← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy ta lumshe ido ta bude tana murmushi.

“Wani lokacin kana maida Talba kamar wani karamin yaro, ya san yadda zai kula da kansa Alhajiâ€

“Ko da Mu'az zai shekara dari matukar ina raye to shi yaro ne a gurina, a shirya mana abincin rana tareâ€

“An gama ranka ya dadeâ€

Ya mike tsaye sai Amal ta kalleshi.

“Daddy ni ma fa kaga ina fushin nan amman baka ce komai baâ€

Sai a lokacin Daddy ya tuna da tana gefensa sai ya kalleta yana murmushi.

“Amal sorry wata taba ki?â€

Ta nuna Kabir sai Kabir yai saurin daga hannayensa sama ya mike tsaye.

“Na ma bar muku falonâ€

Kamin Daddy yace komai ya nufi kofar fita daga falon da saurinsa yana murmushi.

“Mu yi masa uzuri amman yau kawai next idan ya sake tsokanarki zamu raba gari da shiâ€

Daddy ya fada yana kallon kyakkyawar yarsa. Sai ta sakar masa murmushi.

“Toh Daddyâ€

“Goodâ€

Cewar Daddy yana ciro wayarsa ya kira Talba, ringing daya yai picking kamar daman can kiran yake jira.

“Hello Daddyâ€

“Mu'az kana Ina?â€

Ya kalli katon office din da yake ciki kamar mai son tantance inda yake.

“Office Daddyâ€

“Me kake a office? Yau Weekend?â€

“I don't know...Getting some fresh airâ€

“Baka fada min kana da damuwa ba, mu da kai ba abokai ba ne? Ba ma boyewa juna abu?â€

Wani irin kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya mike tsaye daga inda yake zaune ya nufi windows.

“Daddy ba irin wannan ba you know dan crisis ne kadanâ€

Daddy ya tabe baki yana juya fuska kamar  Talba na gabansa.

“Uhm.. Ka dawo gida yanzu zamu yi lunch tareâ€

“Okay Daddy Allah kara maka lafiya, i love youâ€

Daddy yayi murmushi ba tare da yace komai ba ya sauke wayar, sannan ya nufi wata kofa a dayan bangaren falon wanda zata sadashi da bangarensa.

“Ita Leila ba ya bace kenan? Da ba zaka kirata ka tambayi inda take ba?â€

Daf da zai wuce Momy ta yi wannan maganar sai ya juyo ya kalleta, sannan ya dauke kai ya bude kofar ya fice.
Sai da ya rufe kofar sannan Momy ta tabe baki ta kai hannunta ta dauki wayarta ta kira Leila, sai da wayar ta kusa yankewa sannan Leila ta daga.

“Leila kina ina?â€

“Gidansu Madinaâ€

Ta amsa murya can ciki.

“Ki dawo da wuri, and make sure kin ci abinciâ€

“To Momyâ€

Momy ta sauke wayar sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen.

Misalin 2:30pm Talba ya daka motarsa harabar Daddy, ya fito ya nufi bangarensa kai tsaye hannayensa duka biyu zube a alhaji, tafiya yake kamar wanda baya son shiga bangaren, haka yake idan yana fushi be cika son ya rabi mutane ba ko kuma mutane su rabe shi, a tunaninsa tare da kowa zasu ci abinci, domin Daddy ya saba zuwa bangaren Momy ya zauna a ci abinci rana tare ko na dare wani lokacin har da na safe, sai dai yana yin haka ne kawai ranar kun Assabar da Lahadi. Domin ranar weekend ba ya fita ko'ina sai idan fitar mai dalili ce kamar daurin aure ko wani abun, wannan al'adar ba shi kadai ba har yaransa sun saba da ita, every weekend zaka samu kowa a gida sai mai dalilin fita yake fita.
Ya samu kusan dakika 40 zuwa 50 sannan ya danna door bell din kofar falon Daddy, babu bata lokaci Amal ta bude masa kofar.

“Ya Talbaâ€

“Lil Sis... Waye da waye a ciki?â€

“Just me and Daddyâ€

Ya sakar mata murmushi sannan ta shiga cikin falon, tun da ya hango dinning din babu komai a kai ya tabbatar daga shi sai Daddy za su ci abincin. Kai tsaye ya wuce karamin Falon Daddy inda ya saba zama. Yana shiga ya samu Daddy zaune saman kujera yana amsa waya, sai ya zauna a inda aka jera manyan kuloli ya dauki plate biyu ya zubawa Daddy shimkafa, ya zubawa kansa a dayan plate din sannan ya bude miyar dake ta kamshin naman kaji ya zuba ma kansa kadan domin ba ya son miya tai yawa a abinci ya zubawa Daddy ta jera kofuna biyu ta zuba musu lemu ya hada komai sannan ya dauki na Daddy ya dora masa a dan karamin center table dake gefen kujera da Daddy yake kai. Sannan ya koma ya dauko na shi ya dawo kusa da Daddy ya zauna a kasa, ya soma cin abinsa yana kallon katuwar plasma dake karamin falon, Bayan Daddy ya gama wayarsa ya kalli Talba.

“Na lura har yanzu baka san ka girma ba Mu'az, ya kamata ka koyi hakuri da iya danne fushi, idan ina kiranka na damu da inda kake, wata rana bana nan, domin akwai rayuwa akwai mutuwa, na san kana kokarin ganin ka kawarda damuwa a zuciyar wasu musamman yan'uwanka, amman kai baka san yadda zaka yi ka cire kanka a damuwa ba, sai dai ka karawa kankaâ€

Talba ya dakatar da cin abinci da yake yana sauraren Daddy ba tare da ya kalleshi ba.

“Ka daina fushi da abinci idan ranka ya bace, And su mata ba a fushi da su, lallabasu ake, idan ka san wahalar da na sha kamin ya auri Amina sai ka ji ka tsani matar nan, amman haka na daure dan marayan Allah da ni har Allah ya ba ni itaâ€

Talba ya kalli Daddy yana murmushi mai sauki.

“Haba Daddyâ€

Daddy ya kalleshi yana dariya.

“I'm telling you my friendâ€

Daddy ya kai hannunss ya fara cin abinci.

“So haka zaka yi hakuri kai ta lallabata, mata soyayya suke so da kulawa, no matter how rich they are, anya ma kana kiranta da safe ka ji ya ta tashi? Like hello Baby how was your night?â€

Talba ya saka dariya sosai har yana kwantawa jikin kujerar dake bayansa. Daddy ma Murmushi yai.

“Yes... Gida daya muke da Hajiya kuma a guri daya muke kwana amman kana gani kullum sai na gaishe, ni ban san abun da yake damun ku yaran yanzu ba, mu a da kunya da rashin wayewar addini ya saka iyayenmu da mu kanmu ba su yi wasu abubuwan na more rayuwar aure ba, amman ku a yanzu ga ilmin addini da na zamani a arha ga wayewa amman kuke ta zaman matsalar zamantakewar aure, ban san miye matsalar matasan yanzu baâ€

“So that's mean nine mai laifi kenan?â€

“Kai ne mana, taya zaka samu mace kai tsaye da irin wannan maganar, bana jin yadda kake zaunawa kai hira da ni kana yi da ita ma, kawai kai gaka boss, gaskiya you're not romantic at allâ€

Daddy ya karasa yana wani yatsina fuska, wannan karon dariya sosai Talba yai har muryarsa tana fita kamar ba shi ba, dariyarsa ce ta saka Daddy murmushi mai sauti.

“Trust idan baka canja ba, za a iya kasa kaâ€

Ya daga kafadunsa alamar be damu ba.

“Then ai zan samu wata da gudu maâ€

“Hakan na nufin ba wani son Leila kake ba, because idan kana son ta you won't said thatâ€

Ya dan yi shiru kamar mai nazari.

“No i love her Daddy kawai dai ina sonta, but i won't tolerate nonsenseâ€

Daddy yayi Murmushi yana dafa kafardarsa.

“Idan so ya zurfafa a zuciyarka, baka san lokacin da za ayi maka nonsense ba kuma ka dauka, a lokacin zaka zama wani stupid, fool, za a fada maka baka ga tana maka kaza ba, kace ka ji amman kana sonta ba zaka taba ganin laifin abun da take maka ba, mark my wordsâ€

Talba yayi murmushi irin murmushin nan dake nuna ban yarda ba, ranar ma ba zata zo ba.

“Yanzu ka gama cin abinci kaje ka samu Leila duk inda take ka dauko ta ka dawo da ita gida, kuma ka bata hakuriâ€

“No no no Daddy kasan ni bana ba wanda yake kasa da ni hakuriâ€

“Ba sai kace mata sorry abun da nai ban kyauta ba, no ka mata abun da zata ji farinciki sai ta manta da komai simpleâ€

Ya dan yi jimm yana jin kamar an dora masa katon aiki.

‘Maybe i can try’

Ya fada a ransa a fili kuma sai ya amsawa Daddy da.

“Okay Daddy, for the sake of youâ€

Daddy yayi murmushi yana jinjina lamarin dansa.

FARUQ POV.

A gidan Mahaifiyarsa yai wanka sannan ya fito ya nufi gurin abokinsa, dake unguwar. He got lucky yana gida, yana sallama masa ya fito, bayan sun gaisa Faruq ya gabatar masa da abunda ke tafe da shi.

“Shamsu, na zo neman wata alfarma ne a gurinkaâ€

“Allah yasa zan iya Faruqâ€

Faruq ya busar da iskar bakinsa.

“Wallahi ina cikin matsaloli ba ma daya ba, kasan matsalar kasar nan, mutum zai yi karatu amman aiki shiru, ga dan shagon da na kama sabuwar unguwa ce ba mutane sosaiâ€

“Wallahi kasar ce har ka rasa yadda zaka misalta ta, abubuwan sai a hankali, idan baka yi karatu ba abun ya dame ka idan kuma ka yi aikin ya gagaraâ€

“Shine nake son na fara koyon irin sana'arku, duk da ba iyawa nai ba amman dai idan nayi tare zan iya da yarda Allahâ€

Shamsu ya masa wani kallo na mamaki, a tunaninsa zai ranci kudi ne a hannunsa, sai ya ji yana masa maganar sana'arsu, ba Shamsu kadai ba kusan duk wanda ya ji mutum mai degree zai yi sana'ar gini zai yi mamaki, domin muna a zamanin da masu degree da kuma mutane suke ganin ba ko wane irin aiki ne ya dace da su ba, wani abun ana ganinsa kamar kaskanci ne, ace kana da degree kuma kai yi shi.

“Faruq zaka iya sana'ar gini kuwa? Kai da kai karatu? Kuma jikinka be saba da aikin wahala baâ€

“Shamsu kenan, wanda ya tashi a area kamar wannan kuma dan talaka zai ce be saba da aikin wahala ba? Ya kake magana kamar ba san gidan da na fito ba?â€

“To abun ne da mamaki Faruq naga kai ka yi karatu ka ni ban yi karatun baâ€

“Ka aje komai a gefe ka duba bukatata idan zai yiyuâ€

“Inshallahu, sai dai ka san aikin mu tasowa yake ba wai kullum ba ne sai idan ta samu, inshallahu da mun samu zan kiraka a waya tun da ina da number kaâ€
Chapter 6 · 0% Book details