← Book details Bakin Shafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Bakin Shafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wai me ya shiga kan ku ne ina raba ku , kuna ƙoƙarin yin faɗa da hankalin ku da tunanin ku me maƙon ku kuyi wa wani faɗa kune yau da kan ku kuke yi kar ku manta fa lokacin muna makaranta mahaifiyata Allah ya jikanta da rahama har kwatance take mun da ku amma yanzu kune kuke neman illata junan ku

Rufa'i ya faɗa ya share hawaye jikin su ne yayi sanyi musamman Khalil juyawa yayi zai fita sai kuma wayar sa tayi ringing ashe akan kujera ya ajiye ta komawa yayi ya ɗauka ganin baƙuwar number ya ɗaga tare da akarawa a kunne sallama yayi ba tare da wanda ya bugo ba ya amsa sallamar sa ya zarce da cewa kai ne khalil...?,

Cikin sauri yace '' eh nine me ta faru..,

zan turo maka address kazo asibiti yar uwarka tayi hatsari ana buƙatar ku

ehyi me kace kit ya kashe wayar kallon sa rufa'i yayi yace

'' me ya faru..?,

nima wallahi na rasa gane wa me ke faruwa wai zai turo min address yar uwata tayi hatsari

ko nasreen ce

nima haka nake tunani domin na barta a wani hali sai da na tawo nayi dana sanin tawowa amma bara na ƙara kiran shi danna kira yayi message ya shigo wayar sa da sauri ya bude a fili ya shiga karanta wa yace

Unique Care Al-Haramain Hospital
Plot 297 Jido Layout, Danladi Nasidi Housing Estate Mariri

da sauri rufa'i ya karɓi wayar karantawa yayi ka be ƙarasa ba ya karɓi wayarsa ya daka a aljihu ya fita cikin sauri ya ke komai mantawa da yayi mukulli baya jikinsa tsaki ya ja ya koma part dinsa ya dauko key ya fito bude mota yayi ya shiga

yayi mata key ya kusan buge me bawa shukoki ruwa sai kaucewa yayi ganin a yadda yake Sahara gudu a cikin gidan ya bawa ma'aikatan gidan tsoro sudai sunsan baya shaye shaye buɗe mai get me gadi yayi dai-dai sako hancin motar su lubna sai dai sune suka kauce mai amma shi kamar ma be gansu ba

ko da ya hau titi sharara gudi ya dinga yi har ya isa asbitin parking yayi a waje domin ba zai tsaya jira ba har a ba shi katin shiga da mita ayi checking ta ƙaramar kofa ya shiga wayar sa ya fito da ita daga aljihu kiran mutumin ya shiga yi amma ba ɗauka ƙara kira yayi sai a na biyar sannan ya ɗaga kai tsaye yace mai kana kina gani nan a cikin asibitin...?,

Faɗama masa yayi nan da nan ya mai da wayar aljihu ko tsayawa kashe wayar be ba ya shiga reception hannun sa na dama ya shiga akwai hanya miƙe hanyar yayi har emergency room wuru wuru ya fara can ya hango mutumin yana zurga zurga cikin sauri ya ƙarasa yace

'' tana wanne daki ne..?,

kai hakuri yanzu likitoci na kanta ta bugo ne akai nima wucewa na zo yi na ganta na kaita wasu asiti saboda rashin dan sanda ba a karɓeta ba shi ne na kawo ta nan da ita saboda abin yayi yawa zato suke ba hatsari bane

jingina da bango khalil yayi ko me ya faru da nasreen da sa hannun altab shi ne sanadin komai da ya faru da ita kasa cewa yayi sallar magariba aka kirawo dole ta saka ya tafi yayi salla bayan ya idar ya tsaya yayi mata addu'a sannan ya dawo lokacin wani likita ya fito yana share zufa da sauri khalil ya ƙarasa gunsa yace

'' yaya take kun shawo kan matsalar...?,

dafa shi baturen yayi yace

''don't worry everything will be fine..,

kai khalil ya gyaɗa yace

''I can go in and see her..,

yanzu za a fito da ita a Kaita wani dakin zaka iya shiga amma kafin nan ina son ganin wanda ya kawo ta

sai a lokacin khalil ya lura da mutumin nan baya nan yace

'' kawo ta yayi nine dan uwanta shi temaka mata yayi..,

Okay biyo ni office binsa yayi har office dinsa zama yayi sannan yace

'' a'a ga guri ka zauna mana...,

zama yayi zuciyarsa na tsananin bugu buɗe laptop likitan yayi sannan yace

'' yar uwar ka ta kamu da cutar ciwon zuciya me tsanani i am sorry to say

da sauri khalil ya ɗago yana hango baƙar fuskar altab duk shi ya sakata a cikin wannan hali ci gaba da cewa likitan yayi idan ba ayi taka tsantsan ba ko wanne lokacin zuciyar ta zata iya bugawa sannan ta kamu da cutar mental processing disorder amma wannan ba wata matsala bace hankali ana tafiyar fa ita yadda take so zata war ware
idan har kun lura za ku ga akwai abubuwan da take selecting idan kunyi kokarin da raba da shi ciwon zai ci gaba har ya girma ya zame mata matsala

Rubutu yayi a takarda ya miƙo amsa yayi yayi mai godiya magani zai siyo sannan ya biya duk wani kuɗi da aka ka she mata wayar sa ce ta fara ringing cirowa yayi sunan mamy ya gani raɗa raɗa akan screen din wayar sa yasan yanzu za su iya samin labari wata kila saboda haka ta kirawo shi ɗan haka be ɗauka ba...

A yanzu nasreen bata da wani gata da ya wuce nasa insha Allahu ba zai taɓa barin ta tayi kuka ba fita yayi yaci ka ciɓis da mutumin da kawo ta hannu ya miƙa mai yace

'' bawan Allah kai hakuri a dazu bana cikin kwanciyar hankali nagode nagode Allah ya saka da alkairi ya baka abin da kake nema duniya da lahira...,

Ba komai ai yiwa kaina wallahu nayi maka wannan uzurin kallo ɗaya za ai maka a san baka cikin kwanciyar hankali ya me jiki

aa nine da godiya me jiki alhmdllh komai ya zo da sauki

kai masha Allah motar ta tana gurina zo muje na nuna maka inda take...

KU HANZARTA PAYMENT DIN KU BAZAN DADE INA FREE PAGE BA DOMIN SHIGA PAID GROUP ZAKU BIYA

500

Amina Muhammad Alhasan opay 8141785374

Ku turo da sheda ta wannan number 09061890481

ƁAƘIN SHAFI

EPISODE 4

A'a bara na haɗa ka da bakanike ni a kwai inda zani tunda kacs motar ta samu matsala sai ya tafi da ita ya gyara ta

gaskiya ta samu matsala ga ban motar duk ya lotsai ba damuwa kira shi sai na je da shi ya dauki motar

waya ya khalil ya ciro a aljihunsa yace '' to sai dai ban san sunan ka ba..,

dariya yayi yace

'' nima ban san sunan ka ba ni dai sunana HAFIZ JIBRIL MAI DAWA...,

ƙara waya yayi a kunne yana cewa '' KHALIL HAMZA HUSSAIN MAI TANGARAN..,

to nayi saving number ka kai ma sai kayi tawa insha'Allah zan ƙara kawo muku ziyara na ga jikin ta wallahi na tsorata da ganin halin da ta shiga a lokacin da na kawota jini jiƙa min rigata yayi

Okay ba damuwa mun gode sosai wallahi sauke wayar yayi yana cewa kaga be ɗauki kiran ba rana na ƙara yi mai ko Allah zai saka ya ɗaga kaga dare na ƙara yi

Haka ne wallahi

cikin sa'a ya ɗaga karawa yayi a kunne ya danna matsa gefe ci gaba da danna wayar sa Hafiz ke yi har ya gama wayar ya dawo yace

'' ga shinan zuwa ni zan tafi phamarcy na siyo magani..,

okay Allah ya kawo shi lafiya sai ka dawo

amin ya Allah ya ce yana fita da ga gurin ba ƙaramin bill sukai mai ba haka ya dawo hannun sa riƙe da ledar magani daidai karasowar makanike dan haka juyawa yayi yana cewa

ka ganshi ya kirawo ni yana waje zo muje sai ku tafi

wayar sa hafiz ya mayar aljihu suka fara tafiya har wajen musabaha sukai da me gyaran mota sannan ya juyo ya barsu tare da man ya riga da ya gama yi mai bayani

kai tsaye dakin da aka kwantar da nasreen ya shiga tana kwance ban da na'urar da aka saka mata ke motsi alamar tana da rai ba abin da ke motsi a jikinta kanta an nannade mata shi da bandeji ga oxygen da aka saka mata limshe ido yayi ya jingina da bango a lokacin wayar sa ta ƙara ringing wannan karon adda asma ce

ɗagawa yayi cikin tashin hankali tace mai har yanzu fa nasreen bata dawo gida ba ko zaka bincika kaga inda take

kallo yabi gadon da take kwance yace

'' tayi hatsari yanzu haka ina asibitin da aka kwantar da ita amma da sauƙi...,

ajiye Sultan tayi da yake hannunta gaban ta ya yanke ya wadi tace

'' innalillahi ya akai haka ta faru...?,

adda asma ina zan sanu nima kirawo ni akai aka ce ga halin da take ci wallahi kin ganni nan jikina duk ba dadi ga ta nan ko motsi ba tayi sai na'urar da aka saka mata ita ke motsi amma baya ga haka ba abin da ke motsi a jikin ta

innalillahi wainna ilaihir raji'un Allah ya bata lafiya bara na sanar da su

cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa adda asma kin manta dazu me ya faru...? Kinga wanda ya damu da ya neme ta ko yasan halin da take ciki wallahi abar tausayi ce NASREEN farin ciki muka kasa bata shi ya saka take tare da mutanen da take tare da su tafi jin dadin zama da su fiye da kowa

wallahi tun ba yau ba ma fahimci haka ɗebe mata kewa suke shi ya saka take zama da su amma Allah yaye wannan baƙin shafin da ya lulluɓe zuciyar mu da idanuwan mu Amin ya Allah

zan dai sanarwa da daddy Sultan idan zai faɗa musu ya faɗa muku

cewar adda asma

Okay hakan yayi sai an jima

turo min address din gobe zan zo Insha Allah

tu zan turo miki ya faɗa yana kashe wayar

zama adda asma tayi ta zuba ta gumi kasa motsi tayi har sai da uncle Yusuf ya shigo firgigit ta ɗago kanta, ta kallesa tace

'' sannu da zuwa...,

zama yayi ya kalleta yace

'' tunanin me kike..?,

Nasreen tayi hatsari yanzu haka an kwantar da ita a gadon asibiti
Chapter 5 · 0% Book details