← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya da sauri ya fita zuwa bangarensa domin a can ya baro wayarsa, yana shiga ya koma dakin karatunsa ya dauki wayar ya kira Momy, ringing tai sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga.

“Momy kuna ina?â€

“Gamu hanyar dawowa gidaâ€

“Ina Baaba?â€

Dan Jimm Momy tai kamin ta amsa masa.

“Yaranta sun zo sun dauketa, sun tafi da ita, daman ciwon ba sosai ba neâ€

“Amman...â€

Be karasa ya lumshe idonsa sosai jin Momy ta katse wayar, hakan nan jikinsa ya ba shi kamar ba iya haka ba ne. Idan har ba babban abu ba ne, babu yadda za ayi Momy ta kaita asibiti da kanta, kuma har Leila ta bi ta su tafi tare.

AMINATU POV.

Tun safe take ta wanke tufafin Baba da nata har kusan daya da tabi, abun ka da marar aiki da kuzari, bata da kuiyar aiki kam amman bata da sauri, sai wuni ta kwana tana abu daya.
Bayan ta wanke su fes ta matse ya daurewa ta soma sha shayawa, sannan ta bi tana kwashe wadanda ta shanya da farko suka bushe tana ninkewa, sai ta dora akai da haka har ta gama kwashe ta kai su daki, sannan ta fito ta shanya sauran. Ta dauke kayan da tai aikin da su cike da gajiya ta aje a inda suka saba ajewa.

“Inna tashi ki yi sallahâ€

Ta fada tana doso dakin, har zata shiga sai kuma ta juya ta dauki butar Inna ta cika da ruwa sannan ta nufo dakin, bata sake ce ma Inna komai ba har sai da jera tufafin Baba a inda ta saba saka masa sannan ta nufo inda Inna take zaune ta sadda kai kasa ta.

“Inna...â€

Jin bata amsa ba yasa ta risina a hankali ta leketa, sai ta ga idonta a rufe, da sauri ta taba ta abunka da wanda yai nisan bachi sai ta zabura da karfi ta bude ido, da wanin irin karfi Aminatu ta hade yawu ta sauke ajiyar zuciya.

“Inna anyi sallah, yi hakuri na tashe ki da karfi tsoro na ke jiâ€

Sai Inna tai mata murmushi, sannan ta fara yunkurin tashi Aminatu ta kama ta ta mike tsaye, da taimakon Auta ta fito waje ta shiga bandakin, bayan ta fito ta rika mata butar tai alwala, sannan shimfida mata tabarma da abun sallah ta dauko mata hijabi.

“Allah ya miki albarkaâ€

“Aminâ€

Ta amsa tana kokarin rikata ta zaunar da ita, domin a zaune take sallah, saboda bata iya dadewa a tsaye. Sai da Inna ta fara sallah sannan ta dauki butar ta shiga bandaki bayan ta fito tai alwala ta zo kusa da Inna ta yi sallah, babu komai a cikin addu'ar sai nemawa Inna lafiya, domin shi ne abun da yafi komai tsaya mata a rai a yanzu.

Kamar kullum bayan ta gama ta dora girki, sannan ta matsawa Inna furarta ta jiya ta bata. Baba be shigo ba sai bayan sallah isha'i.

“Sannu da zuwa Babaâ€

“Yauwaâ€

Ya amsa yana sauke gajiya, kamar wanda ya wuni yana aiki, daman can haka yake tun da tsufa ya kama dan abu kadan sai gajiya ta tarar masa. Aminatu ta tashi da sauri ta dauko masa abinci da ruwa ta aje masa.

“Allah ya miki albarkaâ€

“Amin Babaâ€

Ta amsa tana jindadi albarka da suke yawan saka mata, ta san ko ba yau ba wata rana albarka nan zata bita.

“Baba na wanke kayanka fes na ninke makaâ€

“Eyeee Auta gayyar aiki, Allah kara miki albarka yar Babaâ€

“Aminâ€

Ta amsa tana murmushin data manta rabon da ya ziyarci kumatunta, Inna ma murmushin take tana kai hannu ta rage hasken fitilar dake kusa da ita.

“Yau da wuri za'ayi bachi ko? Dan a san akwai gajiyaâ€

Cewar Inna tana kallon Aminatu, fuskarsa sai haske take duk da kasancewar dare ne, sai dai dan hasken farin wata daya haska ta da kuma fitilar dake kusa da ita yasa duk wanda ya kalleta zai yi arba da yadda fuskarta take ta haiba.

“Jikina yau Alhamdulillah ji nake kamar ba ni baâ€

Baba yayi murmushi yana kallon Aminatu wanda ita ma murmushin take.

“Ai na ga alama ga annuri nan a fuskarkiâ€

Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana amsa sallamar da Isah yai, kusa da Baba ya zauna sannan ya aje mata ledar yalo a gabanta.

“Ga tsarabar kasuwaâ€

“Allah ya maka albarkaâ€

“Aminâ€

Ya fada kamin ya dora da amsa tambayar da Baba yake masa.

“Wallahi kasuwa Baba taki ta koma kamar da, kowa a tsorace yake, saboda ana ganin mutanen nan kamar za su iya dawowa, kasan idan suka saka gari agaba sai sun ga bayansa, musamman garin da da suke da dade suna dafafe, tun da ba a taba shigo mana ba sai yanzu, gashi daman yan saka kai na yankin nan sun sha kashe mutane suna da haushin garin nan sosaiâ€

“Allah dai ya tsare, abun da Bashiru yake ta ce min kenan kullum, ga shi tsohuwar ta ku ta ki yarda mu bar nanâ€

Cewar Baba.

“Ku bar ni na mutu inda uwaye na da kakanina suka mutu, ai ba a tsirewa mutuwaâ€

“Amman inna idan mu ka bar garin nan ke kanki hankalinki zai fi kwanciya fiye da nanâ€

Amina ta fada, a karon farko kenan da ta saka bakinta a maganar. Sai Inna ta girgiza kai.

“Babu inda zanje, kina ganina ko tafiya bana iyawa miya rage min Allah na tubaâ€

“Mai ciwo da mai lafiya, duk daya ne a gurin Allah, sai kaga mutuwar ta dauke mai lafiya ta bar mai ciwo aiâ€

Ta daga ma Baba hannu.

“Dan Allah ku daina min maganar nan, ni ban hana ku tafiya ba, amman ni kam ba zan bar garin nan baâ€

“Allah ya kyautaâ€

Duk suka amsa da Amin har ita. Ko da goma tai duk sun kwanta Inna da Aminatu suna daki, Isah da Baba kuma suna waje saboda garin akwai alamun hadari hakan yasa zafi ya tsananta, sai dai hakan be saka Inna fitowa ta kwanta waje, Aminatu kuma duk inda Inna take tana nan. Kowa yayi bachi ban da Aminatu dake ta tunanin abubuwa da dama ciki har da wasikar ta ta karshe da ta bawa Maniru shi ma ya bata, babu yadda be yi ba akan yana son tai masa iso gurin iyayenta ta hana shi saboda tana jin tsoro, ashe ba rabon gaisuwa da shiga tsakaninsa da iyayenta. Sai a yanzu take jin zafin mutuwarsa, kuma take ganin laifin kanta na hana shi ganin Babanta da tai. Ba shiri tai firgigit ta tashi zaune sakamakon kara bindigar da taji, a da can yan saka na yanki su kan harba bindiga idan dare yai, shi ma kuma ba kullum ba, sai dai tun bayan harin da aka kawo musu aka kashe wasu wasu suka tarwatse sai aka daina harbawar, ba ta hadda karar wacan bindigar da kuma ta yan ta'adda ba, balle ta iya banbanci ta su da kuma ta yan sa kai, sai dai yanayin yadda take ta jin tashin bindigar babu kakkautawa yasa hankalinta ya tashi sosai.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'unâ€

Daga waje ta ji muryar Baba yana neman agajin Allah. Kamin su soma jiyo hayaniyar mutane da alama gudu tsiratar da rai suke, Baba ya shiga dakin da sauri ya haske fitilarsa ya bude inda yake ajiyar kudi ya kwashe su ya saka aljihu.

“Aminatu rikata tashi mu tafi yan ta'adda neâ€

Kamar an zare mata lakka haka Inna ta ji, sai jikinta ya kara nauyi, Aminatu ta shiga kokarin rikata da sauri amman ta kasa.

“Tu tafi Malam, ku gudu ko dan saboda Aminatuâ€

Aminatu ta girgiza mata kai da sauri tana kuka.

“Ba zan tafi na barki ba Inna...â€

Ta shiga kama Inna da dukan karfinta tana jin kamar ace tana da karfin da sata iya daukarta ta dora akai, sai gashi tsaye ma ta kasa mikar da ita sai da Baba ta rika mata dayan bangaren, sun mikewa tsaye suka ji harbin kamar a bayan dakinsu, wani kuma a cikin gidansu.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'unâ€

Baba ya fada yana sako fitsari a wando sai kuma ya fara rawa yana tsalle kamar wanda ya tabu.

“Allah ka batar da ni, Allah ka batar da ni kar su gan niâ€

A take cikinsa ya murda sai zawo, abun ka da mai tsoro sai yai cikin tufafinsa na sakawa ya tura kansa sauran jikin a waje, ga wandonsa sharkat da zawo da fitsari. Inna kam gaba daya hankalinta yana gurin Aminatu. Da hannu ta nunawa Aminatu karkashin gadon karfi alamar ta shiga domin bata ko ina magana. Da gudu Aminatu ta nufi karkashin gadon kamin ta karasa shigewa suka shigo dakin rike da magayen makamai, ga wata uwar fitila mai dan karen haske da suke haska ko'ina da ita kamar gulub. Dayan ya turo Isah cikin dakin da karfi, sannan ya karasa karkashin gado ya daga daga katifar ya jefar can gefe, sai ga Aminatu dunkule.

“Fito ko na halbe kiâ€

Dayan ya fada, da Aminatu ake sai dai tsabar tsoro yasa Baba ya ji kamar da shi ake, sai ya cire kansa cikin jakar kayan ya rarafo kusa da Isah yana ta kuka da karanta addur'ar da ta zo masa.

“Yanarukuna bardan wassalamu ala ibrahimâ€

Daga nan ya dora ta ayatul kursiyu, kamin su daka masa tsawa ya kama bakin ya rike jikinsa ta ko'ina rawa yake. Wani irin rawa jikin Aminatu yake tana ganin komai kamar ba gaske ba, yadda take fita da shigar da numfashinta kadai ya isa ya bayyana irin tsoron da take ji.

“Dan Allah karku taba ta, ku kashe ni ita ku kyale taâ€

Inna ta fada, sai dayan ya saka bakin bindigarsa ya buga mata a kai, take gurin ya fara zubar da jini.

“A kyale ta ita tafi sauran yaya ne? Kuna son ta kuka ja mata masifa ba kuri kuke ku kuna da jarumai a gari ba? Yayanka sai kashe mu suke duk inda suka ga bahillace sai ku kashe shi, Wallahi yau ko wa ba mu bari garin nanâ€
Chapter 16 · 0% Book details