallon Inno tayi, tace yar baiwa tawa fita kibar ni dasu, yau zamu yi taho mu gama dasu, daman tunda naga fitsara da yarinyar nan ke yi nace ba ita kadai ba ce..

Ganin Tasleem ta mike yasa Habi kwasawa a guje tabar dakin ta shige nata harda kulle kofa, Tasleem kam rugume Inno tayi, tace Inno kiyi min wanka..

Inno da gaba daya ta gama tsorata da lamarin ta tace, Idan nayi maku wanka zaku bar jikinta? Tasleem tace su suwa kenan? Inno tace ku man? Don Allah ku barmin jika ita kadai nake da ita, tana fadin haka tace ku zauna bara na hura murhu na sa maku ruwan zafi... Ko 30mins ba ayi ba ta dawo dakin ta riko hannunta tace zo muje to,

Mikewa Tasleem tayi ta bi bayan Inno suka shiga bayin, tace Inno ya rike ni a nan, tayi magana tana nuna mata boobs inta, Inno ta buga uban salati tace kice kwartaye ne suka shiga jikin ki, Ganin Inno ba gane maganan ta, ta keyi ba yasa tace ki bari kawai zanyi wanka da kaina. Fita Inno tayi ta jira harta gama suka koma daki, Idan da sabo ta saba da ganin Tasleem ba kaya har sai ta gama shiryawa kafin take sa kaya, Inno tayi fadan harta gaji,

Tana gama shiryawa ta hau kan khimar ta gabato da sallah ta, Inno kam tana zaune tana kallon Ikohn Allah, wai aljanu dama nayi sallah?

Tasleem Kwanciya tayi kan khimar har barci ya kwashe ta..
Washegari da safe bayan ta idar da sallah subhi tayi karatun alkur'ani kafin ta dauki na boko tayi, ta sake Komawa bacci sai 10 safe ta farka adalilin wayar ta da ake Kira,

Amsawa tayi da hello Farhan?

Tasleem anyi postponing tafiyar mu, sai mu gama exams...

Tasleem tace miye sa kuka fasa eh Farhan?

Farhan tace Abbana ya hana ni zuwa yace, until I vacate from school, and I called to tell you after exams we are to visit 2 countries Dubai and Paris, kowa zai rike like 2.5mil, Tasleem naji haka ta mike zaune tace uhmm?

Farhan tace Suhyma zata ji da kudin tickets na Dubai and Rayhan zata ji da na Paris, and don't forget kafin mu dawo hutun mid-semester ki dinka wasu kayan, kinsa you're not online shiyasa na kira na sanar dake...

Hadiye wani abu mai daci tayi kafin tace OK, hakan yayi ma gara in anyi exams din. Tace sai anjima Nanny na kirana, tana yankewa ta saki wani dogon ajiyan zuciya, jin message yasa ta bude taga alert din 100k daga Alhajee, sannan ya tura mata an apology text,

Kiran sa tayi direct, saida ya gama ringing kafin shi ya kira, tace what do you want from me what's your expectations?

Yace forgiveness..!

Tace no I mean soyayya kk so muyi koko harka?

Shuru yayi kafin yace kiyi hakuri baby, ba halina bane, murmushi Tasleem tayi tace turamin kudin da ya dace sai ka turamin address din Hotel din, kit ta yanke Kiran..

Koh 30mins ba ayi ba sai ga alert din 200k, sannan ya tura mata da text kamar haka; Emerald hotel room number 10, Idan kin zo I'd give you 700k just for a day...

Murmushi mugunta tayi kafin tayi reply da OK on my way... Tafi 1hour tana tsarai tsarai kafin ta zauna jiran dawowar Inno da Habi da suka je kiran malamin da zai dubata,

Ganin har Karfe shadaya basu dawo ba, yasa tabar ma suwaiba salahu cewa ta tafi asibiti daga nan zata wuce makaranta, drop ta dauka harzuwa Emerald Hotel,

Kiran Alhajee tayi da tashi go, yace taje gun reception zasu kawo ta dakin sa, tafiya ta keyi majestically harta isa reception din, gaisawa su kayi da receptionist tace room 10, receptionist yayi dariya yace daman kece Alhaji ke zaman jira? To dagga nikab din muga face inki?

Tasleem gasping tayi kafin tace is this necessary?

Mai aikin yace yes, tsarin Hotel din ne, dole computer yayi capturing dinki, tace how long does it takes? Mai aikin yace just 5mins, tazo dagga nikabin kenan yayi daide da fitowar Ali Cuba inda.....

Thanks
MissDmk✍🏻
09074267236
[23/12/2022, 11:22] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

                BY

          MissDmk ✍🏻

Page 21

Ta zo daga nikabin kenan, inda yayi daide da fitowar Ali Cuba da ga matakalan bene, ta yi saurin sauke nikabin gudun kar ya gan ta,

Zuwa yayi kusa da ita, yace Musa Idan su Hydar sun shigo kace na tafi Palace sai nan da Asr zan dawo..

Musa ya amsa da OK my Prince..

Ali Cuba na barin gun, ita ma ta fasa shiga gun Alhajee, da abin da tayi niyyar mai ba a magana amma ganin Ali Cuba, ya sa ba za ta iya zama a Hotel ba shiyasa ta juya ba tare da taji abinda receptionist ke cewa ba...

"Tana fita ta tare Abin hawa, tana cikin abin hawa Alhaji ya adabe ta da kira, ta tura mai da text kamar haka;
Alhaji ya tabbata dai jikina kk so, daman gwada ka nayi kuma nagane gaskiya don haka ka cireni a rayuwar ka kamar yadda nima yanzu zan fitar da kai a rayuwata, send your account details zan yi refunding kudin ka yanzu, and bye for good..! "

Ta tura mai da text din, ko minti biyu ba ayi ba yayi replying da, kije da kudin na barki da halinki, don nafi karfin kiyi min refunding kudi, amma saide ki bi a hankali coz haduwa mu ta biyu ba zai yi kyau ba, coz ko ta karfi sai na sameki.

Murmushi ta yi tace komin banza na wanki Gara, tsohon banza kawai...

TWO WEEKS LATER
Chapter 19 · 0% Book details