← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da sa'id baizo da shirin bukin
sumaye ba amma hidima sosai yayi ya kuma
kyaleni dai da aka gama bikin sarai na raka
sumaye gidan mijin ta har muka maida ita daga
yada sawun da tayi wanda tun daren farko tayi
shi sannan yayi mun maganar yaushe nake
ganin zamu tafi?

Nace aiko gobe kace mu tafi
sai kawai mu daga, tun da an gama komai yace
to zanje in samu baffa zan gaya mishi ina so
zuwa jibi in Allah Ya Kaimu sai mu tafi, nace
mishi to ina shiga gida na gayawa maizube don
nasan itace zata shirya mun tsaraba.

Ina zauna tare da inna ta a cikin dakin ta
dambun naman da nazo musu da shi na samu
tanaci na bude jaka ta na debi kudi masu yawa
na bata ta karbesu tana kallonsu tace a wannan
jejin namu me zanyi da wadannan kudin in dai
ba shanu kike so in kara ba, nayi maza nace
mata a'a inna ina baki kudi ba shanu nake so ki
kara da suba, kashe su nake so kiyi ki rinka cin
dadi ta kalle ni tayi murmushi tace in rinka cin
irin wannan abin kenan da kika kawo mana?

Nasan inna gatse tayi mun don kuwa babu
abubuwan dana kawo musu ariga takaici ya
kama ni ina ma dai kusa dasu nake da kuwa na
jiyar da su dadi da irin girke-girken da na iya.

Rannan a dakin ardo na tare don hira,
kusan raba dare muka yi mu biyu, muna zaune
ardo ya kalle ni yace mun yaya dai seungel ke
da jauro shiru babu wani motsi?

Allah dai Ya sa
mas' alar ba daga wurin ku take ba, bance mishi
komai ba sai da naji yayi shiru sai nace mishi
baffa baza ku taimaki yaya jauro ba?

Ardo yayi
murmushi yace ai jauro bani a cikin al' amarin
shi kuma tun da bodejo ta zuba mishi ido kowa
ma zai gaji ya zuba mishi ido.

Sannan ina so ki
gaya wa mijin ki yayi kokari ya dibi shanun shi
a wannan lokacin nace mishi to.

Sa'id da kanshi ya samu ardo yayi mishi
bayani kan shirin da yake yina zuwa diban
shanun nashi, sai dai yana bukatar ardo ya dan
kara hakuri kadan yace to Ubangiji ya nuna
mana lokacin yin hakan yace amin.

Tsarabar ruga sosai aka shirya mana nayi
sallama da yaya jauro cikin tausayawa na kawo
kudi masu yawa na bashi nace mishi ya kai
cikin yashi ya boye ya rinka diba kadan kadan
yana bata kar ya yarda ya bata lokaci daya yace
ai ba zaiyi haka ba.

Mun dawo gida da kwana uku nayi barin
ciki wata uku hankalin sa'id yayi matukar tashi
baran ma da likita ya bayar da dalilin barin
akan tafiya mai nisa da nayi da 'dan karamin
ciki ina kwance kan gadon asibiti amma bai
fasa fadanda yake yi ba, wannan ma ai
ganganci ne da rainin wayo, ai kin san kina da
shi kika kama hanya kika luluka wannan tafiyar
kikaje kina ta kaiwa da kawowa a jeji.

Umma tace to maryam kuwa inda tasan
da haka ai bana zaton zata yi wannan tafiya
tunda ita ma ai zata so ta ga kwanmta yaya
babba tace a'a umma infa yarinyar nan tayi laifi
ki rinka bari ana nuna mata kuskuren ta, hauka
kenan take yi in har zata dauki ciki wata har
uku a jikinta bata san da shi ba, haka fa
kwanakin baya akace mun wai tayi barin sati
shida sanadin barekatan da ta sha, shima
kuskure ne? bata fi kowa sanin irin wannan
abin a tunda ita ai "yar magori ce.

Umma ta mike tsaye tace mata bar
asibitin nan tunda ke baki iya kwantar da fitina
sai dai tayar da ita, wuce ki tafi ki bani wuri,
yaya babb
a ta wuce ta tafi tana fadin soyaiyar
da kike yiwa wannan yarinyar tana sawa kina
rufe idonki kan cutar sa idu da takeyi inma
hidimar da take yi kike dubawa ai tana wanke
kaifi.ne da ruwan jikin shi, tana fita umma ta
koma kan sa'id ta rufe shi da fada kai kam
abinda kake yi har kunya yake bani ni ban san
abinda yake bani in ban san abinda yarinyar
nan take maka ba da kowane lokaci kake fusace
da ita me take maka ne?

Me take maka da yake
hanaka tausayin ta?

A irin wahalar da maryamn
tayi yau ace wai bar kana iya yi mata tashin
hankali ai kuwa abin da ban mamaki yace
umma cuta ta takeyi tuni kuma na dade da sanin
tana nadamar aure na wannan bari-barin da
takeyi duk da gangan take zubar da cikin don
bata son haihuwa da ni, umma ta kama salati
cikin kaduwa da jin mamakin kalaman shin ai
kuwa cikin rai na naso ta tanbaye shi cutar da
nake yi mishi sai dai batayi hakan ba.

Nima
kuma banyi ba don kuwa ba dani yake maganar
ba bayan hakan kuma tun farko ban nuna musu
ido na biya ba ni kaina al'amarin sa'id yana
matukar bani mamaki, ban taba zaton inna aure
shi irin zaman da zamu yi da shi ba kenan,
kulluma cikin kokacin kyautata mishi nake
amma kuma duk a banza bana burge shi ko anyi
kamar zai dan lafa sai kuwa abin ya dawo wani
lokacima kiri kiri ya rinka nuna manr tsana da
kin jinni a sarari ni dai ina kallon shi ina kuma
yin addu'a kwana biyu nayi a asibitin sannan na
dawo gida har lokacin bai fasa fushin da yake
yiba, nima kuma ban kula shi ba ina cika kwana
bakwai na koma kan sana' ata sai dai ban bari
hakan ya hanani shirya mishi abin shan ruwa
akan lokaci ba har akayi sallah ba, ba wani shiri
muke yi da shi ba sai dai kuma hakan bai
hanashi yimun dukkan abubuwan da suka dace
ba, tun daga wannan lokaci sai na samnu kaina
cikin halin yawan yin balri akai akai abinda
yayi matukar sanyani cikin wani hali ga dai
wahalar da nake ciki gashi kuma duk lokacin da
hakan ya faru sai mun shiga wani hali na fitina
tsakani na da sa'id, saboda zargina da ya keyi
da cewar ni nake zubar wa don bana son
haihuwa da shi.

Rannan ya same ni a dakina ina
kwance akan gadona ya nemi Wuri ya zauna a
gefen gadon yace mun maryam wurin kin a zo
inaso muyi Magana ta gaskiya dake, kin san dai
Allah ne ya hada mu ko ba haka ba?

Nace
mishi haka ne, yayi bayanai masu gamsarwa
sannan yace mun ina so ne kiji tsoron
Mahaliccin mu ki gaya mun gaskiya mene ne
laifi na a wurin ki da kike nuna mu kiyaiya da
tsana?

Nace da nayi maka me?

Yace kin fini
sanin abin da kike yi da dalilan ki na yin hakan.

Ko ba komai dai kina gwadamun kiyaiya ta
hanyar boye mun kina da ciki sai in kin kasa
zubar da shi cikin sirri sannan in sani na kalle
shi cikin natsuwa nace mishi yanzu yayan
sahura da gaske kake yin maganar nan cewa ni
ke zubar da cikin da nake da shi?

Yace to in
bake bace wane ne?

Tunda nayi-nayi dake in
kinga kina dashi ko wata daya ne ki gaya mun
ni zan san matakin da zan dauka akai amma kin
Nace to ina sanin ina da shi ne? ni ina
al'ada kowanne wata uku uku ne ta yaya zanyi
in san da shi?

Ya danyi shiru jimawa can yace
to shikenan kiyi hakuri, daga wannan lokacin
zaki rinka zuwa yin test kowanne wata don in
kina dashi a gane da wuri nace mishi to.

Tun daga wannan lokaci na fara zuwa
gwaji duk karshen wata, rannan likita ya
tabbatar ma sa'id ina da shigar ciki sati uku ya
fadi abubuwan da zan kiyaye cikin su kuwa har
da yawan aiki ya kuma shawarci sa' id daya dan
saurara mun a wannan dan tsakanin yace to,
muka dawo.gida sa'id yace in barwa sahura
gudanar da al'amuran, aikin mu gaba daya in
yaso sai arage yawan abinda akeyi nace mishi
to, ya kira sahura yayi mata bayani tace mishi
aima ba sai an rage ba tunda akwai masu aiki
sosai ni da shi muka koma cin abincin umma
safe, rana da dare don kuwa bana aikin komai
daga kwanciya sai ko sallah ko ruwan wanka
ma shike hada mun wata ran ma ya tsaya ya
cudani muna cikin haka har cikina ya wuce
wata biyar ya shiga na shida ya riga yayi kwari
sai na gayawa sa'id ina so in rinka taya su
sahura aikin da suke yi don aikin yana yi mata
yawa sai takai goman dare bata kwanta don ma
tana da kokari yace to kar dai taimakon ya
zama mai yawa, nace mishi to.

Abinka da
kaddara kwana na hudu da komawa kan aiki na
sai na wayi gari ina Ciwon mara nayi maza na
gayawa umma ta hanzarta kaini asibiti shi kuma
sa'id jamilu yayi mishi waya ya sheda mishi
cewar ina asibiti ya iso asibitin ne dai dai
lokacin da aka fito da ni daga dakin haihuwa
aka kawo ni kan wani gado aka kwantar da ni
yava dai umma?

Cikin kotsawa ya tanbaye ta,
kan ta bashi amsa sai nos din nan ta sake
shigowa tana tambayar ame zaku karbe shi?
Chapter 12 · 0% Book details