← Book details Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yafada yana fara,a itako gabantane yabada dum! Badai fateemah Lurwan d'in datake jinta aranta tana ganin itace "yarta teemahn ba?

Takalli deen tace" wacce ce Teemah aciki,badai Fatima Lurwan ba?

Ya d'aga kansa yana fad'in "itace Umma itama tafara karb'ar kyautarta itace kuma tafara bud'e taro da addu,a kuma itace wacce ta rufe taro da addu,ar gatacan amota ma muje kiganta,yana gama fad'ar haka yai gaba zuwa gun motar gabanta yaci gaba da faduwa

Su hassan suna zuba kyautukan da Teemah tasamu a ckn but suka gaidata har k'asa deen yace" Umma gasu hassan da Hussain fa'

Hjy Salma tace"lallai su hassan kungirma nasan kunmanta ko? kunyi Aure ne?

Dukansu sukai murmushi deen yacafe da cewa"ba Wanda yai Aure suna dai nema gwaurayene kamarni anan "

Hjy maryam tafito taxo suka gaisa tace"Hjy Salma kincika alqawari kinxo munji dad'i sosai harda kyaututtuka Allah yakara budi,

Hjy Salma tace"amin,yau naga teemah surukata ina alfahari da ita naji dad'i anata yabon kwaxonta agurin deen yacemin itace Fatima Lurwan data rufe taro da addu,a,"

Momy tayi murmushi taji dad'i har ranta nayabon Teemah da akayi tace"kwarai itace yau Allah Yy kunga muna bari inkirata kugaisa ,

Ta leka ckn motar dasu teemahn suke tagaya mata taxo sugaisa da Umman deen Akunyace tafuto tai mamakin ganin wannan kyakykyawar matar data raba musu atamfofi lallai Ashe akwai danganta Knn,Ashe surukar tace toko taganeta ko deen ya tab'a nuna mata hoton ta shiyasa taringa mata murmushi? Da walakin dai....sun gaisa da Umman takoma ckn mota da sauri tanajin nauyinta su feenah da nabeehat ma suka fito suma suka gaidata Hjy Salma taleka motarsa Alh Lurwan suka gaisa Hjy Lubna takama baki tace"a,a lallai Hjy Salma rai kanga rai Ashe zamu had'u? Hjy Salma da fara,arta tace"gashi Allah yakawo dalilin haduwar, kinyadani kota waya bama gaisawa wato saidai kuyi zumuncinku da Hjy maryam sbd deen yana gunta?

Murmushi Hjy Salma tayi tace"ba haka bane sha,anin aikine yake boyeni itama hjy maryam din mundade sosai bamu haduba tun atsohon gidanta kema yanxu ai tunda Allah yahadamu saimu karb'i nambar juna ko Allah zaisa wataran naje muku ,

Hjy Lubna tace "toshikenan ba matsala ,wane Aiki kikeyine?

Hjy Salma tace" Lauya ce ni yanxuma tare mukaxo da ma,aikatan mu don shugaban makarantar nan d'anuwan alqalin mune shimuka zowa kara,
" kunyi anko da d'anki Hussain shima a kotu yake Aiki saidai shi bai dad'e dafarawaba"

Hjy maryam takalli Hjy salma tace"to Amma zamuje gidan dake ko tfy zakiyi?"

Hjy Salma tace"zanje mana inaso ingano gidan domin akwai wata magana danake muyi dake "

Hjy maryam tace"toshikenan biyomu muje"

Hjy Salma tana binsu abaya ckn motarta har sukaje gidan megadin yabud'e musu sukai parking a can parking space suka fito suka shiga ciki da jama,a agidan sbd za,ayi kwarya²r walima agidan

A sitting room suka zazzauna hajy maryam da Hjy Lubna sai Hjy salman sai dady da Alh mansur dadyn su hassan

Hjy maryam tace"bari nasa akawo mk kayan motsa baki"

Hjy Salma tace"kafin nan Dan Allah kitaho da Teemah domin ta naxo akanta nakeso muyi maganar"

Hjy maryam tace"to! Ikon Allah! bari naturota

Momy ad'aki ta tarar da Teemah tana latse latsen waya jikinta duk asanyaye yau ranar farin cikin tane Amma kuma gabanta yanata faduwa batasan daliliba sai addua taringayi azcyrta

Hjy maryam tasanar mata kiran da Hjy salman ke mata nan gabanta ya k'ara faduwa Allah dai yasa lfy tanajin nauyin surukar nan tata Amma ita taga wayayyi yace bata jin komai

Dasallama tashiga suka amsa mata tasami guri ak'asa tazauna kanta ak'asa itako Hjy Salma murmushi kawai take tana kallonta tana addu,ar Allah yasa zatonta yazama gaskiya

Hjy maryam tashigo tazauna tana fad'in"to Hjy Salma ga teemahn wace magana ce zakiyi?

Dady yace"toko mufuta mubaku guri kwafi sakewa?

Hjy Salma tayi saurin girgixa kanta tace"a,a Alh basai kunfita ba maganar me muhimmancice kuma yakamata ace kuna gurin"

Hjy maryam tace"to Allah yasa ta Alkairice"

Hjy lubna tace"Amin"

Hjy Salma tagyara zamanta tace"to dafarko Alh Kaine namiji watakila zakafi fahimta ta akan zancen danaxo muku dashi ina fatan zakuyimin kyakykyawar fahimta akai Dan Allah kugarceni domin zcyta ce takemin shakku akan Teemah domin ina ganin kamar itace "yata data b'ace shekara 20 da suka wuce tun tana tsumma,

Hjy maryam tayi saurin mik'ewa tsaye takalli Hjy Salma kallo Na rashin fahimta tace"wannan wane banxan zancen mekike nufi?

Hjy Salma tace" Dan Allah kizauna magana ce zamuyi ta fahimtar juna kitaimaka kigaya min shin awane asibitin kk haifi yrki Teemah dakuma wace rana...?

"Dakata Hjy Salma banason tambayar rainin hankali ke a asibiti kk rasa Yr taki koya? Kuma keya kamata naiwa wannan tambayar bawai nizakiyiwa ba

Sannan alokacin Dana haifi Teemah su biyu sukaxo duniya mijina shedane yana ckn asibitin nahaihu haka duniya ma shaidace kodon kinga basuyi kamaba,sannan alokacin Dana haihu nabuga wayarki nagaya mk haihuwar saikikace baxaki sami damar zuwar minba don kema kinhaihu Amma " yar taxo barai ko bamui hakaba? Tafada tana tsatstsare Hjy Salma da ido ammafa gabanta ba abinda yake sai faduwa tabbas bata fatan abinda Hjy salma taxo dashi yatabbata domin tana qaunar Teemah baxata iya rabuwa da itaba

Hjy Salma hawaye yazubo mata takalli Teemah data zubo musu ido cknta ya d'uri ruwa yaume takeji?

Alhaji Lurwan shima ya firgita da wannan batu Na Hjy Salma Alh mansur yakalli Hjy salma yace"toke awane dalilin kk yarda d'an mutum sukutun ko sace miki ita akai?

Girgizakai Hjy Salma tayi tana goge hawaye idonta yakada yai ja tace"walh har kullum ina nadamar biyewa zcy danayi akan inbi ra,ayin mijina dukda alokacin akwai yarinta... Hjy Lubna tace"kina nufin da kk haihu sai mijinki yace kiyar bayaso?

Dady yakatsesu"kudakata kada mu tsaya wani tambaye² Hjy Salma bamu labarin duk abinda yafaru dake abaya da dalilin ki nacewa Teemah "yarkice.....

_muje zuwa_...

~*Auntyn Sayyada da Shahida*~💘
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

~*Pg 25-26*~

Hjy Salma tagyara zama takallesu d'aya bayan d'aya sannan ta fara basu labarin kamar haka:-

××××× ××××× ×××××
Alokacin Dana Auri mijina kamal akwai soyayya me k'arfi atsakaninmu Wanda atun farko kafin Na Auri mahaifin deen shinaso Na Aura Allah baiyiba Na Auri kamal yana sona ina sonsa saidai son da nake masa yaxarta nasa ina masa tsananin biyayya ina shakkarsa

Kamal d'an gayune d'an boko aturai yai karatunsa dan hakanema yakwaso wasu daga ckn d'abiunsu Na rashin son haihuwa da wuri kokuma rashin son Tara "Yaya dasukeyi

Tun kafin muyi Aure dashi mukai yanunamin cewar inhar mukai Aure bayaso nahaihu da wuri at less yanaso Nafi shekara goma kuma kozan haihun kada muwuce " Yaya 2 ko 3

Ba musu ba jayayya Na amince masa

Haka ko akai Dan da mukai Aure kamal maganin FML planning yaringa kawomin inasha bana munafurtarsa tsakanina da Allah nakesha har Na shekara uku bandamuba saboda nima alokacin karatu nake Na low

Alokacin Dana tafi digree Na Na biyu saina canxa planning nadawo yin allura ita kuma shekara biyu nayita Amma saita ramar Ni tasa nake yawan bleeding saina masa complain saiyakaini asibiti aka canza wani tsarin akasamin inplan a hannu Na shekara uku

Alokacin Dana gama karatuna kafin nasami Aiki ina zaune agida nid'aya kwal sai nake kewar yara naita sha,awar ace nima Na haihu ga shekaruna suna tafiya hatta Yaya mus,ab yayana da mukai Aure kusan tare yaransa uku maza biyu da mace d'aya

Yayar mijina tasha zuwa tasani agaba taringa min tambayoyin ko dai planning nake nakance mata a,a Allah nedai bai kawoba takance inma planning d'in nake sbd karatu nake boye mata to yanzu aina gama gaskiya intaji shirun yaiyawa zamuje asibiti dukanmu aduba mu tanaso taga jinin kaninta danshi d'aya kwal gareta

Natsorata da kalamanta nasameshi da zancen nace gara tun wuri muhakura kawai kada aganomu kotasa yai Aure

Kamal yanuna b'acin ransa akan wannan yr magana tawa waishi in haihuwa nakeso tomu rabu naje nahaihu da wani mana in "yayane ba inada d'a ba meye Na damuwa kuma batun Aure baiga Wanda zaisashi ya k'ara ba danvayada ra ayin k'arawa

Naso Na hakura nabi tsarinsa Amma saina kasa daurewa naje aka ciremin in plan

Aiko nacireshi da wata uku nasami ciki

Tabbas Dana gano inada cikin sai hankalina yakwanta Amma awani b'angaren Na zcyta tana fargabar hln da zamu k'are da kamal

Aiko dai Bai fargaba saida ciki ya fito

Cikin yashiga wata takwas yadawo daga wata tafiya Dan wata uku yai acan wani cos ne da aka k'ara masa girma daya dawo

Yasha mamaki daya ganni da cikin yatambayeni meyake gani nace cikine Allah yabani Dan in haihu

Yatambayeni da ixinin wa nadaina planning d'in?

Cikin dakiya nace" da yardar Allah da ixininsa"

Yakufula yace"aiko ko a zubarshi ko inje innema masa uba murabu kwata²

Naringa kuka koyaji tausaina Amma kamar Wanda aka yiwa asiri akan k'in "Yaya ya dake yama daina nunan kulawarsa akaina yaraba d'aki dani kallo ban isheshiba Aiki ma danake nema yahana yace ba agidansaba

Niko inaso inyi Aiki nasameshi da zancen meyakeso daga gareni Wanda innayi zan faranta masa ?

Saiyace " zubda ciki"

Nace dashi"Ai ciki baxai xububa Dan yashiga watan haihuwarsa in akace za,a cireshi saidai arasamu gabaki d'aya

Kamal yanuna shifa yananan akan bakansa saidai ko inna Amince inhar Na haihu to insan yarda zanyi da abinda nahaifa ko inya ko inkai gdn marayu

Walh har raina Na amince sbd son kwanciyar hankalinsa da shairrin shaid'an

Aiko ganin Na amince da abinda yatsara tuni ya yarjemin nayi Aiki Dan dakansama yafara nemarmin.....

~*Auntyn Sayyada da Shahida*~💘
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_ 👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

~*Pg 27-28*~

Ganin Na Amincewa kamal cewar idan nahaihu zan rabu da abinda Na Haifa d'in nazauna dashi nacigaba da planning din sai kamal yasake dani ba kmr da ba daya juyan baya saiya dawo sakarmin fuska

Munyi abinmu a sirrince duk da bana tona asirin mijina balle wannan danasan babban abune Dan haka saina boyeshi ckn raina saidai abin yana nuk'urkusata nabi duk Na rame sai k'aton ciki ajikina sai k'ashin wuya dasuka fitomin akwai jindadi dai atattare dani tunda ackn arxik'i nake nagodewa Allah
Chapter 11 · 0% Book details