Sashe 11
Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda daaga ranar na soma shirye
shiryen zuwa manbila nayi shiri, nayi tsaraba
na adana kudi saura sati guda muyi tafiyar sa'id
ya kawo kudi masu yawa ya bani yace inyi wa
mutanen da nake ganin sun dace tsaraba, bance
mishi na riga nayi ba don kar yace nayi gaban
kai na sai kawai na karba nayi mishi godiya an
shirya tafiyar ne akan zamu jene mu kwana
biyu mu dawo, ummace tace a'a tunda na dade
banje gida ba, haka ba sai abarni inyi sati biyu
ko uku kafin in dawo don in samu damar
ziyartar dangi so sai, don haka sai sa'id yace to
in shi zai jene a lokacin zai dawo dai dauko ni
don haka tasi'u ne zai je ya kai ni, ni kuwa sai
na roke shi nace to ya bani izini in tafi da
sahura da jamilu tun da dukan su suna cikin
hutu bai hana ba, itama umma murna tayi da
taji na fada haka dan banda kudin daya bani
babu kuma wanda bai yiwa dinki ba a rigar mu,
ya kuma kawo kudi yace in basu kowa da nashi
ga kuma tsarabar su doya su kayaiyakin
masarufi iri-iri haka nan umma da baba sumna
dukan sunyi mun tsaraba.
Daga yin sallar asuba muka bar gida duk
da nauyin motar da irin karfin tafiyar da aka yi
mun isa rugarmu ne bayan sallar magariba
rannan kusan babu wanda ya gane n1 a gidan
mu, abinda kawai suke fadi shi ne 'yan-uwa
mijin sengel ne suka zo kuma ;da yake basugaa
malle ba sa id yace wai za'a bar umma ba kowa
sai zai zo zai taho da ita, ardon yazo wurin
yana y1 musu sannu da zuwa ya ganni yace ikon
Allah "din seungel hande to wuro gun?
"
Ma ana seungel ce yau a gidan, nace eh baffa
sai kuwa gaba daya yara suka fara ihu suna
oyoyoyoyo, kai tsaye dakin ardo na shiga yayin
da su tasi'u suka nufi masaukin da akayi musu
ardo yana kallo na yana murmushi yace seungel
ta zama matar hausawa, na taya shi murmushin
Cikin yanayin jin kunya nace mishi a'a baffa, ai
ni kullum bodice ina kuma alfahari da hakan ya
sake wani murnmushin yace hakane seungel
amma fa kar ki rinka dauka ko bodi yafi wanda
ba bodi ba kin gane ? nace eh baffa muna nan
wurin muna hira ni da ardo har yaya jauro ya
dawo daga cin kasuwar kara daya tafi ya shigo
ya durkusa yana gai da ardo, daya gama sai
yace mishi naga mutanen su seungel ne sukazo
don na hangi mota, ardo yace mishi eh ba gata
ba yaya jauro ya gyara tsuguno ya shiga gaishe
ni ina amsawa cikin zuciyata kuwa kamar in
kyalkyale da dariya don na tabbatar bai gane ni
ba sai daya gama gaisuwar sai yace kai to ita
seungel din fa? na kyalkyale da dariya nace
haba yaya jauro in owa bazai gane niba kuwa
ai ya kamata kai kam ka gane ni ardo yace
kwarai kuwa seungel tunda yana iya sheda
saniyarshi duk inda ya shiga ai ko ya kamata
yafi sheda ki nace yauwa baffa ni da ardo
mukayi dariya shi kuwa jauro sai kallona yake
yi yana fadin Aradu kamar ba seungel ba.
Rannan kwana mukayi ni da ardo da
yaya jauro muna hira, sai da akayi sallar asuba
sannan nikam na nufi dakin maizube na
kwanta, ita kam sahura tana dakin bodejo su
tasi'u da jamilu kuma suna bukkar da aka sauki
sa'id suma aka sauke su, hidima sosai akayi
tayi masu.
Bayan sha biyu ne na tashi nayi wanka
nayi sallar azahar sannan na karya naga su
tasi'u sannan na dawo dakin maizube muna hira
bayan naje na gaida innan su yusuf da yakubu
suka shigo dakin na jawosu jikina na zauna
dasu ina cewa ikon Allah, baffa yayi yan
tagwaye maizube tayi murmushi tace aj kuwa
dai shima abinda yake fadi kenan muna cikin
hirar maizube tace mun ai kuwa kunzo dai dai
yau saura kwana goma ayi bukin sumaye, na
rike baki.cikin nuna alamar mamaki nace wato
goggo inda bamu zo ba da shike nan sai ayi
bamu sani ba, tace eh to dama dai ardo yana
cewa watakila mijin ki ya samu daurin auren
don kusan lokacin zuwan shi kenan mukayi
hira da maizube sai famar tarairaya ta take yi
tana taji dani ina fitowa daga dakin ta na nufi
dakin jume tana ciki ta mulmula kiba tayi
gwanin kyau da ita shi kuwa yaya jauro yana
gefe sai dogon wuya na samu wuri na zauna
muka gaisa muka kuma shiga hira ina tanbayar
ta mutanen gidan su da kasuwa tana bani labari
tanfar dai babu wata rashin jituwa a tsakanin mu.
Kwanan mu uku da zuwa na soma kai
ziyarar dangi babu inda banje ba cikin dangin
ardo da na bodejo har da na maizube duk wani
tanadi na tsaraba da nayi kuwa dama tun daga
nasu bodejon danan 'yan-uwan su duka ban
bantaba har kasuwar manbila da gidajen su
sarkin fawa duk naji inda duk muka je kuma
yaya jauro ne mai yiwa wadan da basu gane
niba bayani, seungel ne fa, wannan da tayi sharo
da majo din nan sai kuma a kama fadin kai
jau.o shi kuwa yayi ta fadin Aradu, to zan
muku karya ne ? suce a'a a'a jauro ai ba sana'ar
ka bace, abin mamaki ne dai yake da yawa har
shagon idi tela naje.
Na kai mishi shima tashi tsarabar tare da
iyalin shi.
Muna zaune a gida ni da yaya jauro a
bayan bukkar maizube muna hira na kalli yaya
jauro cikin kulawa nace mishi yaya jauro me ya
same kane?
Naga duk ka fita haiyacin ka kamar
ba kai ba, dubi yanda ka rame ka kare ka zama
sai dogon hanci.
Ya dan kalleni yace kar ki gayawa kowa,
nace haba yaya jauro ai yanzu nib a yarinya
karama bace, yanzu yace hakane seungel, jume
ne take damuna da fitina, gashi yanzu tace wai
ni din bani da lafiya bana haihuwa har ma ta
matsamun sai da muka je wurin wani mai
magani ya bamu magani yace in dinga sha ni
kadai wai abin a wuri na yake, ya sake dan
waiwaya don ya rada mun magana kuma mai
maganin yace wai shanu biyar za'a bashi nace
bazan iya ba, don ardo ba zai yarda ba, ita jume
tace wai za'a iya diban shanun shi ardo bai sani
ba, to kuma naga kamrr kafar shanu tayi cikin
duwatsu shin e nace ko har sun diba ne? ban
sani ba shi yasa rannan naje kasuwar kara don
in gani ko zanga shanun a can ban gani ba.
Na zubawa yaya jauro ido cikin
tausayawa nace kai yaya jauro kai kam baka
dace dasamun mata ta kirki ba, ina ganin
maganin abin kawai shi ne akara aurar maka
wata matar su zama su biyu watakila kadan
Samu sassauci, yaya jauro ya kama ihu yace kai
seungel wannan shawaran naki na banzane, ni
inacema zaki ce ne a mayar mun da kitso na
kawai dama jume ta koma gidan su amayer?
Maka da kitsonka yaya jauro?
Ka koma
saurayifa kenan?
A ina kaga ana yin haka
bayan ka riga ka tsufa kuma kace kana son ka
dawo saurayi, ai bazai yiyu ba, kai dai bari
zanyi tunanin abin da zamuyi akai yayi maza
yace amma kar kice zaki zage ta don tace inna
hadata dakewa wai zaki tafi ki barmu nace to
yaya jauro.
Ina hira tare da bodejo dadi ya kamata sai
faman murmushi take yi tace mu muna nan
muna jiye miki zama cikin bare ashe ke kina
can abinki Allah Ya hadaki da miji mai kirki,
na kalli bodejo kawai na taya ta murmushin
cikin zuciyata ji nake tanfar in dan fada mata
wani abu game da irin zaman da muke yi da
sa' id, amma na kasa fada mata, ji nake tanfar
zan huda ciki nane in yiwa kaina, su dai su
bodejo a yanzu babu wani wanda suke so fiye
da sa' id in an tanbaye su mutumin da yafi kowa
kirki a duniya yanzu zasu iya cewa sa'id ne, to
in gaya mata laifinshi wuri na to akan me?
Nayi
maza na sake tsuke baki na nayi shiru muka ci
gaba da hirar mu mai dadi har na samu na sako
maganar dake damu na ta yaya jauro da matar
shi, inna tayi maza ta yamutsa ido tace kul!!
Kar ki sake kawomun maganar shin ace Allah
sarki inna in baki taimaki yaya jauro ba wa zai
taimake shi?
Tace uh uh zai sa raini ya shiga
tsakanina dasu kan fitowar da yakeyi yana
kwana a waje dana mishi fada sai yaje ya
kwashe ya gaya mata haka da nayi mishi
maganar yaje yaga wata yarinya yar gidan su
takko innace zan rinka sa ido akan su raina ni
kawai zai sa ta rinka baci na sake lankwashewa
ina baiwa inna hakuri nace in kin yi niyyar
taimakon shi inna kinsan abin da zakiyi.
Satin mu guda a manbila sai ga sa'id da
malle sun iso maimakon sai munyi sati biyu da
yace, gaba daya hankalin mutanen gidan mu ya
koma kan malle saboda yanda ta canza musu
tayi matukar yin kyau ta girma ta zama 'yar
gaye kwalliyar English wears take yi, don shi
sa'id irin kayan da yake sai mata kenan, ga
kanta akowane lokaci bai rabo da kanannan
kitso ga ribbon masu kyan gaske.
Na samu sa'id a sabon dakin da ardo ya
gina don saukar shi nace yaya akayi kuma yau
na gan ku?
Ni da na dauka sai sati mai zuwa
zaka zo ya kalleni cijkin natsuwa yace ai gidan
ba dadi in bakya cikin shi, basa hakuri, nayi
nace bari dai inzo muyi zaman bakuntar tare na
kalle shi kawai nayi murmushi cikin zuciyata
kuwa cewa nayi kamar da gaske, in ina nan
kaki yarda a zauna lafiya yanzu da na barma
gidan kabiyoni kana fadin gidan babu dadi.