← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 25

Sashe 1

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

DUNIYA _1
[11/10, 19:35] MissDmk✍🏻: *🌍DUNIYA🌍*

BY

```(THE DMKS)

MISSDMK ✍🏻```

Book 1
Page 1

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

"Walhy sai kin shiga motan nan,idan bahaka ba inyi miki ihun barauniya kuma kinsan a kasuwa muke,wani kyakkyawan matashin sarauyi ya fada, rike da hajibin wata yar matashiyar yarinya, Wacce bazata wuce shekaru sha takwasa a duniya ba.

"Hehehe saide wata bani ba, ka dade bakayi ba nikam kaga ta fiya ta, tayi magana tana kokarin fizge hijabin ta daga hannunsa..

Kin ma isa? Nace kinma isa?walhy koh ki bani kudina koh nayi miki ihun barauniya...

"Toh Bismillah ina jiranka Mtchews aikin banza kawai in banda kasha kwaya zak... Bata karasa magana ba ya

Dauki hannu zai Mareta kawai wani ya rike mai hannu yace,Haba malam kaikam ba girman ka bane mai zai kaika fada da Macce harka dauki hannu kace zaka mareta?

Mallam ba ruwanka acikin wannan maganar,yace yana huci kamar Wanda yake shirin yin dambe da sa'ar Yinsa..mutumin yace ban gane ba?

Saurayin yace Kayi tafiyar Ka kawai ka barni da ita,

Mutimin yace Toh ka sake ta, sabida bazan taba barin aci zarafin 'ya mace a idona ba, kaga duk mutane sun zagaye ku, kai baka tsoron kaga hotan ka nayawo a social media?

Saurayin yace ba social media koh DUNIYA ce ban damu ba,ka ko san abinda tayi min ne? Tunda Nace Ka tafi ka tafi kawai, yafada yana kokarin kai mata cafka..

Mutumin yay saurin shiga tsakanin su yace,Ke Bawair ALLAH mai ya hadaki da wannan mutumin?

"Walhy daga gani na zan shiga Wancan shagon Siyayya,kawai ya fara cemin wai in shiga mota in bisa Nace akan me? ka sanni ne da zakace nabi ka mota mu tafi?
Wai shine yace min idan ban shiga ba zai min ihun barauniya kaji abinda ya faru kenan.

Toh kai malam kanwarka ce koko matar Ka? Daza ka ga Macce Haka kawai kace ta bika Eh? Mutumin yayi magana cikin bacin rai..

Wai Kai malam ina ruwanka ne Eh? Tunda kai baka san abinda ya hadamu ba,ai ita tasan abinda ya hada mu da ita kuma walhy kudina koh sisi bazai yi ciwo ba koh ki biyani ko kuma ki bini mu tafi..

Kallonsa daga sama har kasa tayi kafin tace, Nawa oo is like this man is mad ? Wana kudi kuma?

Mutum yace, Baiwar ALLAH wanna kudi yake magana akai?

Tace nifa this is my first time seeing this guy, zuwa na garin kenan Nace bara nashiga kasuwa inyi siyayya abin amfanina..

Mutumin yace Kina nufin dama bama Anan garin kke ba?

"Eh. Imma new student dazun nan na shigo daga Abuja nake,watakila ina me kama da watace?tayi maganar da gaskiyar ta..

Ware baki Saurayin yayi cike da mamakin yarinyar, kafin yace lalle ma MEEMsALY ni zaki Raina ma wayo? OK bani phone naki lemme call you and see if it won't ring? Da mamaki take kallonsa aman sai kawai ta Mika masa wayar..

Nan take ya ciro phone insa ya Kira amman baiga kiransa ya shigo wayar nata ba,Can aka amsa kiran da hello Yasir?

Sauke ajiyan zuciya yay kafin yace MEEMsALY Kina ina?

Wacce take dayan bangare wayar tace gani nan ina shiri zanzo gunka..

"OK yana jin voice naki ya canza

Mura nakeyi"

Toh shikenan sai kinzo.kit ya yanke Kiran,mayar da dubansa yayi izuwa gun budurwa dake tsaye gabansa yace, Don ALLAH kiyi hakuri walhy na dauka budurwa tace please I'm sorry.

Kaga irin Abin kenan kafin kayi jumping into conclusions think first sabida gudun Haka inji mutumin da ya raba fadan,

I'm so sorry please accept my apology walhy kamar tasu ta bace, ya mika mata phone dinta, amsa tayi tace ba damuwa ya wuce..

Yanzu ina kka yi? Ya fada yana dan susa keya..

Siyayya zanyi a provision shop Incan don banzo da kome ba, tafada maganar tana tafiya mai daukar hankalin mai kallo, dukda Hijabin dake jikinta baze hana ka gane irin kiran da ALLAH yay mata ba, wato she's endowed with figure of eight..

Bin bayanta yayi,har suka shiga provision shop, ta lodi kaya iya son ranta shi ya biya da kudin sa still yana bata hakuri,tace ya wuce walhy.

Godiya yay mata kafin yace Lemme drove you off, where do you stay off k or Hostel?

Murmushi tayi tace Off K but now I'm heading to shika, I have to pick up some of my stuffs there worry not about the ride.

Are you sure?

Yes..

Thanks once again kafin yace your name please?

Nimrah' tayi magana tana arranging ma dan dako kayan da ta siya, yace okay Nimrah am Yasir..murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, dan dako na gaba tana biye dashi, ta tsaya gun wani cosmetics shop, waigawa tayi taga

Ya Bar gun, ta sauke wani dogon ajiyan zuciya tana Hamdallah ta fito da wayanta ta kira MEEMS kina ina gani nan zuwa...Tana fadin haka ta samu abin hawa ta sallami yaron ta wuce zuwa gidan su Meems, kiran Meems tayi tazo ta taya ta shigar da kayan, direct daki suka wuce sai Dariya sukeyi kamar wa inda akasa ma laughing Gas Tasleem tace,

Walhy Meems Saura kadan da Yaseer ya gane ni, ke ALLAH ne fa ya ceceni..kinga afanin fada mishi sunan ki danayi da kuma bashi number naki K'awa, Kyalkyalcewa da Dariya sukayi cikin shewa.
Meems Bude kayan ki gani man, nan kayan wajan 50k tafada tana murmursawa..

Meems tace, Walhy K'awa ta kina wuta, Gaskiya kin shirya ma saukar waliman da kuma shiga ABU nan..

Kede Bari MEEMS ai indai nice walhy ba fariya ba koh cika baki maza a tafin hannuna suke wai shinan ya turo da 50k inje yayi s*x Dani in ya gama sai ya cikami 50k toh Gashi nan,shegen ba s*x amma naci Mai 100k..

"Hehehe TALATU buga life kenan, kina bani nishadi K'awa...

Ah ah Meems karki kuma Atoh idan ba haka ba walhy aji mu dake ehe miye wani Talatu saikace dussa? Tasleem tayi magana rai bace

Meems murmushi tayi tace Ayi hakuri K'awa, dazun Inno tazo neman ki wai ta bada kudin awaran kina dawowa islamiya sai ki je ki dauko,
Nikam K'awata ya zakiyi ne da batun awaran nan ne inda kin fara ABU?

K'awa Yadda nayi Lokacinda nabar GGSS izuwa DSS haka zanyi man, kema kinsan waccece Tasleem base natsaya ina bata bakina ba..

Meems ta dara kafin tace, Shegiya K'awa ta walhy zanyi missing inki idan nayi aure

Ai kece wai wani aure ana zaune kalau dudu nawa muke dazaki wani ce zakiyi aure nifa idan kka ji na bude baki Nace zanyi aure toh nagama Tara abinda zan Tara ne wollah.

Meems tace, Toh ya zanyi K'awa ta kema kinsan Baba Haka yake aurar damu nice kadai ma nagama secondary acikin yammata gidan mu,

Tasleem tace Cabdi, ALLAH ya kyauta yana academic doctor ace yana ma yaransa auren wuri wai ma na tambaye ki nawa muke ne? we're not up-to 18? bamu ma Gama sanin Mecece *DUNIYA* da abinda ke cikinta ba, ke bara kiji, ni sai nagama degree kafin zan wani dibo aure Yanzu dai ga wannan kayan ki diba naki ki ajiye min nawa tunda saukar Saura sati biyu..

Meems tace keda zaki fara zuwa school ina ni ina taba kayan ki K'awa? Ki ajiye kawai anjima zansa Abba ya kawo miki..

Hmmm Meems, kinsa Yanzu meke damu na?
Meems tace A'ah sai kin fada K'awa,

Rashin kaya walhy Meems ke damuna..

Rashin kaya fa kk ce? Duk wannan kayan naki?

Wanna Kaya? Kina ji jiya nan wasu students suka zo siyan wara naji suna gulma wata wai takalmi daya take sawa.sannan kuma akwai wata wai zallar abayas take sakawa koh sau daya bata taba repeating ba wai kulum kwatance akeyi da ita, nima inso samu ne inyi fiye da nata, nan ne zan kara sanin Yammata masu kudi fiye da wanda nayi a DSS kinsan ABU Ance harda yaran senators da yaran wasu Presidents na other countries and me I want to get more exposed to worthily things kema kinsa halina kuma na duba savings na 60k ne aciki..

Meems tace Hmmmm Hakane kam Don Yanzu inda kina so Ayi dake sai kina wanka kina harkan Manya toh Yanzu ya zakiyi kenan K'awa?

I think Kiran Yaseer zanyi Nace Mai 50k yayi kadan yakara min inaso nayi gyara yanda innazo bazai barni na tafi ba, koh ya kka gani?

Meems tace, Cab ke kina tunanin zai baki ne bayan yau yakamata kije kuma baki je ba ?

"Hehehe maganin shi zanyi ai wai shi Maye, yaga kaya zai lasa toh saide ni na lashe shi,

Meems tace K'awa ina jiye miki tsoro kar watarana yakamaki, kinsa mazan Yanzu da kulafaci akan abinda suke so?

Meems bar wannan maganar plz, ALLAH ya fishi ai baze taba bashi sa'a akaina ba.

Meems tace toh in Hakane ki kara jalin waran man? I think tanan kudin zai fito harki siya kaya koh?

Kede Meems Bara na gwada ki gani ta amsa wayar Meems tayi dialing number sa bugu daya ya dauka tace
Hello baby kana ina?

"Gani nan kwance ina jiran zuwan ki sabida na shirya tsaf Don tarairayar ki my baby,

Kashe ma Meems ido tayi kafin tace ALLAH ko baby? amma bana tunani zan iya zuwa yau tayi maganar cikin shagwaba,yace Mai kk nufi da Haka kuma baby?

Cikin shagwaba tace Toh relaxer danake afanin dashi ya koma 10k kudin saloon 2k kasan yanda wajan mu yake ai ba sauki Saura na siya perfumes dashi Yanzu Saura na gyara fata yadda da ka tabani zakaji wanni laushi kudin bazasu kai ba baby,

Toh bana ce sai kinzo zan baki sauran ba? Kema kinsa money is not my problem kide zo kawai ayi a wuce gun..
Tace Nifa A'ah Gara Ka kara min kudin yadda Dana zo baza Ka barni in tafi ba

Wow! dagaske kk Yi MEEMS?

Ehman baby nifa so nakeyi nayi ma kwana biyu,yadda zamu ji dadin mu..

Wow! Toh bara na tura miki 50k Please kizo da wuri sabida nakosa baby,

OK baby, thank you in shaa ALLAH zaka ganni

Nan take ya tura 50k, yana turawa tasa shi a blacklist suka Kyalkyalce da dariya
MEEMS bara na wuce kafin wannan mayen yafara damuna da kira
Chapter 1 · 0% Book details