← Book details Bakin Shafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Bakin Shafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri ta ɗago kaf duniya bata da maƙiyi sama da Altab kallo ɗaya zakai wa fuskarta kaga tsagwaran tsana da yayi mata me yayi zafi kuma dada ce wa take tana yarinya ya bauta mata amma yanzu fa ba wanda ya tsana sama da ita wayar ta ce ta ƙara ringing da sauri ta kalli screen ɗin wayar sai neman agaji take ganin sunan humy chairlady ɗagawa tayi tare da barin gurin ,

zama yayi ya saki gauran numfashi gaskiya abin da kai be dace ba ya zaku haɗa mata biyu dan dai tana da dakakkiyar zuciya ce da tuni wallahi wani zancen ake ba wannan ba..

Rufa'i ya faɗa ransa a ɓace

a'zafafe altab ya ɗago yace

'' mene abin daga hankali akan yarinyar nan ba ita ta siyawa kanta ba mutum shi yake saiwa kansa da kansa daraja shekaran jiya ba a hotel muka ganta ba munje kamawa baƙin mu da za su zo ita da ƙawayenta nifa wallahi na tsani yar iskar yarinyar nan gani yayi ba zai iya zama da ita ba shi ya saka yace ya fasa...,

toshe kunnan ta tayi wayar ta ta waɗi species ko wanne ɓangare yayi nasa guri tuni idonta ya ƙada yayi ja abin ka da farar fata ɗurƙusawa tayi ta ɗauki layinta da sauran species din wayar ta fita tayi ta bugo mai kofar zuciyar ta duk a jagule zama tayi akan fafaren kujerun da ya zuba su a farfajiyar shashin nasa zuba tagumi tayi tun da take bata taɓa ganin cin mutunci irin na yau ba amma ba komai duk iyayenta ne sula zata zama abin da suke zargi sai a faɗa da hujja

da wannan tunani ta tashi ta bar gurin dakin ta , ta shiga lokacin ba kowa sun tafi dinner kwanciya tayi ba tare da ta cire komai ba duniyar na juya mata kallon species din wayar ta tayi ta ja tsaki

bacci ne ya kwashe ta ba tare da taci re komai ba

Wannan kenan

sosai guri ya ci ka dam ƙam da abokanan arziki rufaida sai murmushi take baki yaƙi rufewa sosai adda asma ke baza ido ko zata ga nasreen amma ba ita ba alamar ta kardai fa ta jawa kanta daman baffa ciki yake da ita shiru tayi tana tunani ji tayi an taɓa ta da sauri ta juyo dan murmushin karfin hali tayi tace

'' zeena har kun zo...?,

eh wallahi daman tun ɗazu nake neman ki ya taro

zama tayi akan kujera zeena ta ja itama ta zauna adda asma tace

'' wallahi alhamdulillah...,

haka abu kuma ya zama abin gaskiya be mun dadi ba na tausayawa nasreeen yawa wacce aka saka mata hannu yan iskan nawa ne suke auro wa

shiru adda asma tayi tana danna wayar ta ba tare da ta tofa komai ba tasan halin zeena tas ta iya munafurci sannan aminiyar umman yaya ce

uhmm nace ba

ɗagowa tayi tace

'' Please bana son wannan zancen kama yayi muyu addu'a koma mene Allah ya kawo karshen abin idan kuma da wanda ya saka mata hannu insha Allahu dan sa zata aura..,

uhmm Allah ya kyauta

amin ya Allah

Sai ƙarfe ɗaya taro ya watsai kowa ya ɗauki motarsa ya tafi gida lokacin nasreen ta farka jin hayaniyar mutane tashi tayi tana ya tsuna fuska shaf ta manta da zata je club dafa kanta tayi gashi ba waya a hannun ta dole gobe ta je ta siya waya ,

tashi tayi ta cire kayanta ta saka na bacci ta koma ta kwanta ji tayi an turo kofar ta kunna bedside blam tashi tayi tace

'' lafiya kuka shi go min daki...?,

aunty nasreen gurin yayi kaɗan har guestrooms sun cika shine dada tace muzo dakin ki

wata uwar harara ta zabga mata tace

'' to ba guri maza ku fitar min daga daki ina za ku zauna a nan..?,

ke yanzu nan dakin har abin alfaharin kine wai yau she zaki hankali ne..?,

ya jero mata tambayar ajere tashi zaune tayi ta yaye blanket din da ta rufe jikinta da shi dafe kanta tayi ta cusa hannu wanta cikin gashinta tace

'' ku fitar min daga daki saboda tsabar raini a ina zaku kwanta ni bana son matsuwa...,

amma kin iya
da sauri ta ɗaga mai hannu tace

'' kana faɗamin magana iya son ranka narantsai da Allah ka jirayi sakamako zo ku fitar min da ga daki bawai tsoranka nake ji ba altab kaddara ce bata wuce faɗawa kan ka ba idan ba zakai wa mutum fatan shiriya ba be kamata ka dinga jefan shi da mugayen kalamai ba wallahi wata ran sai kai dana sani mara amfani zo ku wuce ku barmin daki kowa da inda ya tashi da shi yake alfahari...,

kallon su basma yayi yace

'' ku jira ni a waje....,

sum sum suka bar gurin suna mamakin nasreen da bata jin tsoransa kowa na gidan tsoransa yake ji musamman ma yaran gidan da yake shi ne babban jika a gidan takowa yayi har ida take tsaye ya zura hannuwansa a aljihu yana jefa mata wanni irin kallo me cike da fassara kala kala

danne tsoransa da yake shiga zuciyar ta tayi musamman ma da taga iya kirjinsa ta tsaya dogo ne sosai amma kibar sa ta shanye tsayinsa bawai kiba sosai ba wacce zatai mai muni aa daidai da kirar jikinsa cikin dar dar tace

'' malam fuce min daga daki...,

shiru yayi mata ba amsa ratsawa tayi zata fita ta bar mai dakin ya riƙo mata hannu fisgewa tayi tana cewa bana bukatar ganin ka nace maka ka fitar min daga daki wannan wacce irin kaddara ce ba za a bar zuciyar mutum ta huta ba daga wannan sai wannan

ba ruwan Ubangiji ke kika saka kan ki a ciki

zama tayi a ƙafa tayi shiru zuciyar ta na tsananin bugawa daguwa tayi taga ya fita jan tsaki tayi ta rufe kofar ta dakyar ta samu tayi bacci

washegari wanka tayi ta shirya cikin riga da wando amma wandon falazo ne Golding colour da riga milk colour stocking dinta gashi wuyan rigar
up-shoulder ne ko yaya tayi motsi ana iya hango kirjinta ɗaukan jakarta tayi ta riƙe a hannu ta yafa mayafi a kafaɗa takalmin kafar ta hil ne shafa kanta tayi shaf ta manta da wula kawai sai ta saka mayafin ta a ka tafiya take tana taku dai-dai har ta fito Parlour kallon rashin fahimta dada take mata tace

'' Khadijah sai ina kuma...?,

kallon a gogon hannun ta tayi tace

'' zooroad...,

ban gane zaki tafi zooroad ba

dafe kanta tayi tace

'' ya Allah dada zanje na bude shagona fa..,

gutsurar tufa tayi tana ci tace

'' Allah ya shirye ki haka kurum kin zamar da kanki na miji in banda zamani ina mace ina buɗe shago ta zauna...,
ɗago wa za tayi suka haɗa ido da altab yana cin wainar shinkafa da miyar a gushi kau da kanta tayi daga shi har rufa'i wallahi ba wanda zata gaisar tace

'' Dada ba laifi bane mace ta nemi halak ɗin ta kinga Allah ya sakamin albarka na har shagon saloon na bude...tun ina yin online na buɗe shago..,

wallahi kuwa da ace miki zaune gari banza gwara ki nemi abin yi cewar rufa'i

ya tsuna fuska tayi ɗagowa tayi jin sallamar blood line hugging din sa tayi tana cewa good morning blood line

morning beautiful lady

cika shi tayi yace

'' beauty me ya samu wayar ki ina ta kira a kashe..,

ta sami matsala yanzu ma wata zani na siyo kafin na buɗe shagona

a'a nasreen ina zuwa haka zuwa fa anjima za a kawo amarya cewar adda asma

murmushi tayi me cike da ma'anoni ta samu damar kuntatawa altab tace

'' yanzu aunty me ya hadani da kawo amarya na tafi neman arziki ko da yake duk neman da kake baya cire ka daga zargin mutane ba..,

hannunta khalil ya kama yace

'' muje na siya miki wata special gift happy birthday to you..,

zaro ido tayi shaf ta manta da yau birthday din ta tace

'' wallahi na manta abubuwan sun min yawa nagode sosai..,

idanuwanta duk ya ciko da kwalla karki damu aini ina sani ummi ma tace '' na taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki...,

da sauri ta kallesa cikin mamaki tace '' anya kuwa...,

Wallahi da gaske nake kinga sakon da ta turomin

ture wayar tayi tace '' basai na gani ba da motar ka za mu tafi ko da tawa...?,

farin cikin ki shine nawa

murmushi tayi tace '' nima haka..,

fita sukai a tare suna hira adda asma ce tace

'' Allah sarki khalil komai yana yi domin ya kawar mata da damuwar ta..,

taɓe baki dada tayi tana cewa kinga alamun ta damu ne kike faɗar haka

dada abin fa zai mata ciwo wallahi kawai dai tana kawar wane dan ma duk tarin kawayenta ba wanda ta gayyata wasu ma basu san za ayi bikin ba...

Wannan shine rufin ashirin da Ubangiji yayi mata da fita ma sai ta gagareta dada ta faɗa cikin takaicin abin

addu'a nasreen take buƙata Allah ya kawo karshen abin nan

cewar adda asma

tabe baki altab yayi yana tashi binsa rufa'i yayi yace

'' dada sai anjima..,

kun gama cinye mata waina ai dole kuce zaku tafi

dariya rufa'i yayi yana cewa adda asma kenan kuɗi muka bata tayi mana tambaye ta idan karya muka yi

a'a abin harda sharri ni ko ficika ba su bani ba

Dada wane be san halin su ba sai addu'a

barin kar wannan mutumin yaji labari wallahi ni tausayawa yarinyar nan nake auran soja ba dad'i wallahi daman gashi ga halinsa

wallahi kuwa kawai dai Allah ya saɓa hali
cewar adda asma

Wannan kenan

wani shu'umin murmushi take saki tun ɗazu ko banza ta nuna mata ƙarfin ikon ta wace mata barno gabas ce kaɗan ta fara gani wallahi

mamy da sauri ta jiyo tace

'' basma lafiya kika shigo min ba ko sallama...,

wallahi nayi kece dai baki ji ba kina tunani

ajiyar zuciya ta sauke tace

'' to me kika zo yi...nan ..?,

wani ne yazo a baƙar mota yace '' na ƙira ki...,
Chapter 2 · 0% Book details