Sashe 19
Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Saukowa tai da kafafuwanta a kasa, tana kara share hawayenta. Momy har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleta.
“And for the very last time, zan sake tambayarki kina son Talba?â€
Leila ta daga kai.
“Wallahi ina son sa sosai Momy, ina son shi, miyasa kika tambaye ni?â€
“Ba komai, ki kwantar da hankalinkiâ€
Leila ta daga kai alamar gamsuwa, sannan Momy ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. A hankali ta tura kofar dakinta ta shiga kai tsaye ta nufi gadonta ta sauke jakarta da mayafinta akai sannan ta zauna tana sauke dogon numfashi.
“Allah ka yafe mana...â€
Ya furta tana lumshe ido, sai kuma ta busar da iskar bakinta.
FARUQ POV.
“Ina son anjima zan tafi kasuwaâ€
Ya juyo ya kalleta yana kokarin saka agogon hannunsa.
“Gurin me?â€
“Tufafi zan siyo, kuma zan siyawa Sultan maâ€
“Karki je ko'ina, kuma karki siyawa dana komai da kudin da ban san inda suka fito baâ€
Yana gama fadar hakan ya saka talkaminsa ya fice daga gidan gaba daya. Wani dogon tsaki ta ja ta murguda masa baki.
“Wallahi sai na je, wato bayan talauci har da hassada tana damun talakaâ€
Ta fadi zaune saman kujera rike da wayarta tana tabe baki, Data ta kunna ta shiga facebook, sai da ta fara duba notifications dinta, ta shiga comments tana duba yadda maza ke yaba surarta kowa da yadda yake yaba sabon hoton da ta dora, murmushi take tana ta bin comments dinsu da like har cikin zuciyarta take jindadin yadda suke yabonta. Bata da fargabar komai domin ta yi blocking din Faruq da duk wani dan'uwanta na kusa da ta san zai iya ce mata ta gyara ko ta daina, daga familyn Faruq har nata yan'uwan. Bayan ta gama karanta comments din ta leka inbox dinta, sakonni ta tarar da yawa cikin har da bakin fuskar da basu saba mata magana ba, kamin ta yi ma mutun reply sai ta duba profile dinsa ta duba abokansa aikinsa hotunansa da kuma inda yake zaune, da zarar ta ga alamar mai rufin asiri ne sai ta sake masa idan kuma ta ga sabanin haka sai ta yi blocking dinsa a take.
“Ibrahimâ€
Ta furta sunan dake profile dinsa sai kuma ta shiga duba hotunansa, da inda yake aiki kana ganinsa kasan mai abun hannun ne. Komawa tai inbox din ta amsa masa da thanks akan yaba kyauta da yai. Kasancewar yana online a take ya maido mata da amsa.
“Babu godiya a tsakaninmu, wani ma yai rawa balle dan makadiâ€
“Uhmm haka kaceâ€
“Haka ma yake, wani ya bawa mana matarmu balle kuma niâ€
Ba shiri ta zaro ido gabanta ya fadi.
“Ya san ni kenan, ko kuma dai wasa ceâ€
Ta fada tana tashi tsaye.
“Matarku kuma?â€
Ta tambaya domin tantancewa.
“Eh mana ba matar Faruq ba ce Rafi'ah?â€
“Ka san Faruq ne?â€
“Sosai ma tare muka yi makaranta da shiâ€
Ta kara zaro ido.
“Na shiga ukuâ€
“Gaskiya abokinmu yayi dacen mata, kina da kyauâ€
Ya rubuto mata, sai ta koma ta zauna tana kokarin kwantar da hankalinta.
“Da alama shi ma shegen neâ€
‘Allah sarki, ashe kun yi karatu tare’
Ta amsa masa.
‘Eh sosai ma, na zo har aurensa ai, kuma ko lokacin da kika haihu na so na zo ban samu dama ba, ya Babyn?’
‘Lafiya Kalau, ya naka iyalin?’
‘Ni kam da saura har yanzu ban yi aure ba, sai na samu mai kyau irinki’
‘Hmmm kana koda kyau na kamar gaske’
‘Da gaske ne mana, Faruq be taba fada miki kina da kyau ba’
‘Uhmmm’
Shine reply din da tai masa sannan ta kashe data ta aje wayar, ta nufi inda Sultan yake yana bachi ta tashe shi ta bashi ragowar kazar jiya ita ma ta ci ta koshi sannan ta shirya masa ita ma ta shirya ta dauki jakarta da mayafi ta riko hannun Sultan suka fito daga cikin gidan, sai da ta kulle gidan sannan ta nufi makontansu ta bada ajiyar Sultan ita kuma ta kama hanyar titi, ba yau ta saba satar hanya ta fita ba, wani lokacin idan ta tambaya ya yana ta ma fita take wani sa'in kuma bata ma tambayarsa, gashi idan ya fita baya dawowa sai dare, inda ba wani abun ya bijiro ba. Ko ma ya dawo ya tarar bata nan sai dai yayi hakuri ya danne abun a zuciyarsa.
“Malam tsohuwar kasuwaâ€
Ta fada bayan ta tsaya da mai adaidaita, kai kawai ya daga mata, sam bata lura da kofatun dake kafunsa ba ta shiga, sai da ta gyara mayafinta da face mask din dake fuskarsa sannan ta aje jakarta gefe. Kamar ance duba ki gani tana kallon bayan kansa sai ta ga kan kamar na tsuntsu har wani rawa yake kamar zai fado ga bayansa duk gashi kamar dabba.
“Malam tsaya na fasa zuwa...â€
Ta fada da sauri tana runtse ido, sai mai Napep din ya faka gefen titi, tsabar tsoro yasa bata tsaya daukar jakarta ba ta fita da sauri tana haki, tana fita mai Napep din ya cigaba da tukinsa kamin ta rufe ido ta bude har ya bacewa ganinta, baya tai da sauri tana kara zari ido.
“Innalillahiâ€
Bata karasaba ta ji kamar ta taki abu, sai ta juya da sauri ta kalli Mahaukacin dake bayanta ya tara uban gashi ga tufafin jikinsa duk datti, wani irin tsalle ta daka ta ranta ana kare, wani irin gudun bala'i take mahaukacin na biye da ita shi ma da gudunsa. Wani shagon dake titi ta nufa kamin ta isa mutanen dake gurin suka watse da gudu domin sun san mahaukaci ba ya yi ma mutum da sauki, ita kanta bata taba sanin tana da gudu ba sai a yau, tana karya kwana ta samu wani gida ta shige ta turo kofar gidan da karfi ta rufe, tana ta haki kamar numfashinta zai fita. Mutanen gidan suka fito da sauri suna kallonta.
“Lafiya?â€
Sun tambaya domin kama tai musu da mahaukaciya, kanta babu dankwali balle mayafi ga kafafuwanta babu talkami sai uban datti da suka yi, gashin kanta ma dake fake har ya yamutse, gumi sai sauko mata yake.
“Mahaukaci ya biyo ni....â€
Ta fada daker tana haki, idonta har wani zurfin wahala sukai.
“Subhanallahi tsokanarsa kika yi?â€
Dayar ta tambaya tana kokarin gyara goyonta, kamin ta amsa mata suka ji aka dukan kofar da karfi.
“Zai iya balla mana kofa faâ€
Baturiya ya kauce jikin kofar da sauri ta dawo cikin mutanen tana kallon kofar.
“Ban tsokane shi kasuwa zan je sai mai Napep...â€
Bata karasa ba tai shiru tsabar fita da numfashinta yake da karfi.
“Wallahi haka yake, ranar fa tun daga rijiyar zaki ya dinga bin Marwa har unguwa ukuâ€
Baturiya ta kalli mai maganar, daman tun daga jin yanayin maganarsu ta ji ta banbanta data Zamfara, domin su kananci suke yi, gashi kuma an fadi rijiyar Zaki da unguwa Uku, wanda ta san ba a Zamfara unguwar take ba.
“Baiwar Allah nan kuma wani gari ne?â€
“Kano... â€
“Kano....?â€
Ta maimaita tana zaro ido, sai ta fadi a gurin zaune ta fashe da kuka.
________
Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe.
Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.
Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*
By Khadeeja Candy
Page -9ï¸âƒ£
If you're not living around these people, you will never know what they are going through, fiye da haka ma yana faruwa, kawai dai Allah ya tsare mu su kuma yai musu mafita.
Tun daga jin sunan Labarin kun san abun da ya kunsa. Ban san abun da readers suke so ba, idan an saka kudi da luxury life sai ace writers suna bude idon mutane, and when we're talking about reality kuma ba mu tsira ba, anyway if you don't like the story you can quit it.
         ***    ***    ***