← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aa an raba dai, Daba... Ba ruwana ba zan fadi suna baðŸ¤, sun dauki rabi, kai duk mun watse garin nan fa yau babu wanda muka bari, Wallahi yau mun aikiâ€

Dayan ya fada cikin mutanen da suka zo da su Aminatu, idan suka ce suna nufin gundu, domin akwai Babbar daba akwai karama, kuma daba kala kala ce, kowa da tashi, suna maganar yaron wata na kuka sai dayan ya ce.

“Kai wacan ya dame mu da kukaâ€

Wanda ke kusa da ita ya fisge yaron, sai ta rike masa kafafuwa tana kuka.

“Dan Allah kai hakuri yaro ne be san komai baâ€

Ba su saurareta ba, sai suka aje yaron gefe suka halbeshi, da sauri uwar ta saka hannunta ta rufe bakinta saboda kar kukanta ya fito ita ma su halbeta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'unâ€

Aminatu ta furta tana jin hawayen ya tsaya mata cak. Sai dayan ya haskata daga masa zuwa kasa.

“Ku daure wadandaâ€

Kamar dabbobi haka aka turasu zuwa wani gurin da babu wanda zai iya tantance shi, suka fara dauresu da sarka. Wasu kuma da igiya irin yadda ake yi ma dabbobi, idan an daure sai a saka igiyar a turke. Sauran da aka baro a garin suna da suke kan babura ba su iso ba sai kusan 6:30am daman can haka ake, idan za a saka mata to wadanda za su kura matan su zasu fara tafiya da su a gaba, su kuma sauran su biyo bayan idan sun gama na su aikin. Sai da haske safiya ya baibaye ko'ina sannan Aminatu ta tabbatar da ba ita kadai take ba, domin a gabansu wasu mazan ne aka daure masu yawan gaske, gafensu kuma akwai mata, gana ganin su kasan sun dade a gurin domin sun galabaita tufafin jikinsu sun yi datti sosai, mazan kuma wasu har gemu ya tarar musu, wasu gashin kai yayi musu yawa, a cikin wadanda suke daure akwai marasa lafiya. Sai dai wayewar gari zuwa karfe takwas an kashe mutun biyu a gaban idonta saboda sun cika tari, wai suna gudun kar su saka musu cuta, da zarar ka fara tari yayi yawa sai su ce a kashe ka kar ka saka musu cuta. A lokacin ne Aminatu ta samu kuzari da karfin zuciyar daura zanen dake hannunta ta suturta jikinta.
A wani kebantaccen guri aka fito da abinci, aka fara bin wadanda suka dade a gurin ana zuba musu 3 Spoon na shimkafa fara babu mai babu gishiri babu komai a ciki, kowa aka zubawa jiki na rawa yake cinyewa yana hadeye yawu, ba a baka abinci wadataccen, kuma baka isa ka yi magana ba. Bayan an gama da su aka biyo gurin su Aminatu aka zuba musu a hannu, ita kam rike nata tai a hannu tana ta kallon abinci kamar wanda bata san abun da ake kira da shimkafa ba. Suna zaune a gurin har rana ta fara dukansu, daga ita sai ireirenta ne suke ta murkususun zafin ranar da ya tsanata, sauran wadanda suka tarar a gurin kam da alama sun sab da zafin rana domin ko motsi basa yi. Wadansu mutanen ne dabam suka nufo inda Aminatu take suka kwance ta tare da wasu matan suka zaga da su zuwa bayan wata zana da aka kafa aka kare ta kamar katanga.

“Kwanta nanâ€

Ya nuna mata wani karamin duhu dake shimfide a gurin. Sai ta kwanta kamar daman can an halittota ne kawai dan ta bi umarninsa, da kansa ya kama zanenta ya cire, ya bude kafafuwanta, sannan ya kwance wando ya kwanto samanta ya ratsa cinyoyinta yana kokarin ratsa jikinta, runtse ido tai, ta ja wani dogon numfashi kamar zata shude, sannan ta fashe da kuka.
  Har cikin kwakwalwar kanta take jin yadda yake ratsa cinyoyinta yana kokarin shigarta da karfi, zabar da ta ji ne yasa ta fasa ihu, sai ya rika kanta ya buga da kasa, a take ta ji kan ya sara mata.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'unâ€

Take ta maimaitawa tana tuna nasihar da Inna tai mata. Bayan ya gama abun da zai yi ya tashi, sai wani ya shigo ya saka zanenta ya shafe gabanta, sannan shi ma ya kwanta jikinta ya aikata irin abun da mutumen farko ya aikata, bayan ya gama wani ya shigo, suka suka bi layi, tun tana iya ambaton Allah tana kuka har ta kai bata iya yin komai, Wallahi sun keta haddi Aminatu tun tana cikin hayyacinta har sai da hankalinta ya bace gaba daya, babu komai a tsakanin cinyoyinta sai jini da fatar gabanta data zazzago tana rawa, bayan sun gama suka janyota kamar shara suka fito da ita suka kawo ta a inda sauran matan suke suka barta nan kwance galala sai zanenta da suka rufa mata a jikin.
  Ba Aminatu kawai sukai ma ba, kusan duk macen da suka dauko sai sun mata haka, suna yi ma mata fyade har sai sun fita hayyacinsu, ba matan kadai ba har da mazan suna keta musu haddi, sai dai ba kowa ce Daba ce suke haikewa mace kamar Dabar da aka kai su Aminatu ba, ta haka ne mazan da aka kama suke gane an ketawa mace haddi, ko kuma namiji, domin idan sun gama suna barin mutun a wulakance.

LEILA POV.

“So kike ki tonawa kanki asiri ne?â€

Momy ta tambaya tana kallon Leila, sai Leila ta girgiza kai tana share hawayenta.

“To na ce ki yi shiru ya isa, babu abun da zai faru, amman wannan kukan da kike zai saka Talba ko Daddynku ya zargi wani abu, bana son tashin hankali kin saniâ€

Kai ta daga mata, sannan ta kai hannunta ta dauki tissue ta goge hancinta, a daidai lokacin da Momy ta faka motar a harabar gidan. Kusan a tare Talba da Amal suka fito har ma da Kabir da ya shigo bangaren ba da dadewa ba.
  Amal da Kabir suka karasa gurin Motar ban da Talba da ya tsaya jikin kofar yana kallon Momy da Leila da ta kasa hada ido da shi. Abun da Momy ta fadawa Talba shi ta fadawa Kabir, sannan ta nufo inda kofar falonta take wato inda Talba yake tsaye yana jiran karasowarsu.

“Sannu da zuwa Momyâ€

“Yauwaâ€

Ta amsa masa sannan ta ratsa gefensa ta wuce cikin falon. Yana tsaye a gurin har Leila ta iso, idonta yayi ja sosai kana ganinta ka san ta ci kuka ba kadan ba, uffan Talba be ce mata ba, bayan kallonta da yake har ta shige cikin Falon.

“Me Leila take yi ma kuka?â€

Ba Kabir daya tambaya ba, har Amal dake tare da Kabir din sai da ta Kalleshi, sai dai bata ce komai ba ta wuce cikin falon. Kabir ya saka hannayensa biyu aljihu yana kallon Talba da mamaki.

“Really? Ina ce matar da zaka aura ce, miyasa ba zaka same ta da kanka ka tambaye ta damuwarta ba?â€

Talba ya dan daga kansa sama ya sauke.

“Kabir Leila tana da matsala you know itâ€

“Tana da matsala ko kana da matsala? Simple tambaya ba zaka iya baâ€

“No baka gane ba ne, ina son na san idan tana kuka ne saboda abun da ya faru da Baaba or not, saboda ban gansu da abun da Momy ta fada baâ€

“So Momy ta yi karya kenan?â€

Kabir ta tambaya yana masa wani kallo. Shiru Talba yai domin be san me zai sake ce masa ba. Ganin hakan yasa Kabir kai hannunsa ya tura kofar falon ya shiga ciki, Talba kuma ya sauke ajiyar zuciya sannan ya nufi bangarensa.

“Momy miyasa za ku dage sai Talba ya auri Leila ne? Ba ku tunanin kamar za ku takura masa ne?â€

Momy dake kokarin yaye mayafinta ta juyo ta kalli Kabir dake tsaye bayanta.

“Ya maka wata maganar ne?â€

“No kawai ina ganin kamar Talba ba sonta yake baâ€

“Idan ba sonta yake ba wa yake so? Tun da kake a gidan nan ka taba jin ya yi maganar wata yarinya? Be taba yin maganar aure ba, sai da Engineer ya gabatar masa da Leila, kuma ya amsa yace yana son ta, idan kuma har baya son ta ai ba zai ce yana so baâ€

Kabir ya kwanto jikin kujerar yana fadin.

“Ina ganin kamar ya amince ne saboda kar ya bawa Daddy kunya... â€

Momy ta daga masa hannu.

“Yana sonta baya sonta, saboda Engineer ya amince what so ever, ba damuwar mu bace, tun da ita Leila tana sonsa, daman shi ai be san so baâ€

“Amman tsakani da Allah fa zai cutu nan gaba, kuma ita ma....â€

“Kabir....!!!â€

Momy ta daka masa tsawa, tare da mikewa tsaye.

“Ka daina yin abu kamar ciki daya kuka fito, kai yana tausayinka ne ko ya raga maka? Ba zaka gane hakan ba sai nan gaba, kullum maganar Talba kake baka duba yar'uwarka, baka tunanin idan aka fasa aure ita Leila zata iya shiga damuwa?â€

“Kara ta shiga damuwa a yanzu, da wanda zata shiga nan gaba... Domin abu ne mai wahala Talba ya canja rayuwarsa, imagine yanzu fa ni yake tambaya miyasa Leila take kuka ba zai iya tunkararta ya tambaye ta baâ€

“Zai canja, domin dole ya canja, dole ne mu gyara masa zama, idan ba haka ba zai wahala neâ€

“Ko kuma ita ta wahala ba..â€

Momy ta kalleshi da kyau.

“Wai Kabir ko so kake mu bar Talba ya dauko mana wata bare can daban? Bayan ga yar'uwarsa a gida?â€

Ya dan tabe baki yana kallon Momy, domin ya san a yanzu ba zata fahimce ba. Daukar mayafinta tai da jakarta ta nufi upstairs rai a bace. Har zata shige dakinta sai kuma ta nufi dakin Leila ta murda kofar a hankali ta tura, sai ta same ta zauna tsakiyar gado hawaye shabe shabe a fuskarta wayarta makalle a kunne, da alama magana take da wani.

“Da wa kike waya?â€

Momy ta tambaya with serious face. Sai da ta sauke wayar sannan ta kalli Momy.

“Madinaâ€

Momy ta karasa shigowa cikin dakin gaba daya, tare da maida kofar ta rufe.

“Leila wannan sirrinki ne, duk amintar da kike da Madina karki fada mata sirrinkiâ€

“Toh Momyâ€

Ta amsa tana share hawayenta.

“Ki dauka kuskure ne kowa ai yana kuskure, idan kina yawan kuka sai ki saka mutane su zargi wani abuâ€
Chapter 18 · 0% Book details