Sashe 9
Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Saboda Talba, na daya daga cikin irin mazajen nan masu matukar tsada da wahalar samu, kin ga duk wannan abubuwan da kike da su, Talba na da damar da zai iya cewa ba ya son ki idan har baya son ki, kuma ta zauna, domin kin san mutun ne da baya boye abu a ransa idan be masa ba, kuma babu wanda ya isa ya cilastashi, idan har baya son ki kai tsaye zai fada, amman be amsa cewar baya son ki ba ya aminceâ€
Leila ta dan yi sama da ido.
“Haka ne but...â€
Madina ta tari numfashinta.
“But Talba yana da matukar tsada Leila, Talba wani irin murdadden mutum ne mai wahala sha'ani, yadda kike takama da kyau yana da kyau, yana da dukiya, yana da duk wani abu da ake so a jikin namiji, yana da arzikin da yake jin zai iya tankwara komai yadda yake so, yana ganin tun da yana da komai dole a bi shiâ€
“Shi ne matsalarsa aiâ€
Leila ta fada tana zaunawa kusa da kawarta.
“Yeah ya kasa yarda cewar akwai abun da kudi basa siye, a nan ne kawai yai kuskureâ€
Leila ta yi murmushi.
“Ni kuma zan gyara masa wannan kuskuren, sai na nuna masa banbanci da sauran mata, dole ne ya san cewar ina da kima da daraja, kuma dole ya koyi yadda zai yi rayuwa da ni, all those four years of dating, ni nake bashi hakuri ko da ni ce da gaskiya, ina binsa kamar wani sarki da baiwa, all those years ni nake masa text how are you, so so so this, idan ya bar kasar nan ni zan kira shi na tambayi lafiyarsa, ko na masa sako, amman ko da rana daya Talba be taba daga waya ya tambayi ya nake ba! Idan na yi kwaliya be taba ce min kyau ba, be taba replied sakona ba, be san yai min kyauta irin ta masoya ba, balle har ya dauke ni muje yawo, ba zan taba yarda na aure shi a haka ba, now it's my turn, dole ne ya canjaâ€
Ta karasa yana yawo da idonta a dakin. Madina ta kama hannunta.
“No Leila mutane irin Talba suna da wahalar sha'ani, kuma suna da shaukin kai ga wanda ya iya zama da su, kar garin gyara ki ballo wata barnar, idan kin bashi hakuri a inda kike da gaskiya ai ba laifi ba neâ€
“No dole ne ya gyara, yana son soyayya amman be san yadda zai nuna ta ba? Be san yadda zai biya ta ba? Ban taba kiran sunansa a gaban idonsa ba sai na sakaya, amman shi be taba gwada kirana da suna mai dadi baâ€
Ta karasa tana murmushi.
“I'm such a foolâ€
Ta kai dubanta gurin wayarta da ta soma ringing. Hannu ta kai ta dauki wayar sannan tai picking.
“Hello?â€
“Kanwata ga mu harabar gidanâ€
“Okayâ€
Ya mike tsaye ba tare da tunanin komai ba ta nufi kofar fita.
“Talba ne?â€
“Ali dai Uhm Talba zai zo nan?â€
Ta fada tana mere baki sannan ta fice, hango Motar Talba harabar gidan ba karamin mamaki ya bata ba, domin ko a mafarki bata taba saka ran zai zo ba, kuma bata zaton Ali ya aro motarsa ne. Tun kamin ta sauko entrance din ta canja tafiya, kamar wata hawainiya haka ta rika takawa kamar bata son karasawa kusa da motar.
Da gangan tai haka domin ta san a cikin abubuwan da Talba ya tsaya akwai jira, ko bata masa lokaci for nothing, mutum ne da yake daukar lokacinsa da muhimmanci sosai, dakika daya ko biyu idan ka kara, zai iya rushe ko miye a tsakaninku, hakan yasa yana girmama lokacin wani da ra'ayinsa.
Kamin ta iso Talba ya cika har ya kusan fashewa, ba karamin jihadi yai ba na bawa zuciyarsa hakuri har ta iso. Ali dake front seat ne ya sauke gilashin motar yana murmushi, Talba kam ko inda take be kallo ba sai taba wayarsa yake kamar his life depends on it. Kallo daya Leila tai masa ta dauke kai tana amsa gaisuwar da Ali yake mika mata.
“Lafiya Kalauâ€
Ta amsa tana kokarin juyawa. Sai Ali ya bude motar ya fita.
“Ina zaki je?â€
“Ciki zan koma, baka fada min tare da wani zaka zo baâ€
Kallon mamaki Ali yai mata, ganin ta yi abun da bata saba ba. Wani irin tafasa zuciyar Talba take kadan ya rage ta kone, bude motar yai ya fito a fusace ya zagayo inda take tsaye.
“Na zo nan ne, saboda Daddy ya saka ni, ba dan ra'ayina ba, na fi karfin daukar wulakancin mace ko wace iri ce, na fi karfi na bawa na kasa da ni hakuri wannan ranar ba zata taba zuwa ba...â€
Ali ya rasa inda zai saka kansa, sai kawai ya koma cikin mota ya zauna, shi da ya zo sasanci sai kuma a sake yin fada a gabansa. Talba na gama fada mata haka ya juyo ya dawo cikin motar yadda ya rufe ganbun motar kadai ya isa ya sanar da bacin ransa.
Kamar wanda akai wa gorin tuki haka yai ribas ya rika danna horn, Mai gadin ya bude masa gate da sauri, ya firgi motar kamar wanda ya shirya bakuntar lahira.
“Wannan wace irin soyayya ce Talba me ke damunka, wai anya kana son Leila kuwa?â€
Da mugun karfi Talba ya taka burki, he got lucky babu motoci da yawa a titin.
“Fitar min a motaâ€
Ya fada ba tare da ya kalli Ali ba. Ba sabon abu bane gurin Ali ya saba nasa haka idan ransa ya bace ko suka samu tsabani, sai dai baya hana anjima ya neme shi.
“Kana da matsala Wallahi kana da matsala, wannan mugun fushin ban san inda zai kaika baâ€
Ali ya fada cikin bacin rai.
“Ka san bana son ana min ihuâ€
“Mtsssssâ€
“And i hate tsakiâ€
“Ba zan fita daga motar baâ€
Ali ya fada yana gyara zama. A take Talba ya bude motar ya fita ya barta kunne, ganin hakan yasa Ali yai saurin fita ya zagaya driver side ya cigaba da tukin yana mamakin rayuwar Talba.
Gefen Titi Talba ya dawo ya tsaya, a ganinsa kaskanci ne ya shiga napep balle kuma ya hau babur zuwa gida, not just that even tsayin da yake a gafen titi ba girmansa ba ne, wayarsa ya ciro ya kira direban gidansu.
“Ka zo ka dauke ni zan turo maka location ta whatsapp yanzuâ€
Shine kawai abun da ya fada ya kashe wayar ya kunna datarsa ya shiga whatsapp dinsa ya tura masa location din, sannan ya maida wayar aljihu yana kallon titi, har lokacin zuciyarsa zafi take masa saboda Leila ta kira shi da wani, how on earth zata kira shi da wani?
After like 15 min direban ya iso, da kalle kalle har ya hango inda yake ya faka masa motar, Talba ya bude ya shiga ba tare da yace masa komai ba, shi ma direban be yi kokarin yi masa magana ba domin ya san Talba baya son yawan gaisuwa da kuma kallo, idan kuma kana son bata masa rai to ka cika shi da surutu.
Suna isa gida ya bude motar ya fita ya nufi bangarensu, wato shi da Kabir sai dai kowa side dinsa dabam, kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya jefar da wayarsa kan gado ya cire rigarsa da agogo ya shiga bathroom, sannan ya ciri jean din dake jikinsa ya kunna shower ya tara jikinsa yana kallon kansa a katon madubin dake facing dinsa a bathroom din, kamin ya dukar da kansa yana kallon zanen sunansa da tattoo dake kirjinsa wanda babu wanda ya san da shi sai shi kadai, can kuma ya dago ya lumshe ido.
AMINATU POV.
Kusan ko wane gida dake garin an taba, wasu an kashe wasu an kwashe duka da dabobi, wasu an tafi da yayansu da mata, wasu kuma anyi ma matan fyade, sai dai ba kamar gidansu Aminatu ba, domin wulakancin da akai wa mahaifiyarta ya wuce na kowa mutum goma shadaya a lokacin daya, kuma aka kashe yayyayunta hudu, aka kona rumbun hatsinsu, aka raunata wasu, aka kora dabobinsu.
Ba gidan kadai ba garin gaba daya tsit yai duk kuwa da kasancewar barayin sun yi iya barnar da zasu yi sun tafi, amman tsoro ya hana kowa fitowa, sai kuke kuke kake ji a gidanje, sai dai gidansu Aminatu ya fita dabam da baka jin kukan kowa, har asuba Aminatu na boye karkashin gado, mahaifiyarta kuma tana zaune a bakin kofar idonta a bude amman bata iya komai kamar an zare mata lakka a jiki haka take ji, Sanusi kuma na tsakar gidan a sume. Kamar macijiya haka Aminatu ta fito karkashin gado, ta janyo zanen gadon dake kan gadon karfe dan bono na Inna ta nufi Inna dake kwance tsirara tana kawar da idonta tana kuka har ta karasa kusa da ita ta kulluba mata zanen. Sannan ta juya ta koma inda fitilar kwai take ta dauka ta kara haskenta, ta taka kamar mai koyon tafiya ta fito waje. Wani rawa jikinta ya fara yi hango rumbun abincinsu na ci da wuta, sai kuma ta juya a hankali ta sauke idonta kasa ta kalli gawar Iro, da ta Amadu, ga kuma Sanusi shi ma dake kwance, kafa na zubar da jini, gaba daya ilahirin jikinta ne ya fara rawa kamar yadda bakinta ma yake yi.
“Ya... Ya... Ya.. Ya..â€
So take ta kira sunan daya daga cikinsu amman ta kasa, hawaye sai aikinsu suke a fuskarta. Ta saki fitilar numfashi na fitar mata da karfi, wani kuma na shiga da sauri. Juyowa tai ta kalli Inna dake kwance bakin kofar har lokacin idonta na zubar da hawaye, sai wulakancin da akaiwa mahaifiyarta ya fado mata a rai, komai ya zame mata sabo.
“Me muka musu?â€
Ta tambayi kanta tana wani irin kuka na fitar hankali, sai kuma ta ruga da dugu gurin yayanta Sanusi ta taba shi. Sai kuma ta juya ta kalli yayanta Amadu dake kwance kai a fashe, take ta girgiza kai.
“Ba da gaske ba ne aa, wannan be faru ba, yan'uwana ba su mutu ba, ba ayi ma mahaifiyata fyade ba, wadandan nan mutanen ba su zo ba, komai be faru baâ€