← Book details Bakin Shafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Bakin Shafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NASREEN dan girman Allah ki fito

haba ya Khalil dole sai an bi abin da zuciyar sa ta ƙitsa masa bakar saƙa idan har ku yana iya lanƙwasa ku ni wallahi nafi ƙarfin'sa bazan fito ba amshi key ɗin motar ka kai ni gida kaga shegiyar matar nan tasa me suffar bururruka na shiga sai na fasa mata kai

idanuwan altab ne yayi ja be san lokacin da ya fusgota ba ya dinga jan ta har cikin Parlour sa da sauri rufaida ta ajiye burner din hannunta kallon mamaki take mai tace

'' honey lafiya naga kana jan ta..?,

Sai a lokacin ya saki nasreen majeed da Khalil suka shigo gaishe su tayi amma hankalin ya na kan nasreen Allah ya na gani bata kaunar ganin nasreen da namijin ta guri ɗaya itama da za a tambaye ta dalili bata sani ba ajiyar zuciya ta sauke tace

'' sannun ku da zuwa...,

da sauri majeed yace

'' yauwa ki dai yi hakuri ranar farko a gidan mijin ki mun ɗauke shi sai yanzu muka dawo da shi..,

dan murmushi tayi tace

'' wallahi ba komai ga kuri nan bisimillah...,

zama sukai ta kawo musu drinks da snacks a cikin ƙaton tray ta ajiye har yanzu nasreen tana tsaye kallon ta tayi taga jini a rigar ta komawa tayi ta zauna kusa da altab tana jifan ta da wani irin kallo sai dai abin bakin ciki har yanzu nasreen bama ta san da zaman ta a parlour ba.

ya Khalil kai fa nake jira na gaji wallahi so nake nayi wanka na kwanta
tashi khalil yayi yana cewa
Amarya sai na ƙara zuwa na kwashi girki
da sauri altab ya riko shi yana cewa ya zaka tafi bayan ba abin da kaci

da sauri nasreen ta kalle sa tana aika mai da wani mugun kallo wallahi bata san yadda za tayi da altab, ta wuta wannan wanne irin mutum ne duk abin da zai sakata baƙin ciki ya iya shi tace

'' ya khalil ni zan tafi..,

da sauri ya zare hannunsa daga riko da altab yayi mai yace

'' muje ya za ayi na barki, ki tafi ke kadai bayan ba ishashshiyar lafiya gare ki ba..,

ni na samu sauki in anjima fita zanyi

da sauri khalil ya kalleta yace

'' haba nasreen me isaka duk abin da zaki cutar da kanki shi kika fi so..,

tashi altab yayi yace
''ka kyaleta mana dole ne duk abin da take aikatawa tasan ba dai-dai bane kawai dan ta zubarwa da halin mu mutunci take yi wallahi tur da me hali irin naki..,

juyawa tayi ta kallesa sai kuma ta fasa magana da wani abu zata faɗa mai da zai yi sular tarwatsai war farin cikin sa amma da ta tuna idan ka ruwa wani asiri Allah sai ya rufa maka asiri sai ta juya ta fara tafiya bin bayan ta Khalil yayi ya bude mata mota ta shiga ya zayo wajen driver ya shiga a hankali ya fara tuki har ya fita da ga cikin gidan horn yayi mai gadi ya buɗe mai parking ya daidai ta ya fito ya bude wa nasreen daidai da fitowar mamy da mukullin mota a hannunta da alama wani gurin zata chak ta tsaya tana nuna khalil tace

'' wato khalil ban isa na faɗa maka ba ko..?sai abin da kayi niya yanzu mutuncin kane za aka dauko kilaki a motar ka , ka wuce mutane su dinga nunaka da baki..,

sosai maganganun mamy sukaiwa nasreen daci a rai giram Khalil ta gani da kimarsa amma yau da ace ita da ita ta faɗawa haka da ta kwashi ruwan mamaki amma ba komai a juri zuwa rafi wata ran tulu zai fashe ratsawa tayi ta gaban ta ta wuce main parlour ta shiga ba kowa a ciki ita haka ba karamin dad'i yayi mata ba hawa sama tayi ta tura kofar dakin ta,

yadda ta barsa haka tazo ta same sa cire kayanta tayi ta shiga toilet sakarwa kanta shower tayi ta runtsai idanuwanta hawaye na bin kuncin ta da ba dan tsoron Allah ba , da wallahi abin da mutane suke zargin ta shi zata aikata da ba dan gatan Allah dana ya khalil ba da wani zancen ake ba wannan ba to a haka tayiwa Allah godiya..

gama wankan tayi ta dauro towel ta fito jan dressing mirror tayi ta zauna kurawa kanta ido tayi sai a lokacin ta tuna tayi gyaɗa da ta jiƙa kanta dafe kanta tayi ji tayi an turo kofa da sauri ra jiyo dada ce tace

'' yanzu abin da kikai kin kyauta kenan daga yi miki faɗa shine lilkafa ta ci uwar ta da kika tafi har da kwana me kike so jama'a su kiraki bayan sunan da suke kiran ki ada ..,
idon tane yayi ja ta ɗago da fuskarta da sauri dada ta kalle plaster dake kanta ta buɗe baki za tayi magana kenan khalil ya hauro sama yana cewa nasreen ga maganin ki ganin dada da yayi ya tsuguna har kasa yace

''ina wuni mun tashi lafiya...,

Lafiyar qalau alhamdulilah ya miƙa mata ledar maganin nasreen yayi yana cewa yauwa dada dan Allah ki dinga lura da ita tana shan magani na san kinsan ba son sha take ba

da sauri ta kalle nasreen din tace

'' yimin bayani kun sani a duhu me yake faruwa..?,

Dada baki san nasreen bayan ta fita ba hatsari tayi Allah ne ya rufa asiri da tuni yanzu wani zancen ake ba wannan ba yanzun nan aka sallamo ta daga asibiti

kallon tausayi tabi jikar ta ta dashi zuciyar'ta ce tayi ba dadi tana fatan Allah ya kawo karshen wannan abin da ke faruwa komai ya daidaita sanadiyar wannan abu yau kimanin shekaru goma sha ɗaya bata ƙara ganin dan ta ba sai dai waya kullum ya dinga ce mata zai zo ga yau nasreen shekararta ashirin cib a duniya da wasu kwanakin tu tana shekara tara ya bar garin ajiyar zuciya ta sauke tace

'' Allah ya ƙara sauki amma kam na son magani nasreen take ba..,

tashi yayi yana ajiye maganin a kan mirro yana cewa sai an jima kallonsa nasreen tayi tace

'' Nagode Allah ya saka da alkairi...,

amin ya Allah yace ya fita itama fitar tayi shaf shaf ta gama shirinta busar da kanta tayi sannan ta bude wardrobe wata doguwar riga ta dauko read colour da adon flowers black da white colour ba ƙaramin kawata rigar sukai ba feshe ta tayi da tsadaddun turarurruka Sannan ta saka tare da yin bisimilla bata da hannu hannunta irin siririn nan ne kuma bata durar mata har ƙasa ba iya kaurinta ta tsaya ana gano kyawawan diga diginta farare tas da su ...

kunshin da tayi na bikin nan ba ƙaramin kyau yayi a fatar ta ba takalmi ta dauko mara tudu baki ta zura jaka ta dauko ta rike a hannu itama baka ajiyawa tayi da ta tuna bata daka agogo ba daurawa tayi sannan ta dauko mayafi ta yafa buɗe jakar tayi ta saka Atm dinta sannan ta fito tun daga sama take jin hayaniya.

ciro bakin glasses dinta tayi a jaka ta saka daga sama tana iya hango mutane da kakin sojoji da alama yan gurin aikin su altab ne ba ƙaramin kyau tayi ba , wanda zai kalleta yayi tunanin bahaushiya ce zakai tunanin balarabiyar kasar Turkiyya ce saukowa ta ƙarasa yi ba tare da ta gaisar da su ba ta fara tafiya kallonta dada tayi tana cewa nasreen ina zaki ke da ba lafiya ce da ke na chak ta tsaya sannan ta juyo kallon agogon hannun ta tayi tace

''bazan jima ba zan dawo..,

sakar baki wani a cikin su yayi yana kallon ta ba ƙaramin tafiya da itamanin sa yayi ba daman altab yana da kanwa kamar haka amma be fada mai ba yasan irin matar da yake burin aura amma be taɓa faɗa mai ba khalil ne ya shigo kallon ta yayi yace

'' ina zaki bace min kikai ba kin gaji kina so ki wuta..,

dan ya tsuna fuska tayi ta langwabar da kai tace

'' blood line ina so na je saloon kaina yayi min nauyi sannan zan biya restaurant nayi take away zan je na siya mota tun da waccen ba a san ranar dawowarta ba..,

da sauri ya kalleta jin wannan uban lissafi da take yi ko da yake kayan dubu nawa ne a shagonta yace

'' amma kya bari ki sami lafiya sannan dan girman Allah ban da zuwa..,

da sauri ta saka mai yan yatsunta a bakin sa kasa kasa tace

'' ban da zuwa club..,
Sannan ta cire hannun ta daga bakin sa dafe kanta tayi tace

'' da ace karatu ne wannan maganar da na ruga da na gama cin jarbawa idan aka zo yi min saboda na hadda ce kullum maganar ka ɗaya...,

komai da ke nake yi domin kyautatuwar taki rayuwar nake yi nasreen

juyawa tayi ta haɗa ido da altab murmushi ta sakar mai wanda ya kusan zumar da Nasir tace

'' are any way barana na tafi kar nayi wasting time..,

muje na sauke ki

girgiza mai kai tayi dan mayafin da ta yafa ya zame daga kanta raba gashin ta gida biyu tayi tayi kitson nan two step tace

'' okay muje..,

kallon abokanan altab yayi yace

'' soja marmari daga nesa sannun ku kun iso lafiya..,

dukkan su suka masa da alhamdulilah Nasir yace

'' soyayya ta rufe maka ido sai yanzu ka gan mu..,

dariya Khalil yayi yace

'' wacce soyayya kuma muna tauna babban issue ne ya aiki..?,

Alhamdulilah nasreen gaba tayi tana fito da chingum ta saka a bakin ta ganin suna neman cinye ta..,

binta Khalil yayi tabe baki sharifa tace

'' da wannan kyawun nata take rudar maza kinsan shekaran jiya basma da tazo wucewa ta islamiyyar mu lokaci kina aji ta ga wata ta fito malam sunusi wanke hannu ya dinga yi ranar ba ƙaramar dariya nayi ba ..,

dariya basma tayi tace

'' ai ta can canta wallahi komai nata me kyau ne..,
Chapter 9 · 0% Book details