← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sahura ta fito daga dakin umma itama
tasha kwalliya irin kayan jikina ta sanya nayi
murmushi nace kingan ki kuwa/ sahura kin
zama tanfar.....,.... .. zan fasda tayi maza ta
katseni tace uh uh ban san zuga wai don kar
ince kin cionye kwalliyar ta shigo ta debi
saurian abincin da aka zuba taci gaba da
rabawa.

Muna tare da umma a kicin har aka
sauko daga sallar idi baba yana shigowa ta fita
ta bar aikin ta nufi wurin shit a dan jima kadan
kafin ta fito tace mana kije ki gaishe shi da ni
da sahura muka shiga muka mishi barka da
sallah shi kuwa yasa mana albarka da zamu
fito sai yace sahura ga barka da sallar ku ta
tsaya karba ni kuwa na fita.

A cikin umma tana shirya abincin da zata
kaiwa baba sahura tazo ta miko mun mikakkun
kudi na karba na kirga nace duba daya ne,
sauran fa?

Ta dan yi wani murmushi na sakarci
alamar wai dabara take son yimun tace kin ga
aika baba ko bah aka ba da yake mudin mun
riga mun shiga hannun ki ko bakya shafa komnai
mun riga munji mun gani ko kuwa anti?

Umma
ta kwalkyale nda dariya ni kuwa nace ban
kudina ban yarda da wannan wayon ba, tace to
ke dai Allah dudu hudu ne kin gani?

Umma
tace dubu hudun ne aka baku kika bata dubu
daya bata kudin ja'ira mai waton banza in
banda itama ai shi Allah dari biyar zai baki
goron sallah, sahura ta yamutsa fuska tace a'a
unmmau ni da anti mun fi kusa har kince ta mata
da miji ba'a shiga tsakanin mu.

Umma ta dauki tiren data gama jera
abincin ta fita tana fadin karbi kudin ki maryam
dari biyar zaki bata, shima sai kin miko dama
tana fita sahura ta miko mun kudin nace mata
rikesu sahura tace Allah?

Tayi Tsalle cikin
murna tace na gode Allah Ya kara girma.

Wajen bayan salalr azahar ne sa'id ya
samu shigowa cikin gida a dalilin tsayawar da
yayi a a wajke aka yanka dabbobin da aka yi
laiyan da su a gidan, nima sa'id yayi mun laiya
da tikekken rago lokacin nan kuwa mun hadu a
falon umma muna ta hra dasu jamilu da yayan
yan uwansu da suka zo barka da Sallah sai da
ya shiga wurin baba sannan yazo falon umma
har zai zauna sai umma tace ma shi ai da wurin
ka kaje ka dan huta, Allah dai Yasa baka manta
da wani cikin mutanen cikin gari ba a rabon
naman yace aiban tsaya an gama ban a shigo su
tasi u suyi rabon in sun dawo tace to ya wuce
zai tafi nayi maza na wuce shi a dalilin da nayin
na kulle wurin nayi maza nasa key na bude
mishi waui ya shige i kuwa in dawo wurin
hirar mu tunda tana mun dadi sai kawai naga ya
turani cikin gidan ya jawo kofar ya rufe na daga
ido na kale shi yayi matukar daure fuska kekam
Allah Ya ta:make ni kiyi dabara da wuri a ina
kika ga ana zama wurin hira a kyale miji shi
kadai?

Baki bani abinci ba, banga kwalliyar ki
ba, amna kina sauri ke zaki koma nace to kayi
hakuri na biyoshi muka shiga na kawo mashi
abincin na shirya mushi wanda baici ba sai da
yayi wanka ya canza kayan jikin shi sai ma nayi
zama na nan mukayi wasannin mu da sukafi
hirar da na baro dadi da daddare da nayi wanka
kayan da sa'id yayi munna sanya kayan da
kwalliyar tawa tayi mishine ya sanya yace mun
dauki gyalen ki muje ki kira sahura da Hafsat
suyi mana rakiya zuwa ungwa ne dani sai dai
ina matukar boyewa tunda na nuna zumudi na
a sarari kan zuwa wata ungwa yace ya fasa.

A falon umma ne naji yana ce mata zamu
je gidan yaya babba da yaya balaraba da Alhaji
sunusi wanda duk wadan nan gidajen an kai
musu abincin sallah tace to sai kun dawo.

Gidan yaya balaraba muka fara zuwa don
shi ne a kusa, hannu bibbiyu ta karbe mu cikin
murna da farin ciki ita da mijin ta da kishiyar ta
abin gwanin sha'awa aka danyi hira da bar
kwanci har kishiyar ta tan ace mishi ashe dai da
hikimar ka da kaje can ka samo matar ka gyara
abinka, sukayi rahar su da zamu tafi mijin su
alhaji baba yayi mana alheri itama kishiyar ta
haka hakannan yaya balaraba kayan shafa ta
bamu cikin leda mai giwa shi kuwa sa'id sai
mita yake yi waibasu gajiya da hidima, ga
kayan sallah sunyi ga kuma irin wannan
dawainiyar.

A gidan alhaji sunusi kuwa wanda
na fahinci abokin harkokin sa'id ne, sai dai ya
girme sa'id din, matarshi hajiya salma hannu
bibbiyu ta karbemu cikin mutunci da
karramawa tayi ta juna da hira dama kuma mun
riga mun dan saba da ita, saboda duk lokacin da
alhaji sunusi zai zo wurin sa'id tare suke zuwa,
ai ke kam maryam abin naki gwanin sha'awa
gashi har sa'iusu yaje ya dauko miki yar
kanwar ki tana debe miki kewar gidan ku, gashi
ya rike miki ita gwanin sha'awa nace aima ba'a
wurin mu take ba, a wurin umma take ta rike
baki tace ke don Allah nafa dade inajion labarin
kirkin mahaifin su a wurin mutane ko da yake
wasu suna cewa wai mallake mijin nata tayi ta
hanashi yin ayre, murmushi kawai nayi ban
bata amsan komai ba, da zamu tafi itama kayan
shafa ta bamu, mijin ta kuma kudi, mukayi
godiya mun fito tana mana rakiya take tanbayar
sa'id irin wannan iya tsakina da amarya, tayi da
zaka yarda ai da sai ta rinkayi ana kawowa
super market dina ana saidawa yayi maza yace
Allah Ya sauwaka tun bat agama amarciba ta
soma wata sana'ar kwabe-kwabe gaba daya
akayi dariya, mijin ta yace rabu da ita tanace
kowama irin tane tun bata shekaraba a giudan
nan ta hana kanta sakat wai to ga mai sana'a
tace a'a ya daifi ai in zauna ina jiran sai an bani.

A gidan yaya babba kuwa muna shiga
gidan zumudi na ya ragu a dalilin irin kallon da
tayi mun na sheke sheke na samu wuri na zauna
cikin natsuwa na gaisheta sai wani kallona take
yisama da kasa jimamwa can ta gaji tacewa
sa'id iko sai Allah, yau ga inda baki suka zo
suka fi 'yangida kyan gain ji yarinyar da aka
kawo kamar za' a hure ta ta fadi tazo ta zama
wata dindimemiya in ba wanda ya sani bama ba
zaice itace ba to ga kanwarta ma.

Sa'id yayi maza ya rage fara'ar dake
fuskar sshi, yacemata ina maigidan da amarya?

Tace suna saman su, ai ni gaskiya kaci mutunci
na sa' idu ace a baka yarinya a gidan nan amma
kayi mun irin abinda kayi to ni dai in gaya har
yanzu ban gaya nusu tasawa lenyi ba cewa nayi
wannan din sadaka aka baka don haka in ka dan
huta kadan za'ayi wannan din.

Bai ce mata
komai ba, ya mike yace in sun sauko kya gaishe
su kuma munga kayan sallah Allah Ya kara
girma.

Mun iso gida wajen sha daya ne ammna
duk da haka sai da muka kara wata hirar a falon
urima kafin muka iso wurin mu
Anyi sallah kwana uku rannan na caba
kwalliya cikin wata shadda ta kayan aurena ina
falon umma muna hira bayan sallar azahar sai
sa'id yayi mun waya wai inzo in kawo musu
abinci yayi bakin cikin sauri na mike na taho
nayi maza na shiga kicin dina na shirya abinci
tire daya kaya ciye ciye na motsa baki tire
daya ga ku.na abin sha nayi Magana da shi
yazo ya debi tirarrukan guda biyu yace mun
biyoni da guda biyu yace n.un biyoni da guda
daya ana dauka nabi bayan shi zuwa falon na
shi, ina shigo mukayi ido biyu da Mahmud, nan
take naji lanfar zuciyata tana neman tsayuwa
saboda firgita da tayi jikina ya dauki rawa har
bansan lokacin da na saki tiren dake hannu na
ya kife ba, da gudu na fita na nufi dakina nayi
maza nah au gadona na ruhu sai karanto
addu'o'i na keyi saboda tsorata da nayi
mutufmin da na gani a matsayin Mahmud da
kuma maganganun da ya gaya mun suka dawo
mun shin Mahmud na gani ko kuwa dai ta
maizuben ne da tace wai cikin aljanun dajin
mune wani yazo mun cikin kamannin Mahmud
din, ina cikin wannan hali-sai ga sa'id ya shigo
dakin a fusace wai mene ne wannan abin da ki
keyi?

Fusatar da yayi ya kara tayar mun da
hankali nayi matukar kankame jiki na cikin
wani Karin tsoron saboda ban taba ganin shi
cikin wannan halin ba, nan take naji zazzabi
mai tsananin zafi ya kama ni kwana biyu ajere
ina kwance amma sa'id ko lekawa yace mun ya
jiki?

Baiyi ba bal;le ya wani muna mun kulawar
shi sai umma da sahura ne suka yi taji dani ita
umman ce ma tasa tasi' u ca jamilu suka kai mu
asibiti aka saman mun magunguna har naji
sauki bai sauko ba, nima kuwa na shareshi
muka koma zaman kowa harkar gaban shi
kawai yake yi, ni kam na gaji da gabar, a dalilin
ban saba ba, ban taba samun kai na cikin halin
da wani baya Magana da ni ba, na girma ne a
giodan mu bani da abokin fada balle a/ce ga
wata rana da wani zai ki Magana dani, sai da na
bari ya gama shirin say a fita ba tare da yayi
mun saliama ba, kamar yarda ya tsiri yi, sannan
na tashi na shiga wurin umma ta daga ido cikin
natsuwa ta kalleni tace zazzabin nan ya ramar
dake da yawa maryam ko kuwa kina da wata
damuwar ne baki gaya mun ba?

Na kale tan ace
a a umma sai dlai duk da a'an da nace sai da
hawaye suka zubo mun sharrr daga idanuwa na.
Chapter 8 · 0% Book details