← Book details Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 16

Sashe 13

Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dad'e kansa akife akan cinya tunani ya cika masa kwakwalwa saida yayi hawaye itama Teeman hawaye take futarwa

Su hassan da Hussain da Nabeehat da feenah sun tausaya musu,bayama Teemah da saida tayi kuka hawaye kashinb'ar akuncinta kenan zasu rabu da "yar,uwarta Teemah duk saitaji ranta ba dad'i Ashe ba cikin su d'ayaba?

Dady yace" yanxu abinda yakamata tashi zamuyi mutafi gidan ki Hjy Salma domin muyi
Surprise d'in Mijin ki muyi bayanin komai agabansa koba hakaba ?

Alh mansur yace"wannan haka yake"

Dukansu suka mik'e domin tafiya gidan Hjy Salma.....

~*Auntyn Sayyada da Shahida*~💘
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_ 👉🏼 *Nabilancy Luv* ©💘

*KADUNA...*

~*Pg 31-32*~

A B'angaren Aisha kuwa abin duniya yayi mata yawa ita kanta ba qaunar cikin dake jikinta takeba gashi yajanyo mata tsana gun "yan gidansu hatta Aminatu da tafi kula da ita yanxu bata fiye kulataba saitaga dama take mata magana

Abin yadameta ainun ga Adam da kullum yake damunta da zancen ta gudo gunsa sugudu kano suyi kyakykyawar Rayuwarsu a acan babu takura babu kyara balle suyi Abu a d'ari-d'ari

Sharrin shaid'an da kuma sharrin zcy suka rinjayeta ta amince masa ta ringa shirinta a b'oye tak'udura aranta inhar tabar gidan nan tabarshi Knn(kunji wauta da shashanci ko? Hhhmmm duniya budurwar wawa...)

Ranar Laraba aka tsaida yin saukarsu Aminatu a islamiyyarsu anata shirye ²n walima gidan yasami bak'i Na " yan uwa ana gobe saukar talata Knn Allah ya arawa Aisha dama tazille tabar gidan babu Wanda ya farga

Aminatu ce tafara fahimtar Aisha bata ckn gidan domin har goman dare tajita shiru bata dawoba don azatonta tafuta taje gun Adam d'inne kamar yadda tasaba zuwa

Mubeena itace "yar yayar Inna halima taxo gidan zata kwana sbd ayi walimar da ita, a tudun wada take budurwa ce Sa,ar Aminatun ce suna kwance kan gado suna hira har bacci yakwashe mubeenar itako Aminatu hankalinta baya kwanciya harsai taga shigowar Auntyn ta

Har bacci yakwasheta Na mintina ta farka firgigit ta duba agogon bangon d'akin yanda ya buga k'arfe sha d'ayan dare haka k'irjinta ya buga lokaci guda domin Aisha bata wuce sha d'ayan bata shigo gidanba

Ta tashi tsam taje ta lek'o d'akin inna A'i ko can zata kwana aranar sbd takan kwana acan in innar ba itace da girkiba

Aminatu Na shiga taga innar ita kad'ai tana baccinta tashiga mamaki aranta to shin INA Aunty Aisha tashiga haka?

Ta juya zata futa Knn taji innar Na fad'in" ya akayi Ummie? Wani abun ne?

Dayake akwai hasken wutar lantarki Aminatu takalli innar tace"inna ba lfy ba walh hankali Na yak'i kwanciya domin Aunty Aisha bata ckn gidannan"

"Bata nan? To ina taje?

Aminatu tace " nikaina mamakin danake yi Knn nazacima kotana nan d'akin nema shiyasa naxo dubawa

Inna tace"to fa ai bacci baikama muba maxa muje intaso maxan gidan nan su baxama Neman ta"

Kai tsaye inna d'akinsu Yaya baffa ta nufa ta buga musu tana sallama duka nsu suna ciki,jin innar suce yasa suka fito a gaggauce suna tambayarta ko lfy?

Nan ta zayyane musu abinda ke wakana

Duk sunyi mamaki ainun abinda basu tab'a jiba.

Atsakar gida duk sukai cirko cirko inna halima da mallam ma sunfito kowa yana jimanta abin aransa Yaya suraj da Yaya Mukhtar "yan zafin rai sun k'ufula sunci burin sai sunyi maganinta inta dawo

Yaya baffa yana tsaye yai tagumi abin ya tsaye masa arai tabbas Aisha tanada matsala. Shikam yagodewa Allah daba masoyiyarsa ce me wannan halin ba.

Mallam ya janye tagumin dayai yace" Na fahimci Aisha so take tasaka min mugun ciwo araina to insha Allahu daga yau najanye hannuna akanta domin kuwa hanyar data d'auko ba hanya me kyau bace Sam muna mata tarbiyane tana rushewa taje can ta karata inma guduwa tayi baxan damuba A'i duniya ce'"yana gama fad'in haka ya juya yakoma d'akinsa

Inna halima ma barin gurin tayi batace k'ala ba dama domin batada tacewa dukda itama lamarin Na Aisha yana qona mata rai.

Inna A'i takallesu tace"maxa Ku koma Ku kwanta abinku abarwa safiya komai insha Allahu zata dawo daga duk inda ta tafi"

Dukansu suka koma d'akinsu itama Aminatu d'akin takoma tana jin ranta ba dad'i Allah yasa kada zarginta ya tabbata akan yayar tata

Mubeena me nauyin bacci batasan ma me ake cikiba sai baccinta take hankali kwance

Aminatu kasa bacci tayi tana kallon mubeena Na juyi agado ta ayyana inama itace wacce ayau batada damuwa domin tanajin gobe babbar ranace agunta Amma gashi yayarta tanaso tai mata tsaikon farin ciki.

Saida tayi sallar nafila k'arfe d'aya da Rabi Na dare tayi addu,o,inta kana takwanta ckn Sa,a baccin yadauk'eta

Da safe hankalinta ya tashi Dan daga sallar asuba bata komaba tanata "yan laziminta akan sallaya itama mubeenah tayi sallarta Amma ita takoma bacci danta saba komawa baccin bayan asubahi

Hankalin Aminatu yai mugun tashi data farga da akwatin Aisha baya kan saman sif d'insu tabbas zatonta ya zama gaskiya Aisha guduwa tayi

Lallai Aisha tayi girman banxa tabbas kowa yabar gida, gida yabarshi tasan zatayi nadama nan gaba Amma bataso tayi hakaba tana qaunar " yar uwarta Amma gashi tayi mata nisa batasan uwa duniyar data cillaba yanxu yazatayi Knn?

Koda mallam dasu inna suka ji cewar Aisha da kayanta ta tafi sai sukace tafi ruwa gudu ai duniya tafi bagaruwa iya jima,suka nuna kamar basu damuba ammafa can k'asan zcyr mallam wani abune ya tokare masa yak'i tafiya saida ya rubuta ayar Allah yasha sannan yaji sauk'i aransa,

Itako inna halima Har kuka tayi ad'akinta taji inama Aisha ba "yar cknta bace da bata ringa kurb'ar wannan bakin cikin ba

Su Yaya Mukhtar kamar su hadiyi zcy Dan haushi da bakin ciki tabbas duk randa Aisha ta dawo inta shiga hannunsu sunci alwashin saita gane shayi ruwane.....

~*Auntyn Sayyada da shahidah*~💘
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

*KANO...*

~*pg 32-33*~

Tun Ahanyarsu ta zuwa gidan Umman deen Hjy salman ta kira megidan nata kamal yana d'agawa tace"Ranka ya d'ade kana ina? Yace mata"ina gida ban fitaba banajin dad'in jikina ya akayi?

Tace"bakomai ganinan da bak'inka"

Yace"bak'i Na kuma? To daga ina amma basuyimin wayaba?

Tace"saidai munxo kawai,

Tana kashewa takalli Teemah dake gefen ta tai mata murmushi tace"my dotah yau zakiga mahaifinki yau Abbanki zaiyi farin ciki Wanda bai tab'a yiba,Dan Allah kisaki jiki damu domin saikin yi mana biyayya sannan zaki samu aljannah,bazamu rabaki da momy da dadyn kiba amma mune dolenki kinji,

Teemah tayi murmushi itama tagyad'a kanta itanma ai a ckn farin ckn take

Sunyi fakin d'in motocinsu a a parking space bayan sun shishshigo da motocinsu uku ta Hjy Salma ta hudun,

Alh kamal kasa zama yayi Dan gabansa keta faman faduwa yanata tunanin wane bakine wadandan da sukaje gun matarsa kafin sugaya masa zasuzo?

Saida takaisu sitting Room kana ta nufi d'akin Mijin nata kicib'us sukai a korido Dan shima saurin yake ya fito sbd yaji shigowar motocin

Yakalleta yaga tana murmushi yace"yadai my madam akwai news ne?

Tagyad'a kanta tace"sosai ma kuwa,yau kukanka ya k'are yau ka xama baba Allah ya amshi tubanka ya amsa maka rokonka mijina

Yace"bangane nufinkiba"ciki kk samu ne?

Ta kama hannunsa tace muje d'akin bak'i kaga wani Abu

Yabita zagwai zagwai

Da sallama tashiga suka amsa masa .idonsa akan deen shikadai ya gane kawai yanemi guri ya zauna sukuma kallonsa kurum suke domin sungano tsantsar kamarsa da Teemah,

Itama teemahn kallon mahaifinta take cikin so da k'auna tabbas ta d'aukoshi idonsa sak nata gashi yanada haske

Bayan ya zauna aka gaggaisa samari da "yammata suka gaidashi

Hjy Salma ta kalli Teemah tace" my dotah dawo kusa da Abbanki,

Tsam Teemah ta mik'e ta dawo kusada Alh kamal ta zauna yak'ura mata ido yanajin wani Abu akanta baigane nufin matar tasaba kwata² yadaiyi shiru yana saurarenta amma zcyrsa harbawa kawai take

Hjy Salma takalleshi tace"dafarko inaso kafara da godewa Allah subhanahu wata,ala domin ayau kukanka ya k'are Allah ya baiyana mana "yarmu da muka rabu da ita tun tana jaririya....

Tayi shiru ta nuna masa Teemah tace" kagan tanan fatimah sunanta Wanda Allah ya baiwa Iyayen rik'on saif ita domin sune suka tsinceta,saigashi k'udira ta Allah data girma kuma sai Allah yasaka soyayya atsakaninta da Saif.......

~*Auntyn Sayyada da shahidah*~💘
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Mutuwar zaune Alh kamal Yy saida matarsa Hjy Salma ta taso ta dafashi ya dawo hayyacinsa hawaye yaji yana biyowa kan kuncinsa hajy Salma tace"bakuka zakayiba Abban Teemah kayi murna ka godewa Allah daya bayyana "yarka kaganta da idanka pls kadaina zubda hawaye akwai yara agun,

Yakama hannun teemah ya rik'e gam tamkar Za,a kwace masa ita yakura mata idanuwansa masu kama da nata yace" kiyafeni my dotah munyi nisa dake baki shak'u damuba nasan kinji cewar duk laifi nane walh nayi matukar nadama nayi Dana sani me hali irin nawama ina masa fatan shiriya ina sonki Mamana,

Teemah batace komaiba saima hawaye dataji suna kwaranyo mata duk Na tausayin mahafin natane tabbas tasakanin iyaye da "Yaya sai Allah taji tana k'aunar Abbanta tasan kuma komai daga Allah ne shiya rubuto mata komai dazai faru arayuwarta

Tasa hannu ta goge hawayensa tana masa murmushi

Hjy Salma tace" Abban Teemah kagodewa iyayen goyon Saif domin sun mana komai arayuwa sunbaiwa diyarmu tarbiyya mekyau sun tsaya tsayin daka akan iliminta Na addini Dana boko tabbas bamuda abinda zamu saka muku dashi saidai muce Allah yabiyaku da gdn Aljanna.

Alh kamal yakalli Alh Lurwan yace"hakika yau ranar farin ciki ce agareni nagodewa Allah kuma ina matukar godiya agareku domin kunmin komai Allah yasaka da alkairi yabiyaku da kairan naji dad'i sosai

Alh Lurwan yayi murmushi yace"babu komai Alh kamal komai muk'addarine daga Allah shiya tsara faruwar hakan tabbas naga kamanninka da Teemah ga kuma irin zoben dake hannunta ahannunka hakika Na Dada yarda da Fatima yarkace

Hjy maryam tacire tagumi data rafka tace"nidama tun a farkon zancen da Hjy Salma taxo mana dashi nayarda da batunta domin baxata xomana da zancen k'aryaba saikuma gashi naga irin zoben hannun Teemah ahannunka Alh kamal
Chapter 13 · 0% Book details