← Book details Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 24

Sashe 5

Bakar Wasika Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi murmushin mai sauti kamar yadda ya bukata, sannan ta aje wayar, ta juya ta koma inda ta fito. Kamar yadda ta fito haka ta koma gidan da gudunta ba da damuwa da titi ko sauran motoci burinta dai ta aikawatar da abun da take so. Horn biyu tai kamin tai na uku Mai gadin ya bude mata gate ta shiga cikin gidan da mugun gudu ta faka motar a inda ranta ya so ta fito ta nufi kofar falon, door bell ta danna da karfi kamar zata balla shi sannan taja ta tsaya tana tsaki, shiru ba a bude ba har sai da ta sake danna door bell din sau biyu ta hada da knocking. Sannan Baaba ta bude mata.

“Wallahi tallahi kika sake barina a tsaye a waje ina knocking, abincin ki ya kare a gidan nan Baabaâ€

“Wanke wanke nake yi Leila shiyasaâ€

“Na dai fada mikiâ€

Ta fada cikin tsawa, ba dan Baaba ta yi saurin kaucewa ba da Leila tureta zata yi ta wuce. Baaba ta maida kofar ta rufe sannan ta juyo cikin falon cikin rashin jindadi zata koma Kitchen din sai ta ji muryar Momy dake tsaye stairs.

“Baaba a rika kula mun dauke ku aiki ne kawai saboda mu huta, a daina batawa yarana raiâ€

Baaba ta daga kai ta kalli Momy sannan ta daga mata kai cikin da ladabi.

“To Hajiya Inshallahu za a kiyayeâ€

Sannan ta sadda kanta kasa ta nufi kitchen din cikin rashin kuzari.

FARUQ POV.

Kallonta ya tsaya yi da dayan biyu kamin ya amsa gaisuwar da tai masa, domin ba kasafai take gaishe shi da safe ba sai idan tana son wani abun ko kuma ta lura aljihunsa da dan nauyi.

“Lafiya Kalau an tashi lafiya?â€

“Alhamdulillah, sai yunwa da nake ta ji tun jiyaâ€

“Toh Allah ya buda mana kofafin samuâ€

“Amin...â€

Ta amsa tana kallon Sultan dake motsawa alamar zai farka daga bachin da yake.

“Na ce wai ba zaka kira abokin nan naka ba, ka roki shi dan wani abu?â€

Ya girgiza mata alamar aa.

“Ba zan dauna kullum ina bin abokai ina rokonsu ba, bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abun da zai ci ba, kuma ni ma na yi karatun idan mu kai hakuri komai zai wuceâ€

“Matsalar kenan Faruk girman kai, kana da girman kai, yanzu haka zamu zauna mu wuni da yunwa gashi idan ka fita baka dawowa sai dare? Ga ni da ciki ga Sultan?â€

Yayi shiru yana jin yadda kansa yake sara masa saboda maganganun da Baturiya ta fara masa.

“Shiyasa na ce zubar da cikin nan zan yi na huta, kai ma ka huta domin na san ko ragon suna da wahala a samu a yanka masa wannan bakin talaucin da muke fama da shiâ€

Ta fada cikin kukanta na munafurci. Sai ya kalleta a raunane.

“Zubar da ciki ba zai kawo mana Mafita ba Rafi'a miyasa ba ki da tunani ne wai?â€

“To ni dai gaskiya yunwa nake ji, tun jiya fa ban ci komai ba, kuma anjima na nan ga Sultan maâ€

Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya mike tsaye ya fice daga dakin cike da damuwa. Binsa tai da harara.

“Ni dai Wallahi na gaji da wannan bakar rayuwa, Allah kadai ya san yadda masu kudi suke ji, su kwanta a mai kyau a ci abun da ake so, ni ko na kare a nan duk kyau naâ€

Ta fada tana mikewa tsaye tare da bin bayansa, sai da ta tabbatar ya fita sannan ta dawo ta dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta kamo number da tai saving jiya. Maryam Dahiru Sokoto ta aika mata kira, ringing tai har ta tsinke ba a daga ba ta sake kira nan ma ba a daga ba.

“Ka ji yan gayu sai ayi ta kira basa dagawa...â€

Whatsapp dinta ta bude ta shiga gurin numbers ta kamo number wanda ke dauki da hoton wani matashin da ba zai wuce sa'an mijinta hakimce cikin mota. Sai da ta gama kallon hoton sannan ta shiga aika masa sako.

‘Assalamu Alaikum, ranka ya dade fatar an tashi lafiya, ya aiki ya Madam da yara. Ranka ya dade sunana Fee'ah matar Faruq abokinka, na kira baka daga ba shiyasa na yanke shawarar turo maka sako. Wallahi muna ciki matsala, yau kusan kwana nan mu hudu ba mu girka komai ba, shi ma idan ya fita haka yake dawowa saboda shagon da aka bude sabon gurin ne cikin wata sabuwar unguwa ba kowa yake ta aski ba, yanzu haka Sultan kuka yake, ni kaina dauriya kawai nai saboda da na, Dan Allah ka taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ka, na duba na ga a cikin abokan Faruk babu mai tausayinsa da son taimaka masa irinka, na so Faruq yai maka magana da kansa amman yace nauyi yake ji, yanzu haka be san na dauki number ka ba, domin idan ya sani ina ciki matsala. Ka huta lafiya Allah kara rufa asiri’

A rarrabe ta tura sakon har tana gadawa da emoji din rokon da kuka. Sannan ta duba last seen dinsa tun jiya da dare, tana jin motsin turo kofar gidan tai saurin aje wayar ta kwanta kasa. Faruq ne ya shigo dakin rike da bakar leda har biyu a hannunsa. Ya aje mata dayar a gabanta ganin hakan yasa ta tashi zaune tana kallon 200 dari biyun da ya mika mata.

“Ina ka samo?â€

“Ke dai ka barâ€

“Dan girman Allah Faruq ka daina mana cin bashi kana kara mana kanskanci a unguwa kamar kan mu farau talauciâ€

“Ba bashi na ci ba wayata na bashi jinginaâ€

Bata ce komai ba ta karbi dari biyu kana ta bude ledar tana duba taliya da makaroni dake ciki sai maggi da mangyada.

“To wannan ledar fa?â€

“Mama zan kaiwaâ€

Yana fadar hakan ya juya ya kalli dansa dake sharar bachi sannan ya fice ba dan ranta ya so ba.

“Mu ba mu wadatu ba amman sai dauka ka kaiwa wasu, mtchhhhâ€

Ta karasa tana jan tsaki.

“Kuma Wallahi sai na zubar da cikin nan haka kawai zan zauna ga talauci ga wahala da kurciyata da kyaunaâ€

Ta fada tana mikewa tsaye ta dauki ledar taliyar ta fito waje domin sarrafawa. Kallo daya zaka masa ka karanci damuwarsa abubuwan duniya sun taru sun masa turr kamar ya zagi arziki kamar komai yake juye masa, gashi yayi degree amman aiki ya gagara duk inda yai applying shiru ba wani motsi. Da tunani kala kala mai achaba ya sauke shi unguwar Dallatu wato gidan mahaifiyarsa, sai ta ciro naira dari a mika masa sannan ya ratsa cikin gidanje har ya isa kofar gidan ya tura ya shiga da sallamarsa. Kanensu biyu mata da suke tsakar gidan suka amsa masa suna masa sannu da zuwa, bayan ya amsa musu ya nufi dakin Mahaifiyarsa ba karamin faduwa gabansa yai ba ganinta a kwance domin ba al'adarta bace yawan kwanciya musamman a irin wannan lokacin.

“Mama lafiya dai? Ko jikin ne?â€

“Da sauki ai Alhamdulillahâ€

Ta amsa masa tana murmushin karfin hali.

“Wani irin da sauki ga ki kwance? Kai Innalillahi Wa'inna illahirraji'unâ€

Jin furuncinsa yasa ta yunkura ta tashi zaune tana kallonsa.

“Ina Sultan?â€

Kasa amsawa yai sai kallon mahaifiyarsa yake, yana jin kamar ace yana arzikin da zai iya kaita Asibiti, domin ba yau ciwon ya fara ba.

“Mama ko dai maganar auren Aisha da akai ne jiya ya tada miki hankali? Idan ma fasa aurenta zai yi ai ba wani abu ba ne zata samu waniâ€

“Har aure nawa za'ayi ta fashi ne Faruq? Haka zamu ta zama ana fashin aure saboda talauci? Kuma yaran nan sai girma suke, sai gulma ake mana a unguwaâ€

Ta tambaya idonta tab da hawaye, Faruq yayi saurin kawarda nasa idon yana sauke ajiyar zuciya, domin kukan mahaifiyarsa na daga cikin abun da ya fi tsana a rayuwarsa.

________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
https://www.wattpad.com/story/283871769?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZCqcO2wXIv6pkkxIr3do4ng1%2BTHhzoVPTPFtpfDcb1ftHOVsldMflpG2lAwd5aYtrehJ12WEeerjWSVNDZunKAH9QpxhI0A%2BzJsYI6RrshbTOZsoLUXljeZDCPaDNtKr

*💔 BAKAR WASIKA 💔*

By Khadeeja Candy

Page -3ï¸âƒ£

Shigowar Daddy ne yasa Momy ta cire farin gilashin idonta tana murmushi.

“Ranka ya dade an fito?â€

Kusa da Amal ya zauna yana murmushi.

“Allah ya yardaâ€

Ya fada yana karewa katon falon kallo ganin Momy ce kawai sai Khadija da kuma Kabir, abun da ba kasafai yake gani ba, ya saba every weekend yana zuwa falon Momy ya zauna tare da ita da kuma yaransa, kowa ya fadi bukatarsa ayi hira a bawa juna shawara, ayi nishadi. Sometimes kuma shi zai kira su a bangarensa a tare a can.

“Daddy barka da wuniâ€

“Yauwa, Sonâ€

Ya amsawa yana yi ma kowa kallon tsanaki, ciki har da yar autarsa Amal da ta wani hade rai.

“Hajiya ya ga falon ku kadai? Ina sauran yarana suke?â€

Momy ta kalli Kabir dake kallonta sannan ta kalli Amal kamin tace komai Kabir ya tari numfashinta.

“Daddy yaranka biyu fushi suke da juna, kasan Angry Birds neâ€

Daddy ya kalli Momy.

“Since when?â€

Kabir zai sake magana Daddy ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, wanda hakan ke nuna kai tsaye Momy yake son ta amsa masa tambayarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya.

“Ni ma dazun nan na sani...â€

A tsanake ta labarta masa abun da ya faru ciki har da fadan da tai ma Leila.

“Amman baki fada min ba? Taya zaki bar Mu'az ya fita ba tare da yayi breakfast ba? And baki dama ki san a wane hali yake ba?â€
Chapter 5 · 0% Book details