← Book details Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aranar mallam da bakin ckn abin yakwana yaci alwashin yanda Aisha ta b'ata musu rai itama nata ran saiyafi nasu b'aci don saiya had'ata Aure da d'aya daga ckn Almajiransa kotak'i ko taso dolenta ta Amince,kuma dolenta ta fad'i kowaye yai mata ckn domin anemoshi abashi kayanshi inta haihu domin baxa a d'au zunubin zubda ciki ackn gidansaba.......

_muje zuwa_

~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

~*Pg 17-18*~

Washe gari da k'arfe 1:30 pm Aminatu ta dawo daga makaranta agajiye sunyi jarabawar biology dukda taxo musu da sauk'i bakamar yadda suka zataba Amma tilis tashigo gidan asakamakon kwalleliyar ranar da akeyi ga yunwar da take cknta

Tana shigowa kicin ta nufa dama tayi sallah a sch ta zubo abinci a plet shinkafa da miyane tadora cokali akai tafuto tanufi d'akin inna A'i

Tatarar innar tana sallah tazauna akan kujerar innar 2siter tafara cin abincinta anutse

Inna ta idar da sallar takalli Aminatu tace "a,a Autar mallam har kun taso?

Aminatu tace" walh mundawo inna da yunwa yau nadawo bantsaya yin Karin kirkiba shiyasa yunwa takwak'uleni dayawa

Inna tagyad'a kanta tace"dafatan jarabawar batai wuyaba ko?.

Aminatu ta girgixa kai tana murmushi tace"inafa wuya inna walh taxo da sauk'i anwatso mana simple questions munkuma amsa suka sai fatan samun Sa,a

Inna tace"to ubangiji Allah yabada Sa,a

"Amin,inna yanaga motocin su Yaya ak'ofar gida kuma ba week End ba, badai sune suka dawoba?

Inna tace" sune mana ba dole ki gansuba mallam ne yai musu waya kan abinda Aishar tayi zama za,ayi yau akanta yanxu haka ma suna masallaci sai kawunku ya iso zasu shigo gidan

Aminatu tace"hhhmmm koma dai menene Aunty ita tajanyowa kanta nasan mallam baxai mata ta dadiba,walh inna tun farko nake gayawa Aunty Aisha akan sabuwar d'abi,ar data tsiro nafutar dare intaga bakwa tsakar gidan bata dawowafa sai kusan anrufe gida saitakai shadaya awaje nasha yi mata magana akai nanuna mata rashin kyan hakannai mat nasiha Amma bata d'auka saidai ma ta hayayyak'o mini tun daga rana takarshe datayimin kashedin nakyaleta kada nasake yi mata magana akan hakan Shikenan nai gum nazuba mata ido,kuma Ni ina zargin akwai wani danaji tana waya dashi waishi Adam watakil shine yai mata ckn nan Dan gunsa take futa

Inna tace "babu musu a zancenki Ummie don nima sau 2 ina kamata da futar nan datake Aisha tanada kunnen k'ashi yanxu gashinan kwabarta tayi ruwa Dan mallam ya rantse cewar baza,a zubar da cikin nanba k'auye zaikaita gun danginsa ta haihu acan inyaso saita dawo yad'aura mata Aure da Almajirinsa abinda ta haifa kuma amik'ashi gun ubansa.

Aminatu tayi ajiyar zcy tace"Allah yakyauta to yanxu wannan wa gari ya waya,karatun da taketa kulafuci zatayima baxata samuyiba Knn,

Inna tanisa tace" to aidama koba wannan abin datayi mallam yahanata yace bayada ra,ayin barin "ya mace agabansa tayi dogon karatu gara inkunje can gaban mazajenku kwayi insun bari.

Aminatu tace" ummm dama Ni inna ban zurfafaba domin wanna ma Dana samu nagode wa Allah Yaya ma baya son inci gaba yace sana,a zanyi acikin gidansa

Inna tace"hakan yayi Allah yataimaka Aikin iya d'inki da sak'ar kayan sanyi duk sai a sai miki komai kitafi dashi

Aminatu akullum Hankalinki k'aruwa yake halayyarki tana burgeni Allah yai miki albarka

Aminatu tace"Amin inna,

Ta mike tafuta dontaje d'akinsu ta cire uniform sauransu jarabawa 1 danm suna saka interval atsakani da tuni sungama

Aminatu ta tarar da Aisha a zaune tayi tagumi ta zauna kusa da ita takalleta kawai awani b'angaren tana bata haushi wani b'angaren kuma tausai take bata bayama dataji irin hukuncin da mallam zai yanke mata ayau

Aisha ta janye tagumin datayi tace"Ummie ina ckn damuwar wannan abin danayi walh nayi matukar nadama da danasani gashi ina fargabar zubar da ckn nan domin ance anashan wuya wajen zubda ciki kokuma ka rasa ranka nagayawa Adam yace zubarshi za ayi...

Aminatu takatseta"zubar da ciki kuma Aunty?

"Kema kinsan mallam baxai yardaba gara tun wuri kidaina tunanin xubarshi don mallam yace saikin haifeshi abaiwa meshi...

Hawaye suka zubowa Aisha tasa bayan hannunta tagoge tana fad'in" nashiga uku Na lalace walh baxan bari nahaihuba gara.....sallamar inna takatseta"tokuzo maxa yanxu d'akin mallam kowa ya hallara Ku ake jira.

Gaban Aisha saida ya fad'i cknta ya d'uri ruwa yau tasan Allah ne zai kwaceta takalli Aminatu tace"Dan Allah Ummie kibani addu ar addu,ar da zanyi kona samu nutsuwa ckn raina.

Aminatu tace"kiringa fad'in innalillahi wa inna ilaihir rajiun dakuma lahaula wala quwwata illah billahi alaihil azim,

Nan Aisha tayi caraf tahauyi Aminatu tarigata yin gaba harta shige d'akin itako tunda tajiyo muryar Kawu daga ckn d'akin saigabanta ya tsananta faduwa domin tasan shine farkon yin cuta agareta shiya fara keta mata haddi koma meye dai shine sila tabbas ayau inhar suka matsa mata zata b'allo masa ruwa domin zata futo fili tagaya musu cewar kawun ne yai mata cikin aibai isa ya musaba tunda yasan shiya fara cutarta yarabata da budurcinta.....

~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_👉🏼 *Nabilancy Luv* ©💘

~*Pg 19-20*~

Asanyaye zuciyarta Na dukan uku-uku ta d'aga labulen d'akin mallam d'in da sallama abakinta tashiga kanta a k'asa bata d'aga kai ta kallesuba ta rab'a kusada Aminatu datake ak'asa gab da kofa ta zauna

Suma yayun nata ak'asan suke a zaune sai wurga mata kallo suke

Inna A'i da inna halima suma suna gefe guda ak'asan a zaune

Kawu yana kan kujera one siter mallam ma akan kujerar yake

Gyaran murya mallam yayi kana yace"to kamar yadda nafad'a muku irin cin zarafin da Aisha ta janyo min Na cikin shege agidana to nikuma natarukune domin kuji irin hukuncin Dana yanake akanta sbd baxan d'auki reniba tunda tazama mekunnen k'ashi itace ta fara b'atan gida tanaso sunana ya b'aci a unguwa Dan haka Na yanke hukuncin ta tafi can k'auye gun "yan,uwa ta zauna harta haihu inyaso saita dawo gida anemi uban abinda ta Haifa abashi sai ind'aura mata Aure da Ashiru Almajirina ko kuma ta zab'i barmin gida tashiga duniya ta nemi wasu dangin ta zauna gunsu tayi duk watsewar da zatayi acan ko Yaya kuka gani?

kowa yai shiru a d'akin ita Aisha zcyrta ke bugawa kamar ta tarwatse yama za,ai ta Auri wani Almajiri kuma ma Ashiru datasan k'azantarsa tab walh bazata iyaba

Shiko Yaya baffa tausayi tabashi dukda yanajin haushin abinda takeyi agidan shiya fara magana yace" Amma mallam yakamata arangwanta mata akan Auren Ashiru Dan Allah ina tayata Neman Alfarma domin mutane zasu iya farga suso jin dalilin hakan,Dan haka ina ganin kamata yayi ace shi Wanda yai mata cikin za,a nemo inta haihun aimusu Auren kokuwa ya kuka gani?

Yafad'a yana kallon su Mukhtar

Yaya suraj da zcyrsa ta d'au zafi ya harxuk'o yakalleta yace"ke Dan ubanki wane d'an iskanne yai miki cikin ko waye saimun dank'oshi dole ya Aureki inkuma ba hakaba inyak'i saiki hkr ki Auri ashirin.

Kan Aisha a kife akan cinyarta tana kuka batace k'alaba

K'afa Yaya suraj ya Kawo zai maka mata Kawu yai saurin dakatarshi"barta suraj kada kai mata lahani azo ayi biyu babu bari tafad'a a hankali

Yakalleta yace"Aisha kifadi ko waye za,a nemoshi anitse zamu bishi da lallami ko yak'i Auren naki zan bashi makudan kud'i sbd baki dace da Almajiriba...."walh Kawu yace saidai in zubda cikin za,ayi shine zai Aureni sbd iyayansa manyan mutane ne yace bayaso suji balle kuma nahaihu akai ms d'an baxai yardaba....

"Walh baza,a zubar da cikinba dole ki haihu akai masa d'ansa Dan uwarshi wato mu namu asirin yatonu knn," cewar Yaya Mukhtar

Mallam yace"kudakata Ni bance atsaya jayayyaba tunda har sai an zubarda ciki zai Aureki karya yake yi baxan d'auki zunubin zubda ciki agidanaba yaxo daga baya ma ya gujeki kokuma ki rasa ranki gun zubda cikin gara kawai ayi abinda nace tun farko Ashiru yanada nutsuwa aduk Almajiraina yafisu hankali da kwazon nema Na dad'e da yayeshi saidai ma yakoyar da wasu kuma yana zuwa yayi dako akasuwa danhaka zab'in Dana bakima nakansile dolene Aure da Ashiru kokuma kicanxa uba.

Ta dad'a fashewa da kuka Aminatu tana gefe tsuru batada ta cewa don mallam yagama magana haka iyayanta mata sunyi shiru agefe su aganinsuma mallam daidai yayi

Kawu yakalli Aisha yace"Aisha kiyi shiru ki karb'i zab'in mallam insha Allahu zan tsaya miki akan zamanku da Ashiru zansai gida kuzauna ciki har sai Allah yabashi nashi zan bashi jari metsoka yayi sana,a kema kuma zantsaya kiyi karatu agidansa sannan motarki zata dawo hannunki haka yayi miki?

Ta d'ago kai takura masa ido tana k'issima wani Abu aranta harsaida yaji fad'uwar gaba yakanne yace"toya kk gani ko hakan baiyi mikiba?

Ta girgixa kanta tace"yayi Na amince Kawu

Tana gama fad'in haka ta mik'e ta fuce da kukanta

Mallam yace"to magana ta k'are Dan haka kai Mukhtar xaka kaita k'auye da kanka saika mikata ahannunsu zaka taho

Kawu yace"ba saiya kaitaba ma nahutacceshi nizankaita dakaina

Anan taro ya watse kowa yafuce aka bar Kawu da mallam suna tattaunawa mallam yadubi Kawu yace"inaso dama muzauna tuntuni akan zancen zamanka haka ba Aure banajin dad'i walh kamanyanta ga arxik'i kana samu ba mutuncinki bane zama kai d'aya a katon gida ba mace gara kanemo mace ka Aura ko cikin "yan uwane ko kuwa?

Kawu ya gyara zama yace" insha Allahu kafin musauka zanyi Aure yanxuma akwai k'anwar abokina da mijinta ya rasu takaba take yine munyi magana dashi inta gama takabar zanyi maganar Aurenta

Mallam yayi murmushi"to harnaji dad'i Allah yataimaka

Da Kawu zaitafi dubu hamsin yabaiwa mallam sbd hidimar saukar Aminatu samarin maxan kuma yabisu da dubu ashirin ashirin su inna kuma dubu goma goma yabaiwa su Aminatu biyar biyar

Dama haka yake musu kokowada tasa kyautar inyazo samarin kuwa duk wata yake tura musu da kud'i ta account

Aisha abin duniya yai mata yawa bata iya bacci ba aranar har cikin dare tanata tunanin mafita domin harga Allah baxata iya Auren Ashiruba gashi mummuna gashi Almajiri lallai k'awayenta zasui mata dariya itada take da Auren saurayi mekyau metashen kud'i kamar Adam saikuma suji ta b'ige da Auren k'olo tab A'i walh dole tabi abinda Adam yagaya mata nata zubda cikin tabiyoshi sugudu kano suzauna yanada gida acan
Chapter 9 · 0% Book details