Sashe 1
Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[5/21, 13:03] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘
*Bissimillahir Rahmanir Rahim....*
_Dasunan Allah mai Rahama mai jink'ai nake farawa_
_Ina mik'a d'umbin godiyata ga d'aukacin masoyana Na yanda suka nunan soyayyarsu gareni akan novel d'in_ *ZAMAN MARINA* _naji dad'i sosai har ckn raina Allah yasa wannan ma yasamu karb'uwa agareku ya fad'akar daku ya nishad'antar daku_
_haka wannan littafin shima k'irkirarsa nayi bawai satar fasahaba inwata taga yai kama da labarinta to arashine_
~pg 1....~
Da safiyar Allah ta,ala kukan jaririyar yakad'e bayan asibitin Na Khadija clinic a gindin wata bishiyar mangwaro wata matashir mace ce azaune da jariri a nad'e ahannunta tana jijjigata tana goge hawayen idonta akwai damuwa atattare da ita
Ta dire jaririyar ak'asa tana kuka takawo Yr envelop ta ajiye ajikinta ta mik'e tsaye tana share hawaye tana kallonta ta juya zata tafi dasauri tajuyo tak'ara kallon jaririyar ta bud'eta tashafi fuskarta tace"ko yafeni babyna balaifina bane walh inasonki har raina mahaifinkine baya k'aunarki keba shegiya bace "yar sunnah ce da gatanki gaba da baya,babu yanda zanyi " yata dole ce,oh! Ni Salma waiyau nice zan yarda "yata ta cikina sbd infarantawa mijina rai ya Allah kana kallona biyayya zanyi sbd inason Aurena Allah ka karemin " yata kasakata ahannu nagari,kiyafeni babyna zantafi nabarki sai wata rana.
Tana gama fad'in haka tai saurin juyawa tana kuka ahankali jaririyar ta callara wani mugun kuka tamkar anmintsineta a take mahaifiyarta ta rintse ido tai saurin waigowa tai mata kallon k'arshe tajuya dasauri tai gaba tabar "yar Na kuka ackn tsumma.
*shin wacece Salma?*
***********************
Salma nitsattsiyar yarinya ce me matuk'ar biyayya ga iyayanta Wanda suka tashi a ckn k'uncin talauci d'akyar tagama secondry d'in gwamnati yayanta mus,ab shima yana matakin k'arshe Na Jami,a mahaifinta malam Musa sana,arsa shine kasa kayan miya ak'ofar gida kayan gwari yake saidawa akan tebur a " yar rumfarsa yake kafa bencin yaxauna agefe guda,Allah yakan saka masa nasibi domin da wannan sana,ar dayakeyi yake rufawa kansa asiri yake yiwa yaransa biyu da Allah yabashi hidimar yau da kullum duk da mus,ab yakanyo "yan buga buga a tasha ko dako a singa duk ranar da bashida lecture mahaifiyarsu inna halima tana saida gasara da safe harma takan soya wainar gero akanzo asiya
Salma yarinyace kyakkyawa ajin k'arshe batada rawar kai ko kadan danko k'awaye basu dametaba balle Tara samari harta gama makaranta saurayinta d'aya Wanda takeso yake sonta wato kamal d'an kwalisa Wanda yake matukar sonta saidai shidin karatu yake marayane Amma yayarsa datake Auran me kud'i ta tsaya masa akan harkan karatunsa
Alokacin da Salma ta shekara dagama karatu sai babanta yace mata tafuto da miji Aure zai mata
Tasami kamal da batun sai kamal yace shikam yanxu Aure baya gabansa harsaiya gama karatu Yakama aiki yafison yadogara dakansa intaga zata jirashi to inko baxata jirashiba to intasami miji tayi Aure shikam bayanxuba
Tun dagananma saiya d'auke k'afarsa da zuwa gunta har Allah yakawo ranar Tashin su daga gidan domin dama haya sukeyi Allah kuma yataimaka mallam Musa yasami Aikin gadi a gidan wani hamshak'in me kud'in gaske wato Alh Bashir tekun kud'i
A boysquater suka sami matsuguni inda nan Allah ya hutarsu domin baba Musa yadaina sana,ar gwari inna ta daina saida gasara da tuyar waina shikuma mus,ab yadaina yin dako rayuwarsu tadaidaita adadalin yanda Alh bashir yake yi musu abin arxik'i domin salary metsoka yake biyan mahaifin Salma haka yana yawan kyautata musu duk adalilin son dayakewa "yar tahalikar Allah Salma Wanda bai tab'a nunawaba tana ganin girmansa tasha ganinsa sugaisa inta dawo daga islamiyya sukan had'u afarfajiyar gidan ko inya fito a mota zai futa takan durk'usa har k'asa tagaidashi
Yakan yaba da d'abiunta gashi tayi masa ta koina tanada tarbiya da girmama nagaba da ita,
Aranar da yai k'undun bala yagayawa malam Musa zancen yatsammaci baxai amince masaba Amma saiyaga sab'anin hakan domin murna ma yai da abin har yai masa albishir dacewa yabashi ita
Dayajewa inna da labarin itama taji dad'i sosai tasawa abin Albarka domin dama kullum addu,arta Allah yafito wa da " yarta miji nagari to sunyaba kuma da halayyar Alhajin yana da kyautatawa mutane gashi da tausayin talakawa da taimako yatara kud'i saidai magada
Alh bashir tekun kud'i shekararsa hamsin babban mutum ne baida uwa baida d'a ko "ya sai " yan uwansa guda biyu aduniya da suke ciki d'aya Alh mansur shine k'aninsa yana london da zama tareda iyalansa saikuma k'anwarsa mesuna Haj maryam wacce take Auran v.chairman itama kamarshi Allah bai t'aba bata haihuwaba tana R/zaki da zama.
Magana tai k'arfi tsakanin Alh da Salma domin itama tai amanna dashi batai ja da iyayantaba, yaya mus, ab shima abin yai masa dad'i domin yasan Hutu yaxo musu kwata kwata rashin haihuwar Alh bata damesuba har Akai Auran agidansa dake Zoo road ta tare wannan kuma yabarwa iyayanta
Matar dasuke tare da Alh alokacin dama yagaji da zama da ita sbd yasha kamata da laifuka yana hkr da ita domin yasan ba Dan Allah take zaune dashiba sbd kudinsa ne dama irin yn duniyar nan ne tanada shekaru babbace. Har yawon siyasa take dama a haka ya Aureta ansha Kawo masa tsegumin tana bin maza yn duniya tana shek'e ayarta aboye baitab'a yarda saida yagani da idonsa yakamata da tsohon megadin gidansa k'iri kiri a ckn gidansa awannan dalili yasa yakoreta tareda takardar sakinta sannan yakori megadin nasa yasa anemo masa wani wannan shine dalilin dayasa Aka nemo masa mallam Musa ashe rabon Allah zaisa ya Auri "yarsa ne......
~Auntyn sayyada~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘
_Sak'on ta,aziyya gareki Aunty Nafee Anka_
_Na rashin "yar yayarta datayi ubangiji Allah ya jik'anta yasa mutuwa tazama Hutu agareta_
_Allah yakai Rahama kabarinki_ *Fauziyya Anka*
~*pg 2...*~
A watan da Salma ta tare agidan Alh bashir Allah yanuna k'udurarsa akanta tasami ciki
Huuu! Fad'ar irin farin cikin da Alh yakasance b'ata bakine mutane yaringa fadawa abokansa da " yan uwa suntayashi murna sosai k'anwar Alh hajiya maryam taringaji aranta itama nan gaba zata iya samu Dan haka bxata fitar da raiba itama,
Tabbas Salma taga soyayya ta miji sosai yake nuna mata yafi son cikin jikinta da komai dake ckn duniya yakance da Allah zai karb'i dukiyarsa yabarshi da d'ansa ko "yarsa dazata haifa ms su zauna ckn talauci shihakan zaifi masa domin rashin haihuwa akwai d'aci arai
Salma tasha kyautuka agunsa domin yabata filaye guda biyar tafka tafka kyauta amatsayin gudunmawa motar kuwa da take hawa tazarce tasa yayantama hadaddiya aka bashi ayanxu mus,ab kam bashida matsala afannin rayuwa harkar karatunsa komai yana tfy normal saidaima ya taimakawa abokansa.
Yabiyawa inna da mallam Musa kujerar zuwa hajji sukaje suka sauke farali itako ance saita haihu
Da cikin yai kwari ya isa haihuwa saiyace ba,a Nigeria zata haihuwa gara yafuta da ita k'asar waje tahaihu acan kulawar da zasu bata yafi Na nan.
London yakaita gidan wansa Alh mansur yabarta acan yadawo gida saita haihu zaikoma,matar Alh mansur Aunty Lubna mekirki tanunawa Salma qauna itake kaita awo duk alokacin zuwa inyaxo,Alokacin ita yaranta biyu twins maxa farare kyawawa ita " yar meduguri ce acan ya Aurota yakaita k'asar London d'in don acan yake Aiki babban likitane shikuma tunda Allah yabashi haihuwa a farkon Auransu Na yn biyu basu sake samuba
Alhamdulillah Allah ya sauketa lfy ta haifi d'anta sankacece k'ato fari tas tamkar d'an bature Alh murna tamkar yai tsintsu yaganshi acan aranar da aka gaya masa sai aranar yabi jirgi domin zuwa ganin magajinsa d'an baiwa.
Kamar ya lasheshi yaringaji yayi masa hotuna sosai basu baro k'asarba saida tayi sati biyu likitoci suna bata magungunan k'arin lfy tasha wuya wajen haihuwarsa tubar kalla k'atone Allah yasotama da ba aiki akai mataba tayi k'okari suma sunyaba mata tayi juriya sosae
Taron suna akayi sosai dasuka dawo gd Nigeria yakashe kud'i tamkar baisan amfaninsuba Hjy maryam taringa jin d'an tamkar subatashi k'aunar haihuwa take sosai itama ga d'an da shiga rai jama,a kowa sai yabon kyansa suke saida mallam yasa akai masa rubutun baki aka ringa bashi yanasha bayan suna.
Komai Na Alh sunan d'ansa yake sakawa *Saifuddeen*
Tundaga sunayen kamfanoninsa da sunayen gidajen mansa komai nasa saifudden, kaunar dayake yw deen sai Allah yaron Allah yabashi farin jini gashi yataso da wani irin farin jini kowa sonsa yake yayo kama da Alh sosai yanada jiki,d'an kubul kub'ul dashi ga kuzari da Allah yabashi shekara d'aya yana gudunsa ko ina
Yaya mus, ab yana kaunar saif yakan yawaita zw gidan k'anwar tasa sbd saif
Allahu Akbar!rabon d'a rabon agana dai Alh kwanansa yakare aduniya ciwon ciki kawai ya turnik'eshi aranar da saif yacika shekara biyu anata bajet d'in za,ai masa birthday asatin Ashe babu rabon ayidai
Salma tasha kuka domin Alh yatafi yabarta da soyayyarsa aranta ga tausayin saif da taringaji zaitaso maraya mutuwa tai mata shigar sauri Shikenan saidai avaiwa saif labarin mahaifinsa.
Mutane sunji mutuwar bawan Allahn nan mutum me tawakkali da hkr ga kyauta da iya mu,amula soyayyar sugar dady akwai tsayewa arai don yajiyar da ita dad'i
Aranar da akai sadakar bakwai hajy maryam tanemi abata deen yadawo gunta da zama Amma sai yayanta Alh mansur yahana yace tayi hkr kada tayiwa Salma fami dame zataji daga yin rasuwa ai insuka mata haka da gaggawa akwai kwara gara dai abari idan nan gaba ta tashi yin Aure saisu karb'eshi.
Dole tahakura badan taso hakanba tana qaunar deen bawai Dan mugunta ko son zcy tashirya hakanba
Allah ya sakawa Salma hkr da Dangana gameda rashin Alh aranta
Taci gaba da rainon d'anta agunta alokacin daya shekara uku tana zaune agida sai yayanta yabata shawarar akan ta koma karatu kawai shiyafi kafin Allah yakawo mata miji
Hakan kuwa akai tafara karatunta a Sa,Adatu rimi NCE abinta tana karantar mass communication
tana NCE2 Yaya mus,ab yafito da matar dazai Aura saudat akasaka ranar Aure a filayenta tabashi d'aya a d'an agundi dayake har account tabude masa nanta tayashi ginin gidan akayishi mekyau naburgewa,sannan tabiya musu kud'in kujerar makka ita dashi hajji.
Alokacin saif yana gurin inna sunyi sabo sosai tunda ita ba wuni take agidaba