← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 24

Sashe 7

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“To na gode sosai sai na jikaâ€

Ya mika masa hannu sukai musabaha, Shamsu ya koma cikin gidansa cike da mamaki, Faruq kuma ya nufi titi cike da damuwa.

FEE'AH POV.

“Gaskiya kina da kyau sosaiâ€

“Thanksâ€

Shine reply din da tai ma mutumen da facebook bayan ta tura masa hotunanta masu kyau, kamar yadda ya bukata.

“A ina kike da zama a Gusau?â€

Wannan karon tashi tai zaune tana tunanin irin karyar da zata masa, domin bata fada masa cewar tana da aure ba, duk kuwa da kasancewar bata dora hotonta a profile picture ba, sai hoton sunan Allah data saka as her profile picture dinta.

“Gida dariâ€

Ta bashi amsa.

“Na san gurin idan na shigo zamfara inshallahu zan neme ki mu gaisaâ€

“To Allah ya nuna manaâ€

Ta bashi amsa tana murmushi, kamin ta sake shiga profile dinsa ta duba komai nasa, ciki har da gurin da yake aiki da kuma hotunansa, kana ganinsa ka ga wani hamshakin mai kudi mai connection da yan siyasa, domin yadda ake masa fadanci a profile ma ya isa ya sanar da hakan. Murmushi ta sake yi sannan ta dawo inbox din ta duba tambayar da yai mata ta biyu.

“Are you on whatsapp?â€

“Yeahâ€

Ta bashi amsa da sauri tare da rubuta masa number wayarta ta tura masa.

“Okay Thank You so much Baturiyaâ€

Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana jin sunan har cikin ranta. Sannan ta fita facebook din ta shiga whatsapp, few massage ta samu ciki har da reply din da MD Saleh yai mata, shi ta fara budewa da sauri jikinta har rawa yake kamin ta gama karantawa.

“Subhanallahi, Allah ya wadata, turo account number dinkiâ€

Mikewa tai tsaye ta daka wani uban tsalle ta dire tsabar murna da jindadi sannan ta tura masa account din tana masa godiya.

“Alhamdulillahâ€

Ta furta sannan ta shiga group chat dinsu na makaranta, ta fita ta leka na matan aure ta fita ta shiga na novels nan ma bata dade ba ta fita ta bude chat din Ramlee.

“Kawata kin yi ciniki, wani ya ga Hotonki a wayata ya matsa na nemo masa keâ€

Tana gama karanta sakon kawarta Ramlee ta zaro ido tare da sakin baki a lokaci daya, domin ta san sana'ar kawarta, tana da connection da manyan masu kudi tana hada su da mata kyakkyawa kuma masu siga kamar yadda ita ma take hulda da su, sai dai duk iskanci Baturiya bata taba aikata alfasha ba, za dai hadu da mutum har su gaisa ko kuma ta yi masa nata wayon ta waya ta samu yan canji, amman bata san tai mu'alama da maza ba, bayan Faruq babu wanda ya taba saninta a ya mace.

“Gaskiya aa Ramlee ni dai ina jin tsoro ba zan iya ba, amman idan kin san irin wanda zan yi ma wayo ne na ci kudinsa ba sai mun hadu ba, ba matsalaâ€

Ta mayar mata da amsa duk da kasancewar Ramlee tana Offline a lokacin, sannan ta kashe datan ta aje wayar ta mike tsaye ta fito waje.

“Sultan zo nan yau zamu ci kazaâ€

Ta fada tana zaunawa jikin kofar falon tana mikawa danta hannu fuskarta cike da murmushi kamar yadda zuciyarta take fal da farinciki saboda kudin da za a turo mata, Sultan din ya rugo da gudunsa yana murna.

“Abba zai siyo mana neâ€

Ta shiga kabe masa riga tana fadin.

“Ba nace ka daina cewa Abba ba? Ka rika cewa Daddy, yayan talakawa ne suke cewa Baba ko Abba, yaran masu kudi kuma su ce Daddy ka ji?â€

“To Daddy ne zai siyo mana?â€

“Aa adashen zan kwasa yau sai na siyo mana, amman karka fadawa Daddy ka kaji? Har da lemun kwalba zan siyo manaâ€

Sultan din ya shiga murna yana jindadi yau za su ci kaji, rabon da su ci nama har ya manta.

AMINATU POV.

A bakin kofar shiga gidansu ta hadu da Sanusi tsaye yana latsar karamar wayarsa.

“Ya Sanusiâ€

Ya kalleta sai kuma yai dariya.

“Igee ai sai ki fada mana cewar kin fara fita zance, mu shirya yi miki aureâ€

Ta cinno baki gaba.

“Ni dai dan Allah ka daina, Allah yasa ba ka fadawa Inna ba ko Babaâ€

“Ban fada ba, amman dai zan fada masa, Baba ma baya nanâ€

“Ina yaje?â€

“Gwaggo ta Makka aka aiko bata da lafiya sosai, shi ne suka je tare da Junaidu a baburâ€

“Yanzu?â€

“No tun dazunâ€

“Allah ya bata lafiya shi kuma ya dawo da ita lafiyaâ€

“Inna tace naje na dubo ki, idan kin shiga ki ce ni na zo da keâ€

“Wallahi ba zan fada baâ€

Ta fada tana nufar cikin gidan.

“Ni kuma zan fada mata cewar kin yi saurayiâ€

“To na bariâ€

Ta yi saurin fada har tana dawowa baya, sai ya saka dariya ya biyo bayan kanwarsa suka shiga cikin gidan tare. Kamar Kullum inna na zaune tsakar gidan tana jiran dawowarta, domin bata bachi sai ta saka yarta a ido.

“Oyoyo Auta yar albarka, an siyar ko?â€

Aminatu ta aje kwallon tuwon da bokitin miyar da plates din roba a gaban ina tana sauke gajiya.

“Eh Inna wai Baba ya tafi gurin Gwaggo?â€

“Eh an aiko bata da lafiya, aka ce mai rabon ganawa da ita ya zoâ€

“Allah ya bata lafiyaâ€

Ta fada cike da damuwa, sannan ta ciro kudin cinikin ta mikawa Inna, sai da Inna ta kirga kudi ta ga sun cika sannan ta cire wadanda ta saba bata tana sakawa a asusu ta mika mata.

“Ga na kiâ€

“Na godeâ€

Ta fada bayan ta karba tana kallon Sanusi zuciyarta sai raya mata take zai fadawa Inna maganar, sai har sukai yar hira da zasu yi suka gama bata ci ya dauko zance ba, hakan yasa ta ji dadi sosai. Bata bude wasikar da Maniru ya bata, da fitilar da take zuwa talla ta haska wasikar da ya rubuto mata da hausar ajami, tana karantawa sai murmushi take tana jindadin yadda ya jera mata kalaman soyayya da kwantar da hankali.

Bayan ta gama karantawa ta rumgume wasikar a kirjinta, can kuma ta tashi ta saka a cikin littafanta na Islamiya kamar yadda ta saba, sannan ta gyara gurin kwanciyarta ta kwanta. Inna kam bata kwanta ba sai da ta gama komai ta kintsa komai kamar yadda ta saba sannan ta kwanta tare da rage fitilar kwai dake dakin, hasken ya rago sai dai bata kashe gaba daya ba saboda Aminatu na tsoron duhu sosai, bata bachi babu fitila a kusa da ita.
Misalin 12am gidan yayi tsit domin kowa ya nemi gurin kwanciya ciki har da yan awaki da tumakin da ake kiwo, can cikin bachi Inna ta soma jiyo hayaniya, tare da karar babura hakan yasa ta ta tashi zaune tana sauraren jikinta na bata ba lafiya ba, domin kowa ya san matsalar kasar a yanzu, balle kuma su da suke kauye. Aminatu kam sharar bachinta kawai take bata ma san ana yi ba, jin ihu da kuma fadar Innalillahi a makota yasa Inna ta nufi inda Aminatu take ta shiga tashinta.

“Auta Autaâ€

Ta fada murya can kasa kasa, a hankali Aminatu ta bude ido ganin Inna yasa ta tashi zaune.

“Inna...â€

“Shiiiiiâ€

Inna ta mata alama da tai shiru. Wanda hakan yai daidai da banko kofar gidan ta kwano a shigo, ga wata uwar fitila mai shegen haske da suke ta hasken gidan da ita.

“Innalillahi Wa'inna illahirraji'unâ€

Inna ta furta gabanta na bugawa da mugun karfi, Aminatu ta mike tsaye da sauri kamar wanda ta rude, Inna ta shiga duba dakin tana jin kamar ace akwai wata hanya da zata bi ta fita, a rikice ta nufi gadonta.

“Shiga nan Auta shiga shigaâ€

Da sauri Aminatu ta nufi karkashin gadon na karfe ta shige, zuciyarta na wani irin zillo kamar zata fito, Inna ta nufi kofa domin duba sauran yayanta sai dai kamin ta isa kofar suka shuri kofar da mugun karfi ta cire suka shigo cikin dakin kamar an aikosu. Baya baya Inna tai tana fadin.

“Innalillahi Wa'inna illahirraji'uâ€

“Rufe mana baki dan ubankiâ€

Yanayin yadda yai maganar da karayar halshe kadai ya isa ya sanar da cewar gayu ne suka hauro garin a yau, wato bandits abun da ba a taba ba, domin duk wani hargitsi da ake fama da shi sai dai su ji a makotan kauyukan ko kuma a hanya abun ya rutsa da yan garin, amman ba a taba shigowa cikin garin ba. Ba Inna kadai ba har Aminatu dake karkashin gado sai da ta saka hannayenta ta rufe bakinta. Ta ko'ina jikin Inna rawa yake, ganin manyan makaman da ke hannunsu.

“Ina mijikin yake?â€

Kasa magana tai bakinta sai rawa yake kamar jikinta ga wani gumi dake karyo mata.

“Wato ke ce uwar yaran ga yan iska ko?â€

Nan ma Inna kasa cewa komai tai sai ambaton Allah take a zuciyarta, hannayenta duka biyu rike da bakinta.

“Innalillahiâ€

Inna ta jiyo muryar yayanta a tsakar gidan, wani irin abu ne ya ziyarci zuciyarta sai ta ji kamar ace akwai abun da zata iya yi ta ceci yaranta.
Dun dun dun ta ji tashin bindiga kamin ta tantance komai ta ji muryar Sanusi yana kuka.

“Wayyo Allah na, la'ilaha illahu, Innalillahiâ€

A lokacin ne hawaye ya cika idonta, irin hawayen da kowace uwa take yi idan ta kasa taimakon yayanta.

“Wayyoâ€

Ta jiyo ihun matar Amadu, bata san da inda kuzari ya zo mata ba har ta iya tambayarsu kamar ta rikice.

“Me muka muku?â€

“Tambaya ma kike? Ba kun aje yan sakai a gidanku ba, wai masu yaya ko? To yau sai mun kashe su sai mun muku wulakanciâ€

Inna ta hade hannayenta biyu tana kuka tana rokonsu.

“Ku dubu girman Allah ku yi hakuri, ku kashe ni kar ku kashe yarana dan Allah...â€

Bata gama rokon ba, wani ya karaso kusa da ita ta fisgi rigar jikinta.

“Cire wannan rigar ai har ke da kike uwarsu ba zamu bari baâ€

Sai a lokacin Inna ta kara firgicewa, ta fara bin fuskokinsu da kallo tana ganin komai kamar a mafarki.

“Cire cireâ€
Chapter 7 · 0% Book details