← Book details Bintoto Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 28

Sashe 3

Bintoto Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don hakane rayuwar ƙauyen keyi masu daɗi Shiyasa kuma kowa yasan waye bintoto don kowa yasab ba cikakkiyar ƴar ƙauye cikakkiyar gaja ga ƙaxan tanta da kuma tayi suna akai.
Shikuma Abdurrahamanu yaɗan taɓa karatun shi irin na ƙauyen nasu. Wanda shi a cewar sa yafi son yaxama ɗan kasuwa, kuma so yake yaxama ɗan kasuwan a ilimance da xamanan ce, don haka shiyasa kullum yake fafatukan neman yanda zaiyi ya cigaba da karatun shi, amma bb hanyan yiwuwan hakan, don dana cikin su ma akeji balle har akaiga xancen karatu.
Bintoto kuwa tun da suka fara gudu basu tsaya a ko'inah ba sai a soron xauren gidan su. Wanda sai da suka ɗau a mintoci suna hutawa sannan suka shiga cikin gidan nsu.
Innah ne ta kallesu haɗi da cewa"bintoto na daga inah kk wannan haki da kukeyi na mene? Allah yasa ba tonan faɗa kukayi ba.
Cikin dawai² uwani tace" ahhh wlh innah bamu toni kowa ba. Kawai dai munyi gudune don muyi saurin dawo wa.
Cike da gamsuwa da maganan tasu innah tace" tohh yanxu bintoto shirya ki tafi gidan kitso wurin kuluwa.
Da tohh tabi innah yyn da innah ta kwace ɗaurin da tayi ta gyefen zani ta fiddo naira 30 sannan tamawa bintoto.
Amsa bintoto tayi tana cewa"tohhh innah sai na dawo.
Nan innah ta rakata da adawo lfy.
Da fiton su soro bintoto tace uwani ta tafi gida sai sun haɗu gobe.
Yayin da itakuma ta nufi gidan kitso.
A hanyanta ne na xuwa ta haɗu da mai irin ice creem ɗin nan, nan bintoto ta tsaya tana kallon shi da yaran da suka gyewaye shi, wanda ganin hakan yasa Shi yima bintoto wani irin murmushi sannan yace"taxoh ta amsa.
Aikuwa cikin sauri kunsan bintoto da kwaɗayi nan ta amshe haɗi da cigaba da tafiyan ta, wanda kafun ta kai gidan kitson sai da tashanye tass sannan ta isa gidab kuluwa mai kitso.
Cike da xolaye kuluwa ta ringa cewa"ahhh lallae yau xa'ayi ruwa da ƙanƙara bintoto ne agidan.?
Murmushi bintoto tayi haɗi da cewa"ehhh sannan ta gaidata..bata ɗauki dogon lokaci ba, ta farayi ma bintoto kitson, wanda duk ƙaxantanta gashin kan nan nata har gadon baya, kuma irin gashinnan ne ta cikakkun hausa fulani,ga baƙi ga ƙarfi.
Cike da mamaki da faɗuwan gaba kuluwa ganin duk inta tatsaga kan bintoto sai taga kuɗi, kuɗin ma ba ƙananu ba, yasata cike da tsoro tace"bintoto hala innan ki ta aikeki ne.
Kallon ta bintoto tayi haɗi da cewa "a'ah.
Cikin sharce gumi kuluwa ta hau fiddo da kuɗin daga kanta tana tarawa daga ƙasa, amma ganin kuɗin yaƙi ƙarewa ne yasa kuluwa tace"kai bintoto maxa tashi kije innan ki ta cire kuɗin da ta aikeki da shi, sannan ki bata wannan. Ta faɗi tana mai miƙa mata kuɗun hannun ta, wanda duk ƴan dubu² ne.
Haka bintoto tasaka hijabi ta nufi gida.
Koda ta isa gida bata tadda inna ba, don haka nan ta nufi kitchen don ta ɗora abun da xasuci.
Haka ko taci sa'a da isarta ta cidda komai na tuwon dare, wanda bb ɓata lokaci ta soma haɗa wuta. Wanda kafin lokaci ƙanƙani takusa gamawa, don har tagama tuwon saura miya.
Zaune take tayi zaman dirshan. Tana aukin ƙurxanan cinyan ta, wanda duk inta murxa datti yake ɓanɓarowa. Dai² Abdurrahamanu na shigowa cikin madafin salati ya hauyi haɗi da cewa " binto dama ƙaxanta kk bamu mukeci?
Cikin xare ido tayo waje ta yi saurin haɗi da cewa"don Allah Abdurrahamanu kayi haƙuri.
Biyo bayanta yy dai ² innah na yo sallama, aiko da gudu ta nufeta haɗi da rumface ta.
Nan innah ta hau lfy maoyake faruwa ne...?
Shiru Abdurrahamanu yy don lamarin bintoto yanxu dary yasoma bashi.
Juyawa yy haɗi da nufan ɗakin innah, ganin tafiyar tasa yasa innah mai da tambayar ta ga bintoto, amma sai bintoto tace bakomai innah.
Nisawa innah tayi cikin rashin gamsuwa da mganan bintoto tace" tohh ya kitson an maki?
Turo baki bintoto tayi haɗi da cewa"a'ah innah wai tace kin aikeni, duk in ta tsaga kaina kuɗi take gani, kingama wanda ta ciromun daga kaina.
Ganin kuɗi cike a hannun ta yasa inna baki na rawa tajawo bintoto haɗi da buɗe kallabin kannata, ai ko nan idon ta yacikoro da kuɗin nan a lallan kafe.

Salati innah ta hauyi haɗi da fara xubar da hawaye. Jiyo salatin innah yasa Abdurrahamanu saurin fitowa yana tambayan lfy.
Ae nan innah ta hau nuna mai abun da tagani daga kan bintoto wanda shima cike da ruɗu yajawo bintoto dake binsu da kallo don sam bata fahimci wani abu ba..
Ai yana ganin wannan abu ya maida mata da kallabin ta haɗi da sairin riƙota yana innah muyi sauri muje gidan liman.

Wayyyo bintoto na 😭

Ƴan team bintoto kuyi haƙuri komai xaixo da sauƙi da yardan Allah😭

Kudai cigaba da biyo Alƙalamin Aysha maman teddy don ta warware maku xare da abawa, don tabbas da lauje cikin naɗi....
Sannan naji ruwan comment

*#SHERE T0 ANOTHER GROUPS*

*Maman teddy 🧸*
[4/9, 5:59 PM] mmn Hanif paid: *Tyiping......*

*🌹BINTOTO🌹*

*Episode 6*

*Written by:*
Aysha moh'd(maman teddy🧸)

*ALHERI WRITER ASSO. 📘🖊️*

*A.W.A*

https://www.facebook.com/10798008594602?referre,whatsap

_________________________________

```ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ƙungiya masu aiki domin taimakon Al'umma, ƙungiya masu aiki da naxari da ilimi, Alheri daƙo, Alheri gadon barci```

Kafin kace kobo tuni kowani yaro yakama gabansa, yyn da bintoto bataji maganar sa ba sai dai saukar marin shi jikake tassss....
Cike da firgici ta ɗago haɗi da tashi daga jikin mahamudu wanda ta koma ta zauna.
Wani marin xai kai Mata, sai mai gari da tuni labari ya ishe masa yy saurin dakatar da shi ta hanyar rike masa hannu yana mai cewa"haba Abdurrahamanu wannan ae ba girman ka bane, sam bai dace hakan ba.
Abdurrahamanu ne yake huci kaman zaki nan ya hau cema mai gari"kashe masu ɗa xatayi mai gari taja mana bala'i fitinanniyan yarinya kawai.
Cike da murmushin su ta manya mai gari yace" mal. Abdurrahamanu maxa taimaka ka ɗauko mun wannan yaron muje mu duba lfyn shi.
Sai a lokacin tasami damar buɗe baki ta hanyar sakamawa mahamudu ihu iya ƙarfin ta, inda man ta ruga da gudu haɗi da nufan gidan innah.

Shikuwa Abdurrahamanu bai tsaya bin ta kanta ba, ya dauki mahamudu haɗi da nufan gidan mai gari da shi, wanda bayan ƴan a wanni kaɗan suka samu yaron ya farfaɗo sakamakon adduo'in da mai gari suka dinga yi masa suna tofeshi da shi.

Haka Abdurrahamanu yy tabama iyayen Mahamudu haƙuri akan abun da yafaru.
Da yake mutane ne masu kirki da sanin yakamata nan suka amshe da bakomai ae duka aikin yarinta ne.

Koda Abdurrahamanu yadawo gida nan inna ta faɗashi da faɗa, amma da yasanar mata abun da BINTOTO ta aikata, nan ta hau sallallami haɗi da cewa ta gode mai dayya mata haka.

Sannan ta nufi soronta don tayima bintoto faɗa, amma da isan ta sai ta tarar tuni tayi bacci akan tabarman kaban dake ɗakin nasu ciki ɗaya.
Ganin haka yasa innah juyowa haɗi da cigaba da hargagi.

Bintoto... " bintoto.....
Uwani ne mai wannan mgnan tana bin bayan bintoto.
Jiyowa bintoto tayi haɗi da sakar mata murmushi Haɗi da cewa"ae wlh kinga nace maki dole sai tayimun wannan xanen lallin gashi kuma tayimun kinga wannan juma'an inason nayi wankane anjima zan tafi gidan kitso wurun kuluwa.

Dariya uwani tayi haɗi da cewa"gasky kam kinga rana ta take muje gidan innah mu huta acan, xuwa anjima sai na rakaki gidan kuluwan.

Kafin tace wani abune sujiyo murya mai ban tsoro kuma cike da amo tana cewa"ku ƴaƴan ku taimaka min da sadaka.

Kallonta bintoto batayi ba, illah ma cigaba da tafiyar ta datayi.
Cike da tsoron wannan mata uwani tace"baiwar Allah kiyi haƙuri wlh nan da kk ganmu duka bbu mai naira.
Itako bintoto da bata tatsaya kallon matan ba, balle har tasan ya take yasata cike da masifa tace"toh mun ce bamuda kuɗi maiye na kuma bada haƙuri eyeeeehhh, dalllah xomu wuce, inda mina dashi xamu hanata ne.

Gaba sukayi suka bar matan anan a tsaye, wanda bai fitako biyu sukayi ba, nan sukayi karo da matar a gaban su, nan dukan su suka firgita haɗi da mmkin ganin wannan matan a gaban su, a durkushe da sandarta ta ƙarako gaban bintoto haɗi da cewa"ni kk gayama ba ki da kuɗi ko.
Tohh wlh sai kinsan ni ko waye xaki sani ne, don sai na ɗaiɗaitaki.

Cike tsiwa da yarinta bintoto tace"ahh to mao mukai maki mu? Wlh bb abun da xaki iyamun tunda innah ta tana nan, ka ae tana sona.

Wani wawan dariya matan tayi haɗi da cewa"da hannun ta xata fito mana dake. Mu kai ki wata duniya ta daban.
Kafin suyi mata mgn sai ta ɓace battt, yyn da cike da tsoro suka hau gudu har xuwa gidan innah.

WACECE BINTOTO?

bintoto ta kasance ƴace gurin innah hausi, wanda mukafi sani da innah, kuma ta kasance mata ƴar auta, Abdurrahamanu shine ɗan innah na farko wanda fiye da shaikau innah bata ƙara haihuwa ba, don har ta fara manyanta, sai kuma kwatsam cikin bintoto ya bayyana.
Wanda ta haifi bintoto da shekara biyu mahaifin su wato Mal habu Allah yy masa rasuwa.
Haka dai inna ta cigaba da kulawa ds ƴan ƴaƴan ta. Har bintoto ta girma don gaba ɗayan dangin su a ƙauyen suke.

Banajin comment ɗinku gsky, don haka ina gabda maida littafin bintoto na kuɗi in banjin comment.

Maman teddy 🧸
[4/9, 5:59 PM] mmn Hanif paid: *Tyiping......*

*🌹BINTOTO🌹*

*Episode 9*

*Written by:*
Aysha moh'd(maman teddy🧸)

*ALHERI WRITER ASSO. 📘🖊️*

*A.W.A*

https://www.facebook.com/10798008594602?referre,whatsap

_________________________________

```ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ƙungiya masu aiki domin taimakon Al'umma, ƙungiya masu aiki da naxari da ilimi, Alheri daƙo, Alheri gadon barci...

Dedicate to my fans❤️😍

Wasu suna biyoni private suna tambayata littafai, plz kar wacce takuma biyoni ta tambayani don ban ajiye littafin kowa a wayata don ba karantawa nakeyi ba.

~Kuyi manage da wannan shafin babu yawa.~

A sanyaye kaman ba itah ba tace"Bintoto.
Shiru yy yana naxari kanda ga bisani ya mai da hankalin sa ga excourt ɗin dake bayan shi

Kallon su yayi sannan yace" a taho masa da Bintoto xuwa cikin mota..
Chapter 3 · 0% Book details