← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 24

Sashe 1

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An dauko wannan littafi daga shafin www.hausanovels001.com.ng ku ziyarci shafin na www.hausanovels001.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348138892814

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.hausanovels001.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348138892814 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

*💔-BAKAR WASIKA-💔*
_Mai Farin rubutu_

From the writer of

RAI BIYU
HAFSATU MANGA
ZAGON KASA
ZABIN RAI
KHADIJATU
GOBENA
ZAKI
FULANI

©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠

SADAUKARWA.
Na Sadaukar da littafin nan ga Hajiya Habiba da iyalanta.

GAISUWA
Ga Mutanen Kirki, Rahma Kabir, da Mrs J Moon.

GABATARWA.

BAƘAR WASIƘA...
Mai farin rubutu

Idan aka ce Bakar Wasika Mai Farin Rubutu. Ana nufin wani dunkulelen sako mai wuyar fassara, kamar mutum mai nagarta sai wani mummunnan kaddara ta fada masa.

Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.
Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.
Ban ce babu farincikin ba.
Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.

Labarin Tafida, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal, Kabir da kuma Aminatu.
Labarin BAKAR WASIKA. Labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta...
Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk kuwa da na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!
A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?
Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?

Labarin BAKAR WASIKA kirkiraren labari ne kamar sauran labaraina, kun san dai ban saba baku kunya ba ko?😉 Wannan ma zai zo muku fiye da yadda kuke tsammaninsa inshallahu. Sai dai ba free ba ne na kudi ne, but ina da free pages daga 1-10 ga masu son jin dandanon labarin kamin biya.
Kamar yadda kuka sani bana editing labari so ku yi hakuri da duk abun da zaku gani.

P. O. V
Na nufin Point Of View.

                      Ø¨ÙØ³Ù’م٠ٱللَّٰه٠ٱلرَّحْمَٰن٠ٱلرَّحÙيمÙ

Page -1⃣

Matashiyar yarinya ce yar shekara goma sha-bakwai dauke da farantin giÉ—a tana tsaye jikin window makaranta tana leken daliban da ake yi wa darasi.
Yadda ta maida hankali tana sauraren darasin da ake wa dabiban sai ka rantse da Allah har da ita a cikin daliban. Ilmin zamani na daya daga cikin abubuwan da suke matukar burge Aminatu kuma shi ne kadai abun da ta rasa a yanzu, wanda ta riga ta maye gurbinsa da talla a halin yanzu, a izuwa yanzu ta tabbatar bata da muhalli a ilmin zamani, sai dai shi ilmin yana da muhallin a zuciyarta.

"Ba ni gidar goma"

Wata dalibar ta fada da kamar rada gudun kar malamin da yake musu darasin ya ji ta, a munafunci ta jefowa Aminatu wata tsohuwar naira goma, sannan ta maida hankalinta gurin Malamin.
Aminatu ta duka kasa ta sauke farantin dake hannunta sannan ta dauki naira goma din ta daga hijabinta ta saka naira goma din cikin hular dake kanta ta gyara hijabinta sannan ta dauki giÉ—ar ta mika mata, yarinyar ta karba da sauri ta boye.
A lokacin ne malamin ya hango Aminatu tana kallon allon da yake koya musu darasin, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake arba da yara na shigowa makarantar talla, wani lokacin har cikin ajijuwa suke zagayawa idan sun ga babu malamai a ciki.
Sai dai tsayawa a nasu ana daukar darasin karatu babu kamar Aminatu domin ko daliban makaranta basa nuna mata natsuwa da maida hankali sai dai su nuna mata iya rubutu da kuma fahimtar darasin yadda ya kamata domin su a kullum suna aji ne, ita kuma sai idan talla ta biyo da ita.

"Mtcheesss idan ba makarantun kauye ba ina ake wannan abun? Ace makaranta a bude har masu talla suna shigowa, ko wane aji babu ganbu (Kaure) balle har ma ace an zagaye mana makarantar"

Malamin ya fada cike da jin zafin yadda aka wofintar da abun da ya shafi ilmin boko a yanki.
Aminatu na jin haka sai ta duke kasa gabanta na faduwa, daman can yarinya ce mai gujewa fitina da tsoron bacin ran mutane. Dukuduku tai ta fice daga gurin cikin sanda ta koma can bakin kofar makarantar inda suke zama ita da sauran masu talla suna jiran a tashi yan makaranta fito siye siye.
Rayuwar Aminatu rayuwa ce da ta ginu da ilimin addinin da kuma talla, domin bayan noma da mahaifinta yake yi wanda shi ne mafi akasarin mutanen garin galadi suke yi, babu wani abu da aka doraga da shi a gidansu kamar tallar da take, da rana zata kai giÉ—a makarantar boko, dare kuma ayi mata tuwo, da safe kuma ta fita tallar koko, hakan yasa rabin rayuwarta ta kare a talla. Sai dai ko kadan bata da matsalar rayuwa ta ko'ina domin ita kadai ce mace da mahaifiyarta ta haifa bayan zaratan maza bakwai. Rayuwarta kusan haka rabin rayuwar yan matan garin take ba kowa ya ke damuwa da karatun boko kamar yadda suke damuwa da talla ba, domin talla tana ba su komai cikin har da kayan dakin da ake yi ma yan mata.
Garin Galadi wani yanki ne dake cikin karamar hukumar mulki ta shimkafi, gari ne mai cike da albarka manoma, kusan idan ka ambashi shimkafi kowa ya san gari ne na manoma garin mai cike da albarka da kuma mutanen kwarai. Karamar hukumar Shinkafi tana cikin jihar Zamfara, shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Hedikwatar karamar hukumar tana cikin garin Shinkafi kuma karamar hukumar na da iyaka da karamar hukumar Zurmi Maradun da wasu sassan jihar Sokoto da jamhuriyar Nijar.

Garuruwa da kauyukan da suka kunshi karamar hukumar Shinkafi sun hada da Miyasa, Shinkafi, Bwane, Tunga, Fidani, Tubali, da Faru. An kiyasta yawan al’ummar karamar hukumar Shinkafi ya kai 177,811 mazauna yankin da ‘yan kabilar Hausa da Fulani suka mamaye. Yaren Hausa dai ana magana ne da shi a karamar hukumar, addini Musulunci shi ne addininsu.
Karamar hukumar Shinkafi tana da fadin kasa kilomita murabba'i 674 kuma tana da matsakaicin zafin na digiri 34. Karamar hukumar tana da kogin Tafin Kaiwa da ke ratsa cikin yankinta yayin da matsakaicin saurin iska a yankin ya kai kilomita 11/h. Noma wani babban aiki ne na tattalin arziki da al’ummar karamar hukumar Shinkafi ke aiwatarwa.
Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da al'ummar karamar hukumar Shinkafi suka gudanar sun hada da farauta, kasuwanci, kiwon dabbobi, da ayyukan fata.

*** *** ***

Tana zaune a gurin har aka tashi yan makarantar masu siyen gid'ar suka siya, wanda tai saura sai ta dauki farantin ta dora akai ta nufi gida tare da kawar tafiyarta Rumaisa, suna tafe tana kirga kudin gidarta har suka kawo mararabar hanya (Hanyar da ta kasu hudu) a nan sukai sallama kowa ce ta nufi gidansu. Da sallama ta shiga gidan kamar yadda ta saba.

"Wa'alaikissalam yar Inna yar Albarka"

Inna ta fada tana juyowa ta kalleta fuskarta dauke da murmushi. Sanusi ya wara ido ya zubar da ruwan daya wanke tufafinsa.

"Mu da ba yan Inna ba a nuna mana bolar mu"
Chapter 1 · 0% Book details