← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 24

Sashe 3

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“So kake jinina ya tsotse ne? Kara min jinin ma ya gagara? Haba Faruq, na wuni ban ci komai ba kuma yanzu ka shigo min da gari?â€

Ta masa maganar kamar zata fashe da kuka, ya sauke ajiyar zuciya a hankali.

“Haba Rafi'a tun da kika ga na shigo miki da gari ai kin san ban samu komai ba ne, shagon na mu sabuwar unguwa ce ba a samun ciniki sosai, tun da na fita har babu wanda ya zo aski, wannan garin ma sai da na biya ta gida Mama ta siyo min aka jikawa Sultan ya sha sauran ne na kawo miki, Wallahi ni tun karin safe da na yi ban sake cin komai ba, kara ke na bar miki gwangwani biyu na wake...â€

Be marasa ta mike tsaye tana masa ihu.

“Kai ka so Faruq kai kaso zama da talauci, sa'aninka suna can sun gina manyan gidaje wasu na da manyan motoci, su ci mai kyau su saka mai kyau, amman kai dube ka? Suturar kwarai ma ta gagareka, ni kaina da nake matarka ina kunyar a tararda ni a gidan nan, gida duk ya lalace, da an yi magana kace komai zai wuce sai yaushe zai wuce? Shekara biyar fa da aurenmu Faruq, ka dube ni ka gani tsabar kyau Baturiya ake ce min fa! Amman na kare a aurenka, auren kaddara auren cin garin kwaki, dan sunan mai dadi ma baka iya kirana da shi ba, Rafi'a Rafi'a, Fee'ah Fee'ah haka ake kirana ba Rafi'a baâ€

Ta nufi dakinta a fusace, shi kuma ya lumshe idonsa yana jin zafin maganar da ta fada masa. Yana zaune a falon har 11pm na dare sannan ya tashi ya rufe kofar falon ya kashe wutar ya shiga dakin ya shiga bathroom yai fitsari ya wanke kafafunwasa da fuskarsa sannan ya dawo dakin ya kwanta bayanta, can kuma ya tashi zaune yai ma dansa addu'a sannan ya kashe wutar dakin, ya dawo bakin gadon inda ya saba kwanciya yai tasa addu'ar, ya ciro wayarsa ya aje a gefensa ya kwanta, a hankali ya kai hannunsa ya fara shafata sai ta buge masa hannun ta tashi zaune.

“Miye haka? Ka dawo min da garin dan jinina ya tsotse, kuma yanzu ka zo min na maka me? Da safe kuma dan ka ya dame ni da kayan fitsari tun da an gagara sai masa pampas, ga wannan tsinannen cikin wahala da yake jini, haba duk ni kadai? Wai kai baka da imani ne?â€

“Rafi'a wai miyasa bakinki ba shi da linzami ne?â€

Ya fada a fusace yana kokarin danne fushinsa.

“Shi bakin nawa ai haila yake, kai kudi ka gani idan zan maka duk wannan, su masu kudi ka ga matansu na musu haka ne? Saboda sun ba su komai gurin kwanciya ma dakin yara daban ake amman kai ka hade ni daki daya da yaronka, anjima kace min na taso muje falo ko? To ba zan je baâ€

Sauka yai daga saman gadon gaba daya ya fice daga dakin, be tsaya a falo ba tsakar gidan ya fita gaba daya ya zauna saman turmi ya daga kansa sama.

“Kun faya kun sai kai Allahâ€

Ya fada yana kallon yadda taurari suka kawata samaniya.
Rafi'a na jin ya fitarsa tai azamar dauko wayarta touching, ta dauki keypad dinsa ta shiga contact list tana neman wata number.
MD Saleh a dai dai gurin ta tsaya ta bude sunan ta kwashe numbers din sannan ta maida wayar ta aje, sai tai saving number da Maryam Dahiru Sokoto, kana ta saka wayarta a silent ta kwanta.

________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*

By Khadeeja Candy

Page -2ï¸âƒ£

“Akwai abubuwa da yawa da rayuwa bata iya tafiya sai da su, a ciki akwai numfashi ci da sha, da kuma soyayya. Bana jin zan iya rayuwa idan babu kai a kusa ni, zan iya rasa ci da sha kuma na rayu da soyayyarkaâ€

Ta nade wasikar da ta gama rubutawa da hausar azami, tana murmushi sannan ta mike tsaye ta maida biron da littafin cikin jakarta ta islamiya ta rataya a jikin kusar dake gurin sannan ta saka hijabinta ta fito.

“Inna an gama?â€

“Auta tun dazun na gama, kin yi sallah dai ko?â€

Ta saka wasikar a cikin jikinta tana murmushi.

“Inna ke ma kin san bana wasa da sallah faâ€

“Haka ne, Auta Allah ya miki albarkaâ€

Inna ta fada Baba da ke zaune saman tarbarma yana sauraren redio ya amsa da Ameen yana murmushi. Sanusi ma dake aikin auna tuwon dawo a bakinsa ya so ma zolayarta kamar yadda ya saba.

“Ku na fasa mata kai da wannan kafafuwan nata kamar itaceâ€

Aiko kamar jira take sai ta fara kukan shagwaba, musamman ganin duka gatanta suna nan Inna da Baba.

“Baba kana jinsa ko?â€

Baba yayi dariya tare da kai hannunsa ya kashe redio dake gefensa, ya tofar da goron bakinsa. Yai mata alama da ta zo da hannu, kamar jira take sai ta karaso inda yake tana ta turo baki ita ala dole an taba ta.

“Auta Mamana, ki daina biyewa Sanusi, shi da yake ragon maza, ke da kike Jaruma, ki daina nuna musu rauninki, kin ga shi kin ga Rilwanu ki daina bari suna saka ki kuka, da an miki aure sai kun yi ta marmarinkiâ€

Ta rufe ido da sauri cike da tsantsan kunyar irin ta ya mace bahaushiya. Hakan da tai sai ya kara saka Baba murmushi.

“Allah ya miki albarka ya nuna mana lokacin Autataâ€

Kasa amsawa tai da ameen domin Aminatu irin yan matan nan ne masu kunya da kawarda ido ga wasu abubuwan. Sai kawai ta mike tsaye har lokacin bata janye hannunta daga fuskarta.

“Wai kunya take, kunya kike kika yarda kina fita zanceâ€

Sanusi ya fada yana dariya, a cikin hasken farin watan Aminatu ta watsa masa harara. Ta nufi inda kwallar tuwonta take ta nada ganwo ta dauka ta dora a kai sannan ta mika dayan hannunta ta dauki miyar dake cikin bokitin roba.

“Ni na tafi gurin sana'a taâ€

Ta fada tana kara murda masa baki, Inna dai bata ce komai ba bayan murmushin da tai. Har ta kai bakin kofar fita daga gidan sai Baba ya kirata.

“Mamanaâ€

Ta juyo.

“Na'am Babanaâ€

“Allah ya miki albarkaâ€

Sai ta amsa tana kallon gefen Sanusi.

“Ameen, yan bakinciki sai dai su mutuâ€

Ba Inna da Baba da Sanusi kadai ba, har Rilwanu da Iro da suka shigo yanzu sai da suka saka dariya, domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, inda Aminatu ta yi habaici ko shagube to ba zai wuce Sanisu ko Rilwanu ba take yi ma.

“Mai tuwo a bani na hansinâ€

Ko kallon Rilwanu ba tai ba ta saka kai ta fice tana cinno baki gaba kamar zai zazzago ya zubo kasa. Kusa da Baba suka zauna ko wane ya aje bindigar maharba da manyan wukaken dake hannunsu. Kana ganinsu ka ga zaratan jarumai, tun daga kirarsu har yanayin shigarsu da muryarsu. Domin suna daya daga cikin manyan yan saka na yanki, abu ne mai wahala ka ga gidan da ke da maza uku ko hudu baka samu yan sakai a gidan ba balle kuma gidansu Aminatu da suke da maza bakwai. Ba wuka ba ko bindiga bata huda mahaifinsu balle kuma su da suke shiga dajijikan kauyen neman barayi da kansu.

Tana yin nesa da gida kadan sai murmushi ya wanke mata fuska, a cikin abubuwan da tafi kaunar a rayuwarta akwai yan'uwanta, musamman Rilwanu Sanusi da Musa, domin sun fi sauran sake mata, da kuma kyautata. Gashi basa yarda ko da wasa wani ya nuna mata yatsa a waje balle har a taba ta.
A natse take tafiya, tana ta mikawa mutanen data sani kuma suka santa gaisuwa cikin girmamawa, musamman abokan mahaifinta, sai da ta kusa dandali sannan ta rage saurin tafiyarta da alama akwai wanda take jira ko take son hangowa, can kuma ta ja ta tsaya ta juyo tana kallon hanyar data fito sai ta hango masoyinta tafe da saurinsa cikin shigar kananan kaya, murmushi ne ya cika fuskarta, sai ta sauke idonta kasa domin bata jin kunyarta zata barta tai ta kallonsa har ya karaso inda take.
Sai da yai wani gyaran murya ya waiga ya ga babu mai ganinsu sannan ya ce.

“Autaâ€

“Na'am barka da dareâ€

“Yau ina fitilarta?â€

Sai da yai maganar ta tuna da zancen wata fitila, sam ta manta bata zo da ita ba, sai a yanzu ta suna ta bar fitilar a dakin Inna bayan ta gama rubuta wasikar.

“Wallahi na manta taâ€

Ta fada tana dukawa ta aje bokitin miyar dake hannunta, sannan ta saka hannu a cikin zanenta ta dauko wasikar ta mika masa, ya karba da dayan hannunsa dayan hannun kuma ya mika mata tasa wasikar.

“Na je gida na karbo miki?â€

Ta zaro ido.

“Kai Baba yana nan fa, ni ban saba aikin maza a gidanmu baâ€

Yayi yar dariya yana kokarin magana suka ji muryar Sanusi.

“Auta...â€

Ba karamin tsoro Aminatu ta ji ba, domin bata saba tsayuwa da maza har a ganta ba, duk kuwa da kasancewar ta kai munzalin da zata iya yin hakan, amman kunya da tsoron yayyunta ya hana ta yin haka, duk inda ta san idan ta tsaya da wani za a gani ayi mata magana ko fada bata yarda ta tsaya a gurin. Maniru ne ya soma wayancewa ya mikawa Sanusi hannu suka gaisa, Sanusi ya amsa yana musu dariya.
Chapter 3 · 0% Book details