Sashe 4
Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai masa zanci da kunun gyada
don zafi nake ji, bazan iya shan tea ba, na
kalleta kawai nace kema kenan da garin kune
kike jin zafin to balle ni kuma dana fito
manbila' yankin da kowa yasan irin niimar
dake cikin shi, me zaki karya shi?
Ta bukaci
sani nace ni na koshi ta zuba mun ido tana kallo
na to ai mu ko bako baya cewa bazai ci abinci a
gidan mu ba, umma ta karbi bakuntarshi ba kale
ke umman ta shigo dakin da alamar wani abu
tazo dauka tace me kika zukawa yayar taki
sahura?
Naji dadi da sahurar bata ce mata nace
mata bazan ci koma1 ba, tace waina zan fara
zuba mata da kunun gyada ta zuba tace muci a
tare in kin ki mu in cinye ince tare mukanci
kinga ba mai gane cewar ke kadan ki ka ci.
Muna ci muna kallo sahura na mun
bayanin firm din tana kuma gaya mun sunayen
mutanen na asali da wanda suka fito suna
amsawa wanda nikam gani nake tankar mutum
daya ne kawai yake ta faman caccanza kaya irin
sakin jikin da sahura tayi dani da kaunar da ta
nuna mun na farat daya, gashi kuma dama ban
girme taba, bata girmen ba, sa'o'in juna muke
sai nayi matukar jin dadin mu'amala da ita.
Sa'idu ya dawo dakin alamar shigowan
shi kenan daga inda ya tafi kannen shi sukayi
mishi sannu da zuwa, banji abinda ya gaya
musu ba na dai ga kawai sun yi maza sun tashi
sun fita ya karasa shigowa cikin dakin yace
sahura yaya bakuwar taki dai?
Tayi murmushi
tace lafiyar ta kalau ya dan kalle ni da gefen ido
ya kawarda fuskar shi yace sai dai banga
alamar kin iya saukar bako ba.
Tayi maza tace
da nayi me yaya?
Yace to bikuwa a takure?
Ta
makure wuri daga ido duk hawaye da gani
kasan ta tasa abubuwa masu yawa atare da ita?
Tace to ai ita taki shafa mai yadan tabe baki
yace to zuba mun kunun tsamiya a kofin can ki
bani ki kumate ki samo mun abin nan tay
maza
tace to ta zuba ta bashi ta fita ta tafi dauko
abinnan din da yace mata wanda nayi ta zuba
ido inga dawowan ta inga menene abin nan
din?
Yana ganin ta fita ya ajiye kofin kunun ya
matso gabana ya tsuguna ya sakan mun wani
irin murmushi daban taba sanin ya iya ba a
hankali cikin Magana mai sanyi da natsuwa
yace Allah sarki, yau maryam din yaya jauro ta
zama maryam din wannan mutumin ko ba
sunan da kike kirana da shiba kenan?
Na kara
sunkuyar da kaina kasa ba tare da nace mishi
komai ba, ya dan rage fara'arshi yace hidimar
bukin nan ta sanyaki matsananciyar rama
maryam gashi kuma banga alamar kina shirin
yin abinda zaki daidaita da umma cikin sauri
ba, ita umma da kike gani zaka ji dadin zama da
ita in har zaki kiyaye al'amuran ta, nayi maza
na dago kai na kalleshi don inji al'amuran ta
yace ita din Fata son musu da taurin kai duk
abin da tace miki kiyi ki rinka yin kokari kina
yinshi nace mishi to ya sake kallona yace zaki
ci abinci kuwa ko kuwa kin fiso inje nemo miki
gittere?
Na kawar da kaina kawai ya mike tsaye
ya kwallawa sahura kira nan da nan ta dawo
yace mata kizo kuyi kallon ku bari in karo
muku yasu kasunan tace mishi to.
Muna nan a daki da sahuira kallon mu
mukeyi ko abinci aka gama turowa akeyi
akawo mun inma Sallah zamuyi tare muke
alwala muzo muyi sallar tare amma kuwa duk
lokacin da zata shigo dakin zata miko wani abu
tare ko nono ko nama ko dai yayan itace.
Washegari da yanma su tasi'usuka dawo
daga kai iyaye na gida da sukayi sun kuwa
dawo cikin farin ciki tare da fadin alherin da
ardo yayi masu na baiwa kowa kyautar saniya,
tasi'u ya shigo har inda nake ya durkusa ya
gaisheni sannan ya miko mun wani dan kurlin
abu cikin tsunma yace wai gashi inji yayan ki,
nayi maza na sa hannu biyu na karba, na
kwance shi zoben yaya jauro ne na azurfa daa
yake matukar so ya aikomun da shi nan naji
kewar yaya jauro ta sake kamani nayi ta kuka
sahura tana ta bani hakuri har ta gaji ta mike
tace bari inje in kira umma ko yaya sa'idu don
kar suzo suce ban iya kula da bakuwa taba
sannan ne na share hawaye na.
Kwana biyu muna nan a haka aikin mu
kenan ni da sahura kallo sai ko ciye-ciye wanda
bai da lokaci kowanne lokaci ci mukeyi, saboda
abubuwa ne ba masu nauyi ba, su inabi tuffa
kankana cob-cob ganyaki kowanne lokaci
zakaji umma tana cewa sahura dauko abu kaza.
Kwana na hudu a dakin umma, rannan
ma nayi wanka na jawo kaya na na manbila na
sanya sahura ta kalle ni tace Allah Ya sauwaka,
kullum kina cikin wadannan matsastsun kayan
masu kama da ajikin ki aka dunka su sai kace
bamu miki kayan aure ba?
In baki sani ba in
gaya miki akwatuna hudu yaya sa'id ya shake
da kaya, gudumowan da akayi mishi ko tsinke
biai samu shuga ba bagasu can a wancan dakin
umma ta tarasu, ban san sa'id yana falon a
zaune ba sai da naji yace sahura bakuwar taki
kikewa wannan carin?
Tace ai yau ba bakuwa
bace yaya tunda ta wuce kwana uki na kuma
yimata alkunya na wadancan kwanakin yayi
dariya yace kina da gaskiya, to in karbo muku
dinkunan ku dai kenan?
Tayi maza tace mishi
eh ya kuwa tashi ya fita zuwa can sai gashi ya
dawo da kaya har da kayan shafe-shafe da na
gyaran gashi da turaren ka dukan su na kayan
lliyar jojo ba, kai rinka gani sai kayi zaton
bai yi kayan aure ba.
Sahura tazo ta zauna tana dubawa cikin
murna da farin ciki kai kace itace matan.
Da daddare umma ta shigo tazo ta zauna,
abinda bata taba yi ba don haka nima na kara
natsuwa na kuma rasa yawan hankalin da yake
wurin kallon da nake ganin tanfar har abada
bazan gaji da shiba tace mun maryamina wuni ?
nayi maza na gyara zama cikin natsuwa kasa
amsa gaisuwar da tayi mun don haka ni na
shiga gaishe ta tana amsawa da aka sake
natsu
wa sai tace mun inaso ki dauka ke da
sahura duk daya kuke awuri na babu wani
banbamci in Allah Ya yarda kuma ni bazan
banbanta ku ba sai in kece kika ki yarda da
hakan.
Duk wani wanda yayi mili wani abu a
gidan nan da bai yi miki dai dai ba ki gaya mun
in kinga abinda kike so inyi miki shima ki gaya
mun ina kuma so in gaya miki bakuntar ki ta isa
haka nan gidan mijin ki ne, kiyi walwalarki ba
ayi ta ganin ki a takure ba, nace mata to.
Ranar juma'a da safe bayan mun idar da
sallah, umma ta shigo dakin na gaishe ta sai
tace ke sahura taimaki maryam ta tsefe wannan
kitson nata, tace to muka zauna da kibiya gudu
biyu ni ina tsefe gefen dama ita tana tsefe gefen
hagu, kitson amare mai matukar kyau ne akan
nawa wanda sai da aka zabo gwanar makitsiya
tayi mun shi inda cikin dangin mu nayi aure
wannan kitso da yasha manshanu kafin a tsefe
shi.
Sahura ta kidime ganin gashina, tace
waw!!!, dama ashe boye gashin kitson yayi?
Don Allah anti maryamwai manshanun da kuke
shafawa kankune yasa gashin ku yake tsawo da
kyau haka?
Nace mata eh kema sai kiyi ta
shafawa umma tana daga falo tace ai kuwa kin
bata amsa mai kyau.
Maryamn Sahura ce ta
taimake ni na wanke kaina da ruwan shampoo
yayi fes, sannan a sanya dirayar hannu ta
lousar mun da gashin bayan an tajeshi tsaf, ya
bushe ta shafe mun shi da mayuka kala-kala
sannan aka shafa nayi wanka na fito na dawo
daki na zauna na shafa mai na shafa hoda
la'akari da 'yanmayin kwalliyar mutane da
nake gani ya sanya dana shafa sai kawai na
saka kwalli na bari haka, sahura ta sake
warware gashin nawa tana tajewa tana fadin
kai, umma zo ki ga gashin indiya kawai, yaya
sa'id yaje ya auro mu gani dama kike kama?
Ta
sake dawowa gabana ta tsura mun ido cikin
nazari, jimawa kadan tace 'manisha patel' tace
cikin dinkunan da yaya sa'idu ya karbo miki
zaki sanya ko cikin' kayan auren ki?
Bari in
kawo miki kayan auren ki gani nayi maza tace
mata a'a sahura, a'ina kika ga mutum yana
kallon kayan auren shi?
Ta kelkele da dariya
tace to wa zai sa miki in aki kalla ba?
Hi'um ai
nikam dani za'aje yin soyaiyar kayan aure na,
nace tafdi, siket da pant din dana sanyan sune
na farko dana taba sanya irin su don haka ba
karamin dadi suka mun ba, sahurace ta tilastani
sanya brazier tunda ban taba sanyawa ba,
sannan na zaka /ata doguwar riga mai rowan
madara tasha ado ko da ban san darajar kaya ba
nasan rigace mai daraja na dinko gyaran tana
yafe a kaina bayar, sahurata nade mun gashin
ya zama tanfar gammo abaya ta dauko turare
tana fesa min tana fadin kai ashe dai yaya
sa'idu yasan abin da ya gani, bari Allah Ya
kawo yaya babba yau ta ganshi itace mai cewa
bata ga abinda ya gani ba ajikin ki da yaje yayi
wannan wahalallen aure na cin mutuncu nace
mata waye yaya babba?
Tace itace babbar
yayar mu nan take sai na tuno da maganar su da
Mahmud dana taba ji ina cikin wannan tunanin
Sahura ta katseni ta hanyar gaya mun kinga
wadannan dogayen rigunan duk da tsadar su
Buda goma sha biyu yaya sa'idu ya zuba miki a
Cikin kayan ki, ai zaki sha ado tayi maza ta juya
ta dauko madubi ta miko mun kalli kanki don
Allah kiga irin kyan da kika yina karbi madubi
na kalli kaina ni kaina da kyar ya rage ince
mata ko dai bani bace na dai daure nayi shiru.