← Book details Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 16

Sashe 8

Chakwakiyar Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace"yawwa to Shikenan ma" sukai sallama yakashe

Nan yake gaya musu yanda sukai da Hjy salman teemah ta gyada kanta dukda taso sugaisa da umman Amma ba yanda zatayi dole su hakura sai wataran d'in

Yakaisu gidansu inna tsoffin arxik'i suka ringa nan nan da teemah sunga matar da jika zai aura inna tabata tsaraba tace takaiwa momynta basu dadeba sukai musu sallama ya daukesu donya maidasu gida....

~*Auntyn Sayyada da Shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

_ina mai baiwa masoyana hkr asakamakon jina shiru banyi type ba wayarce takawon matsala_ _adalilin haka har wata tana bina prvt tana gayamin bak'ar magana akan tace naturo mata da novel d'ina wai nashareta Dan haka insani bani kad'aice marubuciya a Nigeria ba danma nasamu ana son nvl d'ina_ _wasu mutanen basa yiwa "yanuwansu musulmai uxuri d'an Adam fa ajizine_......

~*Pg 13-14*~

Bayan Sati guda daxuwansu gdn Hjy Salma momy kuma tasake saka musu ranar da za,a koma har itan.

Da kanta takira Hjy salman ta jaddada mata zuwansu Dan kar asamu sab'ani

Da ranar zuwan nasu taxo kowa ya shirya za ,a tafi sai teemah ce suka jita shiru bata fitoba momy dakanta tashiga d'akin nata ta tararta dafe da Mara tana juyi agado

Hjy maryam ta tsaya akanta tana tambayarta ko lfy taganta haka

Teemah tace" walh momy marata kemin ciwo tun dazu,

Hjy maryam tace"to basaiki fad'aba kyayi shiru ad'aki mu munacan munata jiranki kitashi kisha magani inyaso saiki daure muje karmu barki ke d'aya agidan

Teemah tace"momy kuje kawai baxan iya zuwaba kugaisar min da Umman nasha magani d'azu inba bacci nasamuba baxai lafaba nasaba duk wata inyi wannan wahalar dama

"Hala period d'inne"?

Gyada kai teeman tayi kawai

" kinada always ko in d'auko miki ?

"Akwai momy"

Hjy maryam tajuya tafara tfy tana fad'in "tomun tafi Allah yasauwaka," amin,adawo lfy"

Bayan futar momy bacci yakwashe teemah saida tafarka tad'au wayarta taga kiran da deen yai mata hr 3 missed call

Tayi murmushi tasan dole zaikira dama,takirashi saida takatse sannan yakirata tad'aga muryarta a sanyaye tai masa sallama

Ya amsa yana fad'in"nakikkiraki naji baki d'agaba ko duk zafin ciwon ne?

Tace"walh bansan ka kirabama baccine yakwasheni saiyanxun Na farka "toya jikin?"

Ta lumshe ido tace"da sauk'i sosai ina Umman tamu ya kuka sameta?

Yace"ga Umma tanata tambayarki nagaya mata ciwon mata kk"

Tayi dry harda rufe idonta kamar yana gun"kai Yaya Amma dai dawasa kake yi ko?
Yace"kamar Yaya da wasa?

Tace"Dan Allah da gaske kafad'i hakan?

Yace"gata ai zanbaki ita kugaisa"
Tace"Ni walh kunyarta nakeji balle kagaya mata haka"

Yace "tosaime itafa Yr uwar kice mace,Ni meyasa bakiji kunyataba?

Tace" aibani nagaya makaba nasan abakin momy kaji,

Yace"OK to bari naje Na mik'awa Umman gasucan afalo da momy suna zuba hira futowa nayi nabarsu muma yanxu zamu taho sbd munbarki ke d'aya agida baxanso adad'eba,

Tayi murmushi tace"to Allah ya dawo daku lfy,kawai kagaidamin Umman ba saika bani itanba Allah Yy da gaske inajin nauyinta,

Yace"da wasa fa nake mk bangaya mata komaiba,

Tana rik'e da wayr yaje yakaiwa Hjy Salma takarba takara akunneta suka gaisa duk akunyace teeman take ita kuwa dayake wayayyiyace saihira taja teeman dashi"Teemah kinxo munyi sab'ani yau kuma Allah baiyi zakizo muganaba naji momynki tace bakida lfy' toya jikin?

Ckn jin kunya teemah tace"da sauk'i Ummah ya Aiki?

Hjy Salma tace"Alhamdulillah ai insha Allahu zanzo walimar saukarku Dan shugaban makarantar taku dan,uwan Alkalin mune kuma tunda har anfada min dake aciki kodanke zanzo d'iyata

Teemah tace"to Ummah Allah yabada ikon Zuwa ngd"

Sukai sallama yakarba yace"kikula da kanki kafin mudawo"

Tace"to Allah yadawo daku lfy,

Sukai sallama yakashe

**********************

Ana saura sati d'aya saukar su teemah "yan London suka dira agidan twins ne da Nabeehat kawai banda iyayansu su sai ana gobe sauka zasu diro,

Nabeehat a d'akin mutuniyarta teemah tasauka sunata murnar ganin juna balaifi feenah ta shiga cikin su tasake bakamar daba datake ad'arere tana sha musu k'amshi kamar wata bare acknsu

Adarenma suna tare a falo suna kallon wani Indian film marriage again, sunata hira akan yanda film din gudana kowacce tana fad'ar tauraronta da tauruwarta ackn film d'in

Suko su hassan da Hussain suna tare da deen a d'akin Sa sunata shan hira ta yaushe gamo sunsaka wani american film basu suka kwanta ba sai d'ayan dare

Washe gari teemah ce tashiga kicin don had'a abin Karin kumallo Nabeehat ta tayata sukai soye soyensu feenah tazo ta d'an tayasu don ba kwarewa tayi aharkar girkiba shayi kawai ta dafa ta tayasu kaiwa dinning table

Sai goma aka had'u a dinning d'in feenah tana kusada Hussain yamballs sukeci suna kurbar shayi suna ayyakawa da junansu sak'onni tabbas Hussain yaga canji sosai agun feenarsa yanxu kam yayarda tana sonsa kamar yadda take fad'a masa a network

Teemah nakusa da deen tanacin buredi da bota atsakiya shiko tana kurb'ar shayi hadin murtuku hankalinta kwance

Shiko deen dankali yakeci su Nabeehat ma abinda suke ra,ayin ci shi suke ci agun

Su momy da dady suna azzumi Monday ce basu fitoba,

Hussain kyakkykyawane dogo kamarsu d'aya da hassan saidai shi hussain yanada wani d'igon bak'i akusada kunnensa kamar tusar jaki ta inda wasu keganesu knn farare ne sunada saje akewaye da fuskarsu halinsu ya bambanta danshi hassan bayada fad'a baida zafi yanayin maganarsa akwai sanyi ck

Shiko Hussain bayada hkr inka tab'oshi yanada zafi ga saurin fushi

Hassan Aikin banki yake acan shiko Hussain barista ne basu dad'e dafara aikinba Dan saida suka had'a digree bibbiyu.

*_____________________*
Da yamma dukkansu suka futa ababbar jeep d'in deen mecin mutane kusan bakwai uku gaba hudu baya

Haka aka had'u anata shan hira ackn motar

Kowacce ta tsala kwalliya shope rite yakaisu kowacce tad'auki abinda takeso deen yabiya suka fito ya zazzagaya gari dasu basu suka dawoba sai ana sallar magriba

Hassan dai dole yahak'urewa son Teemah tunda ya fahimci tana son deen sosai koya fad'a matama babu amfani Dan HK saiya ja bakinsa yai shiru domin yanda yafahimta wannan soyayyar tasu sai Allah

Haka itama Nabeehat tunda ta lura deen yanaiwa Teemah muguwar soyayya tasan tabbas ta makaro dukda yasan da tana sonsa baxata iya yi musu tsaikoba dole tasawa ranta salama dontana son Teemah tana kaunarta sun shak'u ayanxu bazataso taga ta tarwatsa farin cikin taba......

~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘

*KADUNA....*

~*Pg 15-16*~

Yaya Mukhtar yana tsaye yakurawa Aisha datake bacci ido zcyrsa fal da takaicin abinda tajanyo musu Na abin kunya jiyake kamar yashaketa ta mutu ahuta,

Yakalli Aminatu yace"Aisha bata kyautawa kantaba meyasa tajanyo mana wannan abin kunyar,tanaso ta tozarta iyayanmu ne Ashe duk irin tsayawa tsayin daka da aka Baku tarbiya saita baiwa iyayanmu kunya walh yau da agida muke babu mehanani inmata mugun duka yanxun ma Dan bacci takene walh da saina lallasata ko ckn yaxube,Dan walh baxata reni shege agidanmuba,

Aminatu ta rintse idonta hawaye yana surnano mata ranta yana mata suya tabbas Aisha tacucesu ta suci kanta

Yaya Mukhtar ransa ab'ace yace "tashi maxa Ummie mutafi gida babu me zama agunta yanda inna ta tafi muma tafiyar yakamata muyi Dan banga amfanin zama agun wannan" Yr iskarba,kud'in da aka cajeni nagado da ruwa da akasa matama nayi Dana sanin biya a aljihuna Wanda yai mata ckn yakamata yabiya baniba,yana gama fad'in haka ya juya yai hanyar futa

Aminatu takatseshi "Dan Allah Yaya kayi hkr kada mutafi mubarta ahalin da take ck,kome tayi dai mune dolen ta,baxan iya tfy nabarta awannan halin ba Yaya...ya d'aga mata hannu ckn fushi yace" toshikenan aisaiki zauna Mara tunani da kishin kanta inke kina sonta to ita ba sonki takeba bakuma k'aunar iyayenki takeba,yaba gama fad'a mata hakan yafice abinsa

Aminatu takifa kanta akan gadon da Aishan ke kwance ta fashe da kuka

***** ***** *****

Acan gida kuwa da isar inna gida tun ak'ofar gida ta aika am kira mallam

Suna zaune jugum itada inna halima donta gaya mata komai sunyi tagumi kowacce rantaba dad'i suna sak'awa da kuncewa mallam ya shigo yanemi guri ya zauna yana fad'in"ince dai lfy ko?

Inna A'i tashare kwallar data zubo mata tace"inafa lfy mallam Aisha ta janyo mana abin fad'a ackn unguwa ta ja mana magana da terere saidai Allah ya sawwak'a donta gama cutarmu ta tona mana asiri wai cikine da ita...

Mallam yace"ciki? Wanne irin ciki kuma ana zaune qalau?

Inna A'i tace"ciki dai Na d'an mutum Wanda ake cewa ckn shege shitake dashi Aisha ta cucemu ta cuci kanta.

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,haka Aisha tayi,Amma dai ta b'ata wayonta tayi girman banza girman kobo,ba komai kanta ta cuta zanyi maganinta kada kusa wannan aranku yaxo ya dameku abanxa nasan mexanyi,ina zuwa yashura takalmansa yafice

*_____________________*
Sai dare ta farfad'o ta dawo hayyacinta ta warware taji k'arfin jikinta aka bata sallama tun a asibitin Aminatu ta gaya mata komai Na abinda yafaru da ita Na abin kunyar data janyo musu,

Kuka sosai Aisha take da idonta hankalinta yai mugun tashi lallai Ashe zargin da Aminatu take akanta yazama gaskiya tayarda aminatun tafita kaifin basira ko ita dayake jikinta bata ganoba bata tab'a tunanin zatai cikiba balle takare kanta

Aminatu dan sahu ta tare musu drop har gida ackn adaidaita d'inma Aisha ba abinda take sai kuka hawayenta sai zarya yake akan kumatunta cknta ya d'uri ruwa tana tunanin shin wane hukunci zata fuskanta daga iyayenta.

Har k'ofar gida me d'an sahu ya saukesu Aminatu tashiga gida takarb'o kud'i gun inna A'i tabashi

Atare suka shiga ckn gidan jikin Aisha asanyaye sallamr Aminatu suka amsa su innar suna zaune akan tabarma duk sunyi jigun² kamar wad'anda akaiwa rasuwa yau

Aisha ganin basu kalletaba ma balle sukulata mahakan yasa tai sunsum tashige d'akinsu

Aminatu kuwa Alwala ta d'auro donta bada faralin sallar magriba gakuma ishsha,I ya doso,

Ashe mallam aranar yaiwa "yan makaranta da suke semester k'arshe waya su yaya baffa da Yaya suraj cewar lallai lallai duk yanda zasuyi subaro makaranta sutaho gida agobe Dan akwai babbar maganar data taso agidan haka yaiwa Kawu Ibrahim waya shima yasanar masa yaxo goben yanason ganinsa da gaggawa akan wata muhimmiyar mgn
Chapter 8 · 0% Book details