← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 15

Sashe 9

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tayi maza tace yi hakuri, kiyi
hakuri maryam, aure kenan kowa kika ga yana
zaman shi hakuri yake yi, hakurin data rinka
bani sai yasani tsanan ta, kukan da nakeyi sai
naji baba abinda nake os irin in ganni a
manbilka gaban iyaye na da yan uwa na da
basu iya fushi dani, tashi ki je ki kwanta banyi
mata musu ba, abin da naji kenan don kuwa
nasan shin ya dace dani har dare yayi ina
dakin umma, ta shigo tace mun yaya maryam,
zaki yi hakuri ki koma dakin kine ko kuwa?

Nace mata a'a, tace to yi kwanciyar ki,
zaki sha tea ne? nace a'a na riga na koshi ta
juya ta fita na koma falo ta zauna tana hirarta
da Hafsat.

Sa'id yayi sallama ya shigo ya nemi wuri
ya zauna ya sake gaishe ta sannan yace mata
maryam tana nan ne? tace mishi eh, ya cigaba
da zama jimawa can yace mata akwai abinci
ne? tace banyi da kai ba don haka duka na bawa
almajirai, ya dan yi shiru jimamwa kadan sai ya
sake cewa to maryam zo ki san 2binda zaki
girkamun da sauri don yunwa nake ji, tace a'a
ba zata ko'ina ba, yanzu ta riga tayi wanka ta
kwanta bai sake cewa komai ba sai jimawa can
yace anan zata kwanane?

Tace mishi eh.

Malle ta tashi ta fita, jimawa kadan ta
shigo rungume da food flask ta ajiye ta sake
komawa ta kawo miya da plate da ruwan wanke
hannu ta ajiye fhishi ya kalli, malle yace mata
ina kika samo mun abincin? tace na dumamen
baba ne na safe na kwao maka zanje in sa ruwva
yanzu sa: a sake tuka wani tuwon, ta juya ta fita
sa' id ya kama cin abincin sai da ya koshi sai
yace unmma dama akwai abincin kika hanani ?
tace to bazan hanaka ba akan me? ai ni
kwanakin nan ma da kake zuwa kana cin abinci
anan ina baka ne don ban san yajin cin abincin
matar ka kake yi ba, sai dazu da Isahura yake
gaya mun yace ai laifi tayi mun tace eh ai dama
hakan da kayin shine dai dai ya gama hirar shi
ya tashi yace sai da safe tace Allah Ya tashe mu
lafiya.

Tun sa'id yana zuwa yayi hira ya tashi
yace sai da safe yayi tafiyar shi a dalilin wai shi
laifi nayi mishi har ya gaji ya yiwea umma
magan kan bai san dalilin dawowa na nan
wurin ba tace tro ai ka makara tun da baka
nemibayani ba, tun farkon dawowanta sai yau
kaje kayi ta zaman ka kai kadai ba sai kuna tare
zata rinka bata maka rai ba, sa'id juyin duniya
da umma akan in koma dakina, shi abin ya
wuce a wurin shi, tace ai ita wanda tayi
baiwuce ba a wurin ta, ganin haka yasa ya
dawo ta wurina yanaso mu sasanta in yaso ni
ince zan koma nima nayi matu'ar share shi
takaici ya kara kama shi in ya shigo ya gai da
umma sai ya nemi malle ta kawo mishi abinda
yake bukata ko gaishe shi nayi baya ansawa.

Rannan ranar wata lahadi ne da hantsi sai
da ya kammala, sannan ya shigo wajen karfe
goma da rabi muma mun kammala har nayi
wanka nasha kwalliya ta cikin wata doguwar
riga yana gama gaida umma ya kira sahura tazo
ta tsuguna tace mishi gani ya mika mata sako
yace ita da hafsat suje su kai inda ya gaya musu
sukace to, suka tashi suka tafi suna fita sai ya
Kalli umma yace umma ban san abin da nayi ba
kika rike maryam anan kwanaki da yawa har
kuma banga alamar zaki ce ta koma ba don
Allah in wani laifi nayi miki a gaya mun tace
a'a nikamme zaka mun tsaka ninka dai kai da
matar ka yace to umma indai ni da itane da ta
kawo kara na ai sai akirani a gaya mun ba'a
rike taba ni a hakan sai naga kamar an mara
mata baya kan wulakancin da ta mun.

Wulakancin me tayi ma ka umma ta
bukaci sani bai boye mata abin da ya faru ba
har lokacin kuma da alamar bai rabu da
sakaicin abin ba, saboda yanda yake jadda da
fadin ina samin ta dashi, mene ne dalilin da
jikin ta zai dauki rawa saboda ta ganshi ? in har
tasan tana mishi irin wannan Son me yasa....
umma ta katse shi ta hanyar yi mishi tsawa kai
karfa ka kawo mun shirme, kai meysa ka shigo
mata da shi cikin gidanta?

Yaya kake nema ka
takurawa yarinya?

Dama akan wannan ne ka
tsira gaba da ita?

Umma ta rufeshi da fada ta
inda take shiga ba tanan take fita ba, yayi ta
saman bata hakuri da kyar ya samu tayi shiru
yayi maza ya tashi ya fita don kar yaci gaba da
zama ta sake taso wata maganar.

Washegari da safe bayan nayi wanka na
gyara jiki na nazo na samu umma don in gaishe
ta sai ta kalleni tace mun yau kam zaki koma
dakin ki don kar mijin ki ya maidani wata iri ko
kuwa?

Ban amsa mata ba, sunkuyar da kaina
kasa kawai nayi ki rinkayin hakuri ki kuma
rinka girmama mijin ki kina mishi biyaiya nace
mata to umma sa' id yayi sallama ya shigo ya
nemi wuri ya zauna ya gaida umm anima na
gaishe shi ya amsa farai farai na tashi naje
kawo mishi abin karyawa na same shi yana
cewa umma to ai yau sai ta koma ko tunda
maganar ta kare, tace zata koma amma zan
gaya maka ban yarda da irin wannan fushin
naka ba, in ta maka laifi kawai ka rinka gaya
mata ai na san zata baka hakuri yace to umm
azan kiyaye ya dan kallen ai zaki dawo wuri
kiyi girki ko ba sai dare ba?

Kan in bashi amsa
sai umma tace mishi a'a ba kin cin abincin kake
yi ba inta girka?

Na dan sunkuyar da kaina kasa
cikin ladabi nace mata kiyi hakuri umma ki
barni kawai inyi mishi, ya dan kale ta cikin
murmushi don Son ganin yanayin ta bata canza
ba, sai kawai naji tace to tashi ku koma can din
yanzu, nayi maza nace kiyi hakuri umma tace
a'a ai. kinga yanzuma ba wani karyawa yayi ba
kuje .can ki shirya mishi abin karyawa Allah Ya
kiyaye na gaba yace amin, umma Allah Ya kara
girma ta tashi ta fita yace to tashi muje mana
maryam nace a'a sai da yanma yace haba
maryam bayan umma tace mu tafi yanzu nace
gaskiya ina jin kunyar umma yace to bari in
leka miki tsakar gida in gani in bata nan sai
kawai ki wuce abinki a hankali ba mai jin takun
kin ace mishi to yayi maza ya tashi ya leka y
gani sannan ya dan yafutoni da hannu nazo kin
gani ba kowa yi ki wuce nace to nayi maza na
lwuce na shiga wurin mu.

Sa'id yana shigowa yasa makulli zai
kulle kofar da dan key nace a'a yaya zaka kulle
kuma?

Yace sai kinyi adadin kwanakin da kika
yi can baki shiga gidan ba, nima ramawa zanyi
badai ke komai aka miki sai kije ki kai kara
gurin umma ba?

Ita kuwa tace miki kiyi
zamanki ba tare da tayi binciken abinda kikayi
ba, saboda ke tana son kin a zuba mishi ido ina
kallonshi cikin tsoro yai yi muirmushi yace kar
ki rinka jin tsoro na maryam girmamawa ne
tsakani na da ke, kin gane?

Nace uh ba tare da
na saki jiki ba muje kiyi mun abin karyawa,
kinji ko?

Baki lura kwanakin nan na dan ragu
ba?

Ban tanka mishi ba na shiga kicin ina
shirya mishi shima ya shigo yana tayani, wunin
ranan bai fita ko'ina ba, muna tare a gida duk
kokarin shi bai wuce nason ganin dashi mun
koma kamar da ba wanda ba'a wani dauki
lokaci mai tsawo ba, hakan ya yiwu.

Kammala karatuna na yaki da jahilci da
kuma koyon girki sai na zama babu abinda
nakeyi in banda zaman gida naso kwarai ace
sa'id ya bar ni na shiga makaranta, don ina
matukar sha'awar karatu amma sam yaki bisa
hujjar da bai wuce kishi ba.

Wai wannan ma
abinda yasa naga ya sanyani don matane ke
tafiyar da dukkan al'amuran inna tashi da safe
kan kace meye wannan?

Na kanmala dukkan
aiyuka na bani da wani abinyi sai ko in dan
dauko littafi ina karantawa wajen buda baki,
wannan dalili ya sanya shawarar da hajiya
salma take yawan bani na in nemi sana' ar da
zan rinka yi yayi matukar karbuwa a zuciyata
sai dai sa'id ne bai yarda ba, babu yanda banyi
da shi ba, babu irin rartashin da ban yi mishi ba
yaki, rannan dai na yanke shawarar zuwa in
samu umma kan maganar nayi mata bayani tace
to bari sai ya dawo zata hadamu muyi maganar
nace mata to.

Da daddare kuwa yana falon ta malle
tazo ta kirani nasan maganar ne don haka da
zan tafi sai na tafi mishi da abincin shi ina shiga
na ajiye mishi tare da yi mishi sannu da zuwa
sannan na nemi wuri na zauria nace wa umma
gani, umma tace maganar da kikazo kika mun
ne nayi mishi maganar shine yace yana son
sanin abin da yasa kika matsu sai kinyi sana' ar
akwai wani abinda ya rage miki ne?

Na sunkuyar da kaina kasa cikin ladabi
nace mata a'a, umma ba abinda nake nufi kenan
in ranshi y abaci yayi hakuri ni dai kawai na
gane wuni nake yi a zaune bana aikin komai, ni
kuma ban saba haka din ba, bana jin dadin
zaman ina bukatar wani abinda zan rinkayi don
in rinka motsa jikina, ni shine kawai bukata ta.

Umma tace to kai kaji bata raina abinda
kake mata ba, saboda haka in kaga baka son yin
sana'ar iat a to ka barta mana ta rinka zuwa
makaranta tare da su sahura tunda gashi hart a
dan fara iya karatu da rubutu, ai ina ganin ba
zai mata wahala ba, yace zanyi tunani tukuna
akai, tace to Allah Yayi mana zabi na alheri
yace amin.
Chapter 9 · 0% Book details