← Book details Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 16

Sashe 7

Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin k'arfe takwas Na dare dady yana zaune afalonsa yana kallon tashar *CNN* Hjy maryam ta shigo da sallmarta bayanta teemah da feenah ne ya amsa musu sallamar suka durk'usa kusa gabansa suna masa barka da hutawa yakalli teemah yace"Uwata dama akan maganar saukar kine dazakuyi shiyasa na aika akiraki naji ko antsaida ranar sbd nasan irin shirye² daxanyi miki.

Teemah tace"k'arshen watan nan ne dady lahadin k'arshen watan anfito mana da ankon shadda purple sai kuma hijab da akace muyi pink colour hark'asa sai kud'in allon zayyana da kud'in walima akace mukai dubu dubu goma shabiyar saikuma abin sadaka da sukace mufadawa iyayanmu duk abinda kayi niyyar yi musu dady suna bukata

Dady yagyara xama tareda rage volume d'in TV yace"yayi kyau duk za,ayi miki abinda kk fad'a insha Allahu agobe ma zansiyo mk shaddar sbd kisamu kibada dinkinta da wuri sannan zansayi saniya nakai musu sadaka fisabilillah haka yayi? Yatambayeta

Tayi murmushi taji dad'i har ckn ranta tagyad'a kanta tace"yayi dady Allah yabiya Allah yasaka da Alkairi,

Itako feenah wani malolo ne yatsaye mata dama sbd teemah akai kiransu aka katse mata chart d'in datakeyi data sanima bataxoba takalli momynta taga itama fuskarta ba annuri

Dady yakalli Hjy maryam ckn fara,a yace"ke momy banji kinfad'i irin taki gudummawar da zakiyiwa "yartakiba Dan nasan tunda macece " yarfari zaki fini bajinta ko? Yafada yana tsattsareta da ido

Ta murmusa tace"sosaima kuwa domin zan d'auki nauyin duk wata cima da za,ayi ackn gidannan Dan dole nima Na shirya mata walima agida kuma akwai wata babbar kyauta Dana tanadar mata wacce bakowane zaijiba harsaina bata ahannunta,tafada tana dry

Shima dryr yayi yana fad'in "a,a toshikenan muma bazamu matsa dole sai munjiba ko feenah,yafada yana kallon feenah tayi murmushi kawai

Dady ya bud'e wata jaka kusa dashi yaciro bandir d'in kud'i yn Dari biyar² yafara mikawa teemah dubu ashirin ne yace" gashi wannan aje ayi siyayyar kayan kwalliya dannasan turare da hoda sunyi low,

Takarb'a tana godiya yamik'awa feenah ma yanda yabaiwa teemah itama takarba tana yin godiya fuskarta fal fara,a ranta yai k'al

Anan suka tashi suka barsu momy afalon suka koma d'akunansu

*********

Washe gari ahanyar zuwnta sch tana ckn motar Yaya deen yana tuk'i yanashan kid'an wakar celindion yana bin wakar itakuma tajingina kanta ajikinta kujera tayi shiru sbd ita music bai dametaba yarage volemu yakalleta yace"ya akaine my teemah?

Tace masa"bakomai menene?

Yace"naga kinyi shiru kina tunani "
Tagirgiza kanta tace"batunani nakeba "

Yace"OK yau saura kwana nawa saukar taku?

Tace "k'arshen watane"

Yace "OK to yakamata fa inkaiki ki gaida Ummana before tym d'in domin tayimin waya lokacin muna London ta taho gidanmu donsu gaisa da momy sundade basu haduba tace nataho nasata ahanyar gidan shine nace mata bama gari donhaka kishirya nakaiki kigaisheta dantasan da zancenki nafison kafin tazo gidan kifara kaimata gaisuwarki kokuwa?

Yafada yana murmushi yana d'aga mata gira

Tayi murmushi tace" yanxu har zancen soyayyar mu yakai kunnenta Dan Allah bakaji kunyar fad'a mataba haba kana Dan fari"

Yayi murmushi yace"Dan fari kuma d'aya tilo ba,tunda banda wa ko k'ani don agidan Mijin natama har yanxu bata haihu dashiba,

Teemah tace"kai aini naxaci kamar momy tace tataba yi mata waya cewar ta haihu d'anba rai,

Yace'to aiku mata inkuna aiki bason Tara yara kukeba maybe itama tana bin wannan tsarin ne

Tace"kada kai mata wannan zargin may be Allah ne baikawo matanba,

Yace "yanxu ke Dan ina d'an fari sai Inji kunyar fadawa Uwata nasami wacce nakeso zan Aura tab,to duk irin son da nake miki saida nazayyane mata

Teemah takama baki tace" wuuu! Lallai aikodai kunyar ta nakeji anya zan iya zuwa kuwa?

Yace"dolema kuwa danhaka a week End dinnanma zamuje asabar ko lahadi tunda bana xw aiki kekuma ba sch saiki shirya dab zuwanki wajib ne

Tace"to Allah yakaimu"
Yace"amin,

*___________________*

Da daddare teemah nakwance ad'akinta kan k'aton gadonta dayasha luntsumemiyar katifarta metaushi saijuyi take ckn jin dad'i tana chart da Yy deen da kuma Yr uwa Rabin jiki Nabeehat sai zuba murmushi take daganinta ackn nishad'i take momy tayi sallama tashigo d'akin nata

Dasauri Teemah ta ajiye wayar gefe tareda Amsa sallamar momyn

Hjy maryam tace"Teemah Yr gatan dady ga shaddarki nan harya Kawo miki gexna ce ta dubunnan kudad'e yace kikai d'inki ayi miki kona dubu nawane dadynki dai yanaso kifita daban ckn "yan sauka

Teemah takarb'i shaddar tana murmushi tace" kai Amma tayi kyau momy naji dad'i kitayani yin godiya ga dady Amma fa ya iya zab'e kamar tare kukaje

Hjy maryam tace"to nima gatawa gudunmawar"

Tamik'awa teemah zoben gwal Dana azurfa (tun Wanda suka tsinci teeman dashi ne)

Teemah ckn jin dad'i takarba tasaka atsanta tana murna sunyi mata cif,

"Kai momy naji dad'i nagode Allah yakara bud'i"

Hjy maryam tayi murmushi tace"to amin,yayanku deen yacemin ranar Asabar zaikaiki gidan Hjy Salma tonace masa harda feenah zakuje itama taje ta gaisheta tunda babu Wanda tasani cknku

Teemah tace "to momy Allah yakaimu"

"Amin, tace tareda futa daga d'akin tabar teemah tanata juya hannunta tana kallon zoben bawai Na gwal d'in ne yad'au hankalintaba Na zurfar ne Dan nagwal tanadashi Momyn ta tab'a sai musu itada feenah Amma baikai wannan tsadar da girma tun suna secondry

Ajikin axurfar ansaka harafin *SK* wannan sunan ne yad'auki hankalinta domin batasan me hakan ke nufiba sbd tasan dai farkon sunan iyayanta babu wannan harafin haka natama

Tarasa gane me wannan harafin kenufi dole tahakura tabar tunanin Neman ba,asin sanin sunan domin batada Wanda zata Tambaya don ita batada yawan tambaye² don magana ma ba damunta tayiba.....

~*Auntyn Sayyada da Shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_ 👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

~*Pg 11-12*~

Aranar Asabar kamar yadda aka tsara tfy gidan Hjy Salma wajen 11:am suka gama shirinsu

Kamar had'in baki teemah shadda tasaka ruwan Zuma haka shima deen shaddarsa ruwan zuman ce saidai tasa light ce tata kuma dark colour ce, doguwar rigace shaf d'in rigar yakamata sosai yafito da cake din breast d'inta cif,Aikin rigar har k'asa aka kawo shi kalar ruwan madara gyalen datasaka ma ruwan madarar ne flat shoe ne ak"'afarta donbata saka me tsini d'an kunnen tama Yr barimace me stone din farar danja

Kwalliyar datayi simple ce bata tsaya k'ak'ale² ba Dan farar hoda tasakama sai weat lips batayi jagiraba domin gashin girarta bak'ine sid'ik cikakke saidai ta tajeshi ya kwanta luf kanfatar yai kyau,

Tayi kyau sosai dukda batayi make up sosaiba domin tana ganin zata gun suruka bai kamata tacika fuskarta da kwalliyaba kartaga tafiye gwalli donbashine da itanba

Turare kala 2 tafesa da _you and me_ da kuma _one Luv_ turarenta kenan ko yaushe sunada matukar k'amshi mesanyin gaske

Itako feenah fuskarnan kamar za,a saketa sai shek'i take anci pondetion dasu eye-shadow da eye liner da jagirarnan da ake yayi janbakin nan anrabaja shi bajau fakistan tasaka sky blue da kwalliyar stone agaban rigar

Riga da wandone rigar har guiwa take me shape a saman k'irji da d'an gyalen rigar ta ratayashi a kafad'a hancinta ta manna barima kamar a indiya dama itama ga hanci dogo kamar biro balaifi tayi kyau sosai Amma bata kai Teemah ba

Teemah tafuto falon ta tarar da feenah zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tasaka ear peace akunnenta tanashan kid'a tanata latse² awayr takalli teemah kallo 1 tad'auke kanta

Itako teemah murmushi tayi tazauna ahannun kujerar da feenar take tace" _wow my sister ur dress is fine_

Bata kalletaba tace atak'aice _tank u_

Teemah tace mata "Yaya fa kobai gama shirin nasaba?

Still dai bata kalle tanba ckn rashin kulawar tace mata " kije kigano"

Teemah tace"basainaje ba bari natab'o shi awaya
Tai dialin d'in wayrsa bugu d'aya yad'aga "kungama shirin nakune?

Tace " eh kana d'akine?

"A,a gani a wajen motata iliya yana wankemin ita kufito yama gama muwuce kawai"

Tace"to"
Tana kace wayar takalli feenah tace"yana waje yace mufito mutafi'

Momyce tafuto da wasanta tace"ymmatan momy kunyi kyaufa"

Dukansu suka dara Hjy maryam tace"inkuje kugaisarmin da ita kuce ina nan tafe nima nan gaba zansa deen yakaini mugaisa tunda ita tayardani"

Suka mike suna fad'in to zataji" suka fita

A cikin mota zcyr feenah tamkar tafashe Dan haushi da tuk'ik'in kishi naganin irin ankon da Yaya deen da teemah sukai gani tayima kamar da gayya sukayi dantaji haushi taji inama bata amsawa momy cewar zata bisunba dabataga wannan takaicinba

Suna gaban mota sunata hirarsu ta masoya deen yanata yaba kwalliyar da teeman tayi

Itako feenah tana gdn baya tasan duk Dan taji haushi Yy deen ke mata hakan tunda yasan har yanxun tana sonsa takasa cireshi aranta dukda Hussain ya nace kullum yana koro mata kalaman soyayya da k'ok'on bararsa ta waya yanxuma dashi suke chart yana gaya mata yakusa zuwa Nigeria sbd ita

Yy deen ya waigo takalleta ckn zolaya yace"yadai "yar k'anwat yana jiki shiru ko ciwon hak'ori kk?

Ta watsa masa wani kallo tace" mekakeso nace bawani ciwon hako'ri danake hankalina yana nan ina chart da masoyinta Hussain yana online "

Deen yace"ah! Lallai abin naku yayi nisa Knn aimu haka muke so gara da kuka k'ulle kinga in antashi biki sai ahad'a danamu ko my queen teemah? Ya fad'a yana kallon teemah da taketa zuba murmushi

Itako feenah banxa tayi dashi domin k'ara k'ularta Yy

A k'ofar gidan Hjy Salma ya faka motar babban gidane mekyau yamatsa hon megadin yabud'e Yalek'o da kansa ganin deen ne yasa yataho da saurinsa suka gaisa yace"saidai hajiyar batanan yanxun nan tafuta"

Deen yace"tafuta kuma? Tafa San da zuwanmu toya akai haka bata kiraniba"

Bala megadin yace"eh to gaskiya naga kamar saurima take da alama ko futar ta gaggawa ce ko gun Aikin aka nemeta,

Deen yace"OK bari nakirata" yaciro wayarsa yakira umman tasa saida yai mata 2missed call bata d'agaba can kuma yn sakanni saiga kiranta yashigo yad'aga suka gaisa tace"Saif harkunxo?

Deen yace"gamu a bakin gate ma baba me gadi yace kin fita yanxu"

Tace"eh walh futar dole ce wani case aka turo daga Abuja babban case ne ahannuna aka dank'ashi shine akaimin waya naxo yanxu akansa za,a zauna kabaiwa surukar tawa hkr kada natsaida Ku Dan banajin zamu tashi da wuri sai wjn yamma zanxo gidan naku nima

Yace"kada ki zamu Umma munyi miki uziri bari nakaisu gidansu inna sugaisa momy ma tace zataxo madawo latter kawai
Chapter 7 · 0% Book details