← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sa d yayi maza ya mika mata babbar rigar gi
anan nos ta juya ta tafi ba tare da ta karbi rigar
ba taje ta kawo shi cikin tasan da suka sanya shi
tun farko umma ta zubawa tasar dake hannun
sa id ido tana kallon shin an take hawaye suka
soma zuba daga idanun ta tana fadin iko sai
Allah, na miji ne an gama mishi halittar shi har
ya fara girma ji hannuwan shi komai nashi irin
naka ne. a hankali yace ba komai umma, kiyi
hakuri bari in kaiwa baba shi sai abinne shi,
yasa hannu ya dauke ya nade shi cikin rigar shi
ya juya ya tafi ya barni tare da umma wacce ba
sai an gaya mun ba ita kanta hankalin ta yayi
matukar tashi da abinda ya faru wannan karon
sa'id kam tunda ya sa kai ya fita da yaron da
aka bashi bai sake dawo wa ba, har bacci ya
sake dauke ni sai farkawa nayi naji yaya babba
tana fadin a'a umma, tunda dai hakane ni na
tafi zan iya cewa a wannan lokacin sahura da
tasi'u ne kawai basu juya mun baya ba, na
shiga wani hali na kuncin rayuwa, kalaman
mahaifiyata na game da auran bare ayi nesa da
gida sukayi ta dawo mun inda ba kusa da
dangina da iyaye na nake anya irin wannan zata
sam ni?

Na kasa hana hawaye na zuba nayi ta
kuka nan take naji babu abinda nake so irin in
ganni gaban iyaye na, ganin ina kuka ya sanya
umna ta sassauto daga bacin ranta ta shiga bani
hakuri kwana daya da wuni nayi aka sallame ni.

Muka dawo gida ban yarda na zauna a dakin
umma ba, kamar yadda tace dakina kawai na
wuce a wannan lokacin naji ina bukatar zaman
kadaici, tunda abinda na zabanwa kaina kenan
tunda naki zama cikin dangina.

Ina zaune a dakina sa'id dai kullum
yakan gaishe ni ne da safe, sai kuma wata
safiyar ita kuma umma dama ba shiga wurin
mu take yi ba tunda ta shiga ta duba ni sau biyu
bata sake ba sai ko ita da baba su turo malle ko
sahura suzo suce suna gaisheni, yaya jiki?

Ince
da sauki.

Rannan ina kwance a dakina bayan
azahar inajin shigowar sa'id da yaya babba ga
dukkan alamu da ga gidan ta suke sai naji tana
cewa ina matar gidan take?

Yace ai inajin bacci
take yi tunda babu motsin tat ace to ai gara
kasan abinda kake ciki don wannan yarinyar ba
sonmu take yi ba, aure shekara hudu amma har
yanzu bata yi sha'awar ta bar mana konmu mu
gari ba shekaran jiya dana je gidan mansura
naga yan ta gwayen ta sai da naji kamar kwalla
zata zubo mun nace da yanzu wadannan
kyawawan yaran mu aka haifawa su yace
yantagwaye fat a Haifa ko?

Tayi maza tace eh
baka gamsuba kyawawa ga lafiya mace da na
miji amma ita wannan sai aukin neman kud
tunda yake ita dama fatauci tazo yi ta samnu
kudi ta hura gida ayita kara mata shanu sa'id
yar dariya yace kina yawan fadin maryam
tama sayen hanu a garin su ina ganin don baki
taba zuwa gidan su bane da kin san ita mai
shanu ce, sha
u basa cikin abinda zata saya.

Tace shanu suna ransune ba dukiyar gado
bane?

Ai daga gan wannan ne su koma gun
wancan ba iya cinsu suke yi ba sai dai suyi ta
wahala dasu kuma ni koma dai mene ne ina so
in gaya maka yana da kyau ka kara aure ko don
kaji dadin zama da ita tunda ka nace kana son
ta in taga wata tazo bayan ta tana goya danta ai
watakila tayi sha'awar ita ma ta haifa, ita mace
in ka gane ba so take ka karu da ita ba ai sai ka
kama kanka, yace mata hakane.

Mas'alar da ta ke tsakani na da sa'id sai
ya baiwa yaya babba alamar shigowa cikin
lamarin aure na tayi ruwa teyi tsaki kullum tana
tare da shi tana cikin gaggaya mishi maganganu
yana kara fushi akan fushin shi na da nima inna
fara sana'ata tun safe sai na kanmala komai
nake tashi bani da wani lokacin barin aiki na
saboda inyi na gida sai wajen umma yake
aikawa a kawo mishi abinci ko kuma yaje can
yaci.

Rannan ranar lahadi ne ya wayi gari yana
gida ban tsaya na shirya mishi abin karyawa ba
ina cikin aiki na sai naji yana kwala mun kira
na dauraye hannuna naje na same shi nace
mishi gani ya tsura mun ido wai ke me ya same
kin e kike wani cika kina batsewa ana kallon
ki?

Nace shi ne dalilin kiran nawa?

Yace eh ko
yayi kadanne?

Nace shi ne dalilin kiran nawa?

Yace eh ko nayi kadan ne ? nace a'a ba ka yi
amma kasan ina da abin yi in shike nan ina so
zan tafi yace to ba laifi jeki, na juya na fita na
koma wurin aiki na sai kawai na ganshi ya fito
da saurin shi yan matan da suke tayani aiki ya
kira yana rabawa kudin wata bayan banfi
kwana hudu da biyan su ba, da ya gama basu
sai yace kuje gida sai an neme ku ko, sukace to
suka kama hanyar fita ya leko dakin da nake
yace fito daga nan na hana wannan sana'ar
daga yau, sahura ta ruga da gudu ta shiga cikin
gida wurin su umma sai gasu sun shigo tare
meke faruwa ne sa'idu?

Yaya zaka koran mata
ma'aikata ka hana ta sana'ar ta?

Ya fito daga
ciki ta samu ta shiga ta ganni a tsaye ina kuka
kuzo nan ku biyoni muje can ni da shi muka
bita sahura kuwa ta tsaya tana kokarin ganin
munyi cake din da aka riga aka kwaba don kar
muyi asarar shi.

Muna gaban umma sa'id yana
bayanin sana'ar ta ishe shi, baya anfanin taba
don taja mishi asara iri iri da bacin rai don
haka daga yau bai yarda ba, bai yarda a sake
yin wani abu don sayarwa ba, tunda ya lura ma
sana ar tawa tana kara bani damar raina shi,
umma ta juyo gare ni ban iya ce mata komai ba,
kuka kawai nake yi ta gaji tayi mana nasiha
tasallame mu muka tashi muka tafi bayan sa'id
ya dage kan cewar zan koma kan sana'atane
kawai bayan mun zauna mun ajiye sabbin
sharuda ni da shi.

Shikenan daga wannan lokacin na koma
irin zama na na farko bana komai daga wanka
sai yan aiyukan da basu taka kara sun karya ba,
sai ko kwanciya, a haka dai sa'id ya lallabani
muka shiry a a dalilin bani da wata hujja ta kin
daidaitawa da shi, abubuwan da suka faru
maganar sana ata kuwa yace shikam a yanzu ya
zama mishi wajibi ya kiyaye duk wani abinda
zai iya kawo mun mas'ala inna sake samun
wani cikin tunda shikam ya matsu yaga ya
samu kwanshi, to ni kaina haihuwar nake so
duk da nikam ina boyewa amma da za'a tona
cikin Zuciyata babu mamaki a tarar na fishi
matsuwa da ita, don kuwa gani nake tanfar
haihuwar itace kadai zata rage mun mas'alar da
nake ciki, gani kuma anan daga ni sai malle
kullum kuwa inna ta kan gaya mun cewar in
Allah Ya baki haihuwa kiyi tayi ki tara yaya da
yawa sai kiga kin fita cikin kewa.

A wannan lokacin sai muka yi matukar
zaman lafiya ni da sa'id lokaci mai tsawo babu
wani abun da ya sake faruwa a tsakanin mu
abinda bai taba faruwa ba nikamna saki jiki na
sosai ganin irin yanda yake tarairaya ta da ji
dani sai na zama akowane lokaci in banda kara
son shi babu abin da nake yi.

Rannan ya dawo daga wurin harkokin shi
da yamma naje na same shi a dakin shi nayi
mishi sannu da zuwa ya amsa na tanbaye shi
za'a kawo abinci yanzu ne? yace a'a ai, kin san
na karya kenan na fita nace eh yace yanzu dai
zo tukuna in miki bayanin fili na, nayi maza na
matsa kusa da shi na zauna yace to wannan
dana gaya miki na hanyar dan batta kudin shi
sunyi yawa don kin san na gaya miki babba ne
kwarai dari da dari wajen goma sha biyu ne
aciki ni kuma zan sone in sayi flin da zan iya
katangewa in gyara komai don in tura manbila
a debo mun shanuna in zuba in kuma bude
wurin kaji don haka zan bar wannan inje in
duba na can hanyar wudil in naga zan iya sai in
saye shi.

Nace to amma shi wannan din zaifi
dacewa da kiwo sosai, tunda shi yayi nesa da
garin nan, hanyar wudil aiya zama cikin gar
sannan nan din a yalwace kwarai yake ina
ganin da zaka yarda sai ka dauki kudin da suke
account di na ka hada kayi amfani da su tunda
inka hada ai zasu gama maka aikin yayi maza
yace a'a a'a, bar kudin ki kawai, na kalle shi
cikin natsuwa nace mishi akan me ? akan ni ba
abokiyar rufin asirin ka bane ? yace a'a ba haka
bane, nace to na sha ganin ka kana rancen kudi
wurin su yaya babba da yaya balaraba, wato
nice da ban?

Yace ba haka bane, yayi mun
bayani mai tsawo sai dai ban gamsu ba ganin na
matsa da hakan sa' id ya amince da karbar kudi
na, amma a matsayin rance in ya samu zai
maido mun su, nace mishi to kwana uku bayan
nan ya dawo gida da rana ya kirani dakin shi
ina shiga na tarar ya juye tulin kudi akan gadon
shi dukan su takardun naira dubu dubu ne,nace
kai kai ina ka samo mana kudi haka?
Chapter 13 · 0% Book details