← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 24

Sashe 8

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta rika jin kamar ba hausa suke mata ba, gaba daya ta rasa gane abun da suke nufi, bata fahimci manufarsu ba har sai da suka barge rigar dake jikinta suka kama zanen shi na suka fisge suka jefar da shi can gefe, suka mata tsirara a gabansu. Aminatu dake karkashin gado ta yi saurin kara rufe bakinta wasu irin zafafa hawaye na sauko mata, saurin rumtse ido rai hango mahaifiyarta tsirara a kwance yaron da be wuce sa'ar danta na biyar ba ya fara keta mata haddi!!
Ba mutum daya yai ba, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba, haka suka jera su goma sha daya suka yi mata yadda suke so, sannan suka fita suka barta kwance kamar tsumma. Abun ka da uwa suna fita ta yi karfin halin rarafawa ta isa inda zanenta yake da idanuwan da take jin kamar kukanta ya kare a yau. Ta dauki zanen da hannunta amman yadda zata sarrafashi ta daura ta suturta jikinta ne ta manta sakamon jin ihun Sanusi, cikin rashin kuzari zuci da na jiki ta isa jikin kofar tana kallon yadda yan bidigar majiya karfi, suka danne Rilwanu a kasa, dayansu ya kunna babur dinsa ya hau ta kan wuyansa ya tsaya.

“La'ilaha Illahuâ€

Inna ta fada da wata irin muryar da bata taba sanin tana da ita ba, tana mika musu hannu. Ba su kulata balle su fasa abun da suke, ba su saukar da babur din a wuyansa ba sai da suka tabbatar ransa ya rabu da gangar jikinsa, daman haka suke ma irin su Rilwanu masu aikin sa-kai domin kare rayuwarsu da kuma ta al'ummarsu, idan suka halbeka da bingida suka ga bata tashi ba, sai su gwada adda, idan ita ma ba tai ba sai su saka dutse ko babur. Bayan sun kashe Rilwanu suka fashe rumbun hantsen dake gidan suka saka Iro a ciki suka kunna masa wuta, tare da hatsin. Wani irin ihu yake yana neman ceto amman babu wanda zai iya kawo masa dauki.

“Kaico Kaico kaicoâ€

Inna ta fada tana kallon yadda danta ke ci da wuta, ga kuma wani a kwance, wani irin shiga da fita numfashinta ya rika yi da karfi, tana jin wani abu na mata yawo a ciki, gaba daya sai ta nemi dan sauran kuzarin nata ta rasa, a bakin kofar ta fadi kwance yawu da majina suna zubo mata a lokaci daya, cikin karfin hali ta dan dago kanta ta juyo ta kalli Inna Aminatu take boye, sannan ta juya tana kallon yadda suka dauko katon dutse suka daga sama suka saki a akan Amadu da yake da wasu barayin suka danne a kasa ko motsi baya iya yi, kamar yadda sukai ma Amadu haka wadancan barayin da suka zagaya gidan Musa suka masa, domin duk wanda ya san yayan Mai Damma ya san wuka ko bindiga bata hudasu, ya sha kuma ba bawa yaransa, ba dan komai ba sai dan kariyar irin wannan ranar, sai dai ayau shan be amfana musu komai ba, ba su kadai ba har da sauran mazan gari da bindiga bata fasawa, sukan kashe su da babur ko dutse, balle kuma Rilwanu da Iro da sukai kwarin suna a garin saboda aikin sa-kai da suke.
Sanusi kam sai yai kamar ya mutum ganin nasa mai sauki ne, domin da babur sauka hau kafarsa dan kawai su gana masa azaba, baya ambatar komai sai Allah, ba a gidan Mai Damma kadai ba, a garin gaba daya haka suka ci suka shude babu wanda ya kawo agaji, suka ci karensu babu babbaka yadda ransu ya so sannan suka bar garin bayan su kwashi abinci da mata cikin har da matan Musa da matar Amadu.

________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
I just published "04" of my story "BAKAR WASIKA". https://www.wattpad.com/1188003519?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=gvBvvJY%2Brh7%2BfdxLjDxcLbTx9rDGdNBA0sMHgr3XMPr%2FqwZ4sIWJ88oZCr4nOa%2BILP0eBQ%2FKRLIQm73M62araHO6%2BoJXjoYprLv7YGhRYyguc1ysae3vRDycS1qvuqiM

*💔 BAKAR WASIKA 💔*

By Khadeeja Candy

Page -4ï¸âƒ£

“So yanzu ka yarda zaka bata hakuri kenanâ€

Talba ta girgiza kai.

“Kai no never ni fa ba zan taba ba wanda yake kasa da ni hakuri baâ€

Ali ya kalleshi.

“Amman ka ce Daddy yace laifinka ne, kuma kaje ka bata hakuriâ€

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa ya sauke numfashi a hankali.

“Yeah ba wai yana nufin na ce tai hakuri ba, ni yanzu so nake ka kirata ka bata hakuri kuma ka dauke ta ku je yawo ta wayance Shikenan komai ya wuce, amman karka ce ni na ce ka bata hakuri faâ€

Ali ya rausayar da kai yana kallon abokin nasa cike da mamaki.

“Miye a ciki dan kace tai hakuri? Ko kuma ka dauke ta kuje yawo, faduwa kai?â€

Sai Talba ya amsa masa kai tsaye.

“Yes, taya zaka bawa mace hakuri macen ma wanda take kasa da kai, ni me fa Aliâ€

“To wai idan kuka yi aure kuka samu matsala, kuma kai kake da laifi...â€

Kamin Ali ya karasa Talba ya tari numfashinsa.

“Sai ta ba ni hakuriâ€

Ta fada da iyakancin gaskiyarta, domin har ga Allah be ga dalilin da zai saka shi bawa wanda ke kasa da shi hakuri ba, kuma mace sai dai shi a ba shi. Ali yayi murmushi.

“Yanzu dai for the sake of Daddy zaka yiâ€

“For the sake of him na zo har ina rokonka da kai, idan ba haka ba babu abun da zai saka na roke ka maâ€

“Look Talba I'm not her boyfriend, ban san kalaman da zan mata ba, kuma ba ni nai mata laifin nan baâ€

Talba ya mike, ganin hakan yasa Ali ma ya mike tsaye.

“Fine, amman tare za mu je, kana driving ina bayaâ€

Talba be ce masa uffan ba ya nufi kofar fita, wanda hakan ya tabbatarwa Ali cewar ya yarda kenan. Sai da Ali ya shiga yai sallama da Samira sannan ya fito ya samu Talba a cikin motarsa. A hankali Talba yake tukin har suka fita daga cikin gidan suka hau titi.

“Kirata ka tambaye ta tana inaâ€

Ali ya masa wani kallo.

“Kiran ma? Talba wai kai zaka bata hakuri ko ni? Just ka kirata ka tambayi tana ina ma you can't?â€

Ko kallon gefen Ali Talba be yi ba balle ya tanka masa.

“Fineâ€

Ali ya fada sannan ya zaro wayarsa ya shiga contact dinsa ya nemo number Amal, domin baya son batawa kansa lokaci tambayar Talba number ta zai iya ce masa baya da ita ma. Ringing biyu ta dauka.

“Helloâ€

“Hello Lil Sis ya kike?â€

Ta yi murmushi jin ya kiranta da sunan da Talba yake kiranta.

“Na'am Ya Ali ina lafiyaâ€

“Good number Leila nake soâ€

“Okay zan turo maka yanzuâ€

“Thank Youâ€

Ya aje wayar yana kallon abokinsa tare da mamakin halinsa. In few minutes Amal ta turo masa number, a take ya kira Leila, abun ka da mai jin kai sai da wayar ta yi ringing ta katse bata daga ba, har sai da ya sake kira, wannan karon ma sai da ta kusan yankewa sannan ta daga kuma tai shiru tana sauraren mai kiran, daman can haka take babu yadda za'ayi ka kirata kuma ka yi expecting ita zata fara maka magana, sai da Ali ya saka wayar a speaker sannan ya fara magana.

“Kanwata Leila kina lafiya?â€

Jin muryar Ali yasa ta dan sake domin ta san waye shi.

“Ali ya weekend?â€

“Alhamdulillah kina ina?â€

“Ina gida dari gidansu Madinaâ€

“Okay gani nan zuwaâ€

Be jira abun da zata ce ba, ya aje wayar ya kalli Talba.

“Idan munje ta fito kai zan bata hakuri sannan na baku guri ku yi maganaâ€

Talba ya masa wani kallo irin really!

*** *** ***

Leila ta aje wayar tana tabe baki.

“Waye?â€

Madina ta tambaya tana gyara kwanciyarta.

“Ali wai gashi nan zuwa?â€

“To ko ya san abun da ya faru tsakaninku ne?â€

“Maybe ai Talba baya boye masa komaiâ€

“Kin gani na fada ya damu faâ€

“Ya damu amman be kira ni ya bani hakuri ko ya aiko min da sako ba? Ni I don't think Talba yana so Madinaâ€

“Yana son ki mana Leilaâ€

Madina ta fada sannan ta sauka saman gadon ta kama hannun Leila.

“Zo nan let me show you somethingâ€

Gaban madaubin dakin ta nufa da ita ta tsayar da ita gaban madubin.

“Kalli kanki da kyau Leila ki fada min abun da kika rasaâ€

Leila ta kurawa kanta ido a madabin tana kallon irin baiwar da Allah yai mata ta kyau daidai gwargwadon.

“Kyau?â€

Madina ta tambaya sai Leila ta girgiza kai.

“Kudi? Lafiya? Kima, gata ko kuma me?â€

“Ba ko dayaâ€

Leila ta amsa.

“Kina da kyau da babu namijin da zaki yi tayin kanki ya ce miki aa ko waye shi kuwa, mahaifinki na da arziki da zai iya siya miki rai idan ana saidawa Leila, kina da kima, ga gata ta ko'ina, kuma duk wannan tarin baiwar da take tare da ke sai zuciyarki ta raya miki Talba baya son ki?â€

Leila ta juyo tana kallon Madina

“Za ki iya fada min dalilin da ya saka yake min haka?â€

Madina ta yi murmushi ta koma saman gadon ta zauna.
Chapter 8 · 0% Book details