Sashe 15
Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna ta fada tana kokarin gyara zamanta, domin a zaune take sallah a yanzu. Aminatu ta kalleta kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta amsa.
“Ameenâ€
Ta mike tsaye.
“Bari naje na yi itace yamma ta yiâ€
Kai kawai Inna ta daga mata, ita kuma ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka ta ta dauki zaren da take daure itacen idan ta yi, sannan ta saka talkaminta ta fice, ba ita kadai ba kusan duk yan matan garin da ma matan aure suna zuwa daji ne su yi kara da yamma saboda dafa abinci, abu ne mai wahala ka ga gidan da ake siyen itace a yanki, yawanci duk a daji suke yin kara.
A da ta saba idan zata tafi yin kara akan biyo mata ko kuma ita ta biyawa wasu, sai dai tun bayan da aka tarwatsa rabin garin take tafiya ita kadai, saboda an tafi da wasu yan mata, wasu kuma sun yi gudun hijira, sauran da suka rage kadan ne. A gurin da ta saba tsayawa ta tsaya ta shimfida zanen sannan ta aje zaren a gefe, kana ta shiga tsintar karan, tana yi tana tuna yadda suke yi a da, ita da kawayenta, har tigengen suke cikin nishadi da walwala, sabanin yanzu da suka bar ta da kewa.
Sai da tai rabin sannan ta samu kanta da mugun faduwar gaba, marar misaltuwa, a take ta nade wanda ta tara a daure ta dauka ta nufo gida da gudunta, kowa sai kallonta yake, kamin ta iso har hawaye ya fara sauko mata, bakin kofa ta jefar da karan ta rugo da gudun gurin Inna da ke kwance tana bachi ta taba ta.
“Inna...Inna.... Innâ€
Bata karasa ba, Inna ta bude idonta da sauri tana kallonta.
“Lafiya Auta?â€
Sai ta fashe da kuka, wanda hakan yasa Inna ta tashi zaune.
“Tsoro nake ji Inna, gabana faduwa yakeâ€
“Tsoron me? Miya faru?â€
“Ban san ni ba, bana son na yi nisa da keâ€
“Auta kenan, kin isa ki tare min mutuwa ne? Da wani na tarewa wani mutuwa ai da na tarewa Yayana, kin san babu uwar da za a kashewa yaya a gabanta kuma ta kyale alhalin tana da ikon yin wani abu?â€
Maganar da Inna tai ya isa ya tabbatar da cewar ta fi jin bakincikin kashe mata yaya da akai fiye da keta mata haddi da aka yi. Aminatu ta yi kasa da kanta tana kuka sosai.
“Kina kuka da wuri, ki adana kukanki saboda gabaâ€
Ta kalleta.
“Miyasa kike min fatan kuka Inna?â€
“Saboda zaki yi kuka mai yawa Aminatu, dole zaki yi kuka, ranar da zaki bude ido babu ni, ranar da zaki ga wata uwar idan kika tuna da taki dole ki yi kuka, ranar da kika ga wasu yan'uwa kika tuna da naki dole ki yi kuka, ranar da kika nemi wani abu kika rasa dole ki yi kuka, ni na riga na gama tawa rayuwar har na yi jikoki kuma na yi Auta, ke kuma yanzu rayuwarki take kan ginuwa, ta fara miki a haka, me kika tsammani a gaba? Dadi? Dadin yana tafe bayan wuya amman, yanzu na fi tausayin rayuwarki fiye da ta kowa Aminatuâ€
Ta share hawayenta, ta kara matsawa kusa da Inna ta kwanta jikinta, ta lumshe ido, tana maida numfashi a hankali.
“Allah ga yata, Allah ka zame mata gataâ€
Inna ta fada a ranta hawaye na sauko mata, ba tana kalamai ba ne domin ta daga mata hankali, a a har ga Allah tana fadin abun da take jin ya kusa tabbatuwa a gareta ne, kuma tana jin nata mai kiran ya kusa kiranta, jikinta da mafarkanta suna bata haka, domin tana jin wani kalar yanayi na dabam a jikinta wanda bata taba jin irinsa ba, sai dai a kusa? Ko a nesa? Yau ko anjima? Shi ne abun da bata da tabbaci.
Bayan sallah Magariba, Baba da Isah suna daki sun saka Inna a gaba suna ta kokarin convinced din Inna akan ta amince da magabar Bashiru su ma su yi hijira su bar garin amman ta ki, Aminatu kam tana zaune waje sai kallon hadarin dake haduwa take, ita kanta bata san na yi ba, tafiyar ko zaman? Inna tana da gaskiya idan sun tafi ba za su tserewa mutuwa ba, sai dai barin garin zai taimaka Inna ta manta wata damuwar, domin a cikin abubuwan da suke bata mata rai har da zaman gidan da take ganin an kashe yayanta kuma tana ganin a kowa ne dare kamar za su shigo ne su yi mata sallama kamar yadda suka saba, yadda rayuwa take a baya.
Sai da akai kiran sallah isha'i sannan Baba da Isah suka fito waje, sukai alwala suka yi haramar zuwa masallacin.
TALBA POV.
Ya kusan minti ashirin a cikin motar sannan ta fito, kamin ta bude motar ta shiga ma wani aiki ne, ba karamin kufula shi tai ba, domin ya tsani jira ya tsani a bata matsa lokaci.
Sai dai ko kadan be nuna mata ransa ya bace ba, ya ja motar suka fita fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Mai gadin be yarda ya tsaya jiran sai Talba ya danna horn sannan ya bude masa ba, tun a lokacin da ya ga ya shiga motar yai hanzari bude gate din ya tsaya, be bar gurin ba har sai da motar Talba ta fice daga gidan.
Be kalli inda take ba, tukinsa kawai yake yana sauraren fm din dake gabatar da wani program, sai dai ita lokaci zuwa lokaci tana satar kallonsa, duk kuwa da kasancewar bata son su hada ido gudun kar ya ga tana kallonsa.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin titi, ya zata yi ta canja Talba? Shine tambayar da ta zo mata a rai, gata a mota daya da shi amman baya nuna mata wata alamar kauna, Baya ma son kallon inda take kamar ba masoyinta ba.
“Na fasa zuwa shopping din take me homeâ€
Sai a lokacin ya kalleta tare da kiran sunanta.
“Leila...â€
Ta kalleshi Irin duban nan na fusata, sai dai kwarjininsa ya hanata nuna masa fushinta.
“I'm not your driver, and this should be the last time da zaki umarce akan wani abuâ€
“Amman ni dazun ka cilasta ni na bawa Baaba hakuri bayan kuma bata cancanci haka baâ€
Ta fada idonta na cika da kwalla.
“Me ka dauke ni ne Talba? Baiwa?â€
Be amsa ta ba, ya juya motar zuwa gida, kamin su isa hawaye da ya wanke mata fuska ya fi a kirga, yana yin farkin ta bude motar ta fita tana share hawayenta. Sai a lokacin ya juyo da fuskarsa yana kallonta har ta danna door bell din aka bude mata ta shige, sannan ya maida dubansa gurin Daddy dake tsaye jikin motarsa yana magana da Momy da gaba daya hankalinsu yake kan Talba.
Bude motar yai ya fito ya rufe ya nufi gurin da Daddy yake tsaye yana wata irin tafiya kamar baya son taka kasa, kamin ya karasa ya zuba hannayensa aljihu kana ya sadda kansa kasa.
“Ranka ya dade baka burge ni ba, da baka tura Leila gida gurin Gwaggo baâ€
Daddy ya fada yana kallon dansa, sai Talba ya kalli Daddy, kamin ya maida dubansa gurin Momy wanda hakan kr tabbatar masa da cewar Momy ta fadawa Daddy abun da yai ma Leila kenan.
“Momy ba zamu iya yin abu a tsakaninmu ba har sai Daddy ya ji?â€
“Yes, ya kamata ya ji ne, saboda kana kokarin wuce guriâ€
“Just because...â€
“It's just because? Tun ba yau ba Talba kana treating Leila kamar ba yar gidan nan ba, ya kamata ka sani ita ma tana da right fa!â€
“Miyasa karamin Abu zai bata miki rai Momy?â€
“Kai kaja komai, wacan yar aikin ma dana kora saboda kai na koreta Talba, saboda kana nuna kamar ta fi Leila gata a gidan nan, and now kana son na kori Baaba ko? Ka cigabaâ€
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar da zata sadata da bangarenta, daga Daddy har Talba kallonta suke har ta shige, sannan Daddy Talba ya ce.
“Ka saba da halin Momy ka ba tun yau ba, kar hakan ya dame kaâ€
Talba yayi murmushi.
“Daddy fita zaka yi?â€
“Yeah zan je gaisuwar Galadima neâ€
“Lemme drive youâ€
“No tare da direba zamu je, go and restâ€
Murmushi ya sake yi ya dan ja baya, ya budewa Daddy motar sai Daddy ya shiga yana fadin.
“Ance an kai hari Galadi, ya kamata A shirya wani abu a kai musu, mutanen nan suna cikin matsiâ€
“Inshallah Daddy, ban ji ba two days ban duba news baâ€
“Sai na dawoâ€
“Allah ya kiyayeâ€
Ya fada yana rufe masa motar, sannan yaja ya tsaya har sai da driver ya ja motar Daddy suka fice daga gidan. Sannan ya nufi bangarensa, daga shi har Faruq da part dinsa yake kusa da nasa a kasa dakunansu suke, tsabanin bangaren Daddy da Momy da akai yi ma upstairs.
Dakin da yake aje tardunsa ya nufa ya bude ya shiga cikin natsuwa ya zauna a kujera ya bude system dinsa ya cigaba da wani aikin da be karasa ba, be bar dakin ba sai kusan 6pm.
Freezer ya nufa ya bude ya dauko ruwa ya zuba a cup ya surka da wasu sannan ya sha, bayan ya ajr cup din ya nufo kofar fita yana duba agogon hannunsa. Kai tsaye bangaren Momy ya nufa domin ya san izuwa yanzu ta huce fushin da take. Door bell din ya danna, yana dauke hannunsa Amal ta bude masa da sauri hawaye na sauko mata.
“Lil Sis?â€
“Na'am?â€
“Me ya same ki?â€
Ya tambaya a yayinda ya saka kafarsa cikin falon yana dubanta.
“Baaba ce...â€
Sai kuma tai shiru, shi dai kallonta kawai yake, as she knows ba zai sake tambayarta ba sai ta soma labarta.
“Tana mopping sai ruwa ya zame ta ta fado...â€
Wani irin kallo tsoro yai mata.
“Ta fado ina?â€
“Daga sama ta fado kasa!â€
“You're kidding meâ€
“No Wallahi da gaske nakeâ€
“Ina take? Ta ji ciwo?â€
“Momy ta dauke ta sun tafi asibiti tare da Ya Leila tun dazu ba su dawo baâ€
“Yaushe abun ya faru?â€
“Lokacin da Daddy ya fitaâ€