← Book details Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 34

Sashe 23

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tanko na dariyar mugunta ya dauki Zainab ya ɗaura a kafada, ko kallon in da Rahila ta ke be yi ba bare ya lura da yanayin da ta shiga na sanadiyar zantukan da ya ke fada game da Zainab. Da sauri ta sha gaban sa, cikin bambami ta furta

"Me ka ke nufi Tanko? Ina fatan kalaman da ka ke akan tarewa da wannan kaɗon ba gaskiya ba ne, In kuwa da gaske ka ke wallahi ba ka isa ba! Ba ka isa ka tara da wata mace wacce ta ke ba halas din ka ba gaban idona na"

"In kuma na yi fa? Me za ka yi? Ku ji mu da shashasha! Jiki duk ya bushe ya jeme ki na tunanin zan ga jiki kamar na kado na bari? Sakarya kawai!"

Cike da bacin rai Tanko ya maida mata da martani yana mai cigaba da tafiya, ganin da gaske tafiya yayi da Zainab nan take wani turirin kishi ya yi gaba da ita, gaba ɗaya ta daina ganin gabanta, juyawa ta yi a guje, tana tafe kamar kububuwa, daga Tanko har yaran sa ba su lura da juyawar Rahila ba, halin su ya raja'a kan nasaban da su ka ci kan Shehu, ga kuma Kado an samu, idan Tanko be yi san zuciya ba kila su ma su sami raban su daga jikin ta.

Inda ake sharo Rahila ta koma a guje, ihu take ba ta ko iya tantance mai take fadi. Ganin yanda ta iso filin da ake sharo ɗin ne ya dawo da hankalin mutane gareta

"Me ya faru? Me aka yi?"

ƴan matasan da ke wajen su fadi a tare suna masu ɗaga sanduna da addunansu. Haka Kuma Muhammad Bello ya shiga raba idanu, nan ya ankare da rashin Usman da Zainab a filin.

"Tannn... ko! Kaaaaɗo!! Sheehu ruwa!!!"

Rahila ta ce muryarta na haɗewa. Nan wajen ta faɗi tana mai kuka cike da ƙunan zuciya, tana jin labarin kishi amma Sam ba ta san haka ya ke da raɗaɗi ba, ta san ko kusa ba za ta haɗa kanta da abu ba, ta san matukar Tanko ya lashi zumar kaɗo tabbas ba za ta sake ji ta kansa ba. Kuka ta ke yi mata na rarrashinta duk a tunaninsu su zainab ta ke tausayi.

Su Bello kuwa tare da sauran ƴan matasa har ma da wasu daga cikin manyan da su ke da saurin ƙarfin su, Rarraba kansu su ka yi cikin daji Allah suna neman zainab, wainda su ka iya ruwa a cikin su kuwa su ka far ma ruwan da Rahila ta ce an jefa shehu.

Wajen zaman Tanko aka fara zuwa nan su ka iske babu kowa a wajen, har tawagar su Bello za su juya su ka hangi wata sabuwar bukka can nesa ta gabas daga inda su ke, ba su yi ƙasa a guiwa ba su ka isa, mazan da su ka gani a tsaitsaiye riƙe da bindigogi ya sanya su yin turus, sai da su ka ƙaraso ne su ka ga ashe ba ma bukka ɗaya bane sun kai biyar.

Ɗaga bindigogin su ka yi suna mai sai ta su, dakatawa su ka yi da fari, amma tunawa da su ka yi Shehu ya sa an haɗa maganin bindiga sun sha kwanaki ya sanya su dosar bukkar ba tare da ko wace shakka ba.

Karar fitar harshashi ne ya sanya Zainab farfadowa daga suman da ta yi. Ta mai raba idanu cikin kokarin gano in da ta ke, idanun ta ya sauka kan Tanko, wanda ke tsaye kan ta ya na shirin afka mata kenan ya ji alamun isowar su Bello.

Cike da bakin cikin an katse masa abin da ya ci buri ya ja tsaki, ya dau bindigar sa a fusace ya na duban Zainab ya ce

"Ki gyara sosai kafin na dawo! Yau sai na more abin da na ke mafarki! Na tabbatar mi ki sai kin kasa takawa! Bari na gama da wancan karamin kwaron!"

Ficewar sa da manganganun sa ne ya sanya Zainab dawowa cikin hayyacin ta.

"Usman! Na shiga uku ni Zainab sun kashe min Usman!"

Cewar Zainab yayinda ta tashi tsaye cikin neman mafita, kuka ta ke wiwi daya na bin daya. Gani take duk abin da Tanko zai mata ba zai kankare rabin zunubi da ta aikata ba na cin amanar shehu. Karar harsashe da ke ta shi be sa ta tsora ta ba, sai ma kokarin tusa kai waje da ta yi, a tunanin ta in ma mutuwan ne gwara harsashi ya kashe ta da ta mutu hannun Tanko.

Duk yanda Tanko da yaran sa su ka so cin galaba kan su Muhammad Bello kasancewar su na da bindiga hakan gagara yayi saboda maganin bindigar da ke aiki jikin su, dama ma su iya magana sun ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, tuni su ka sami nasarar kwace bindigun yayin da su ka kwantar da su da dukar kawo wuka. Inda su Bello ke kururruwar daukar fansa, su Tanko ihun neman doki su ke, su na fadin

"Mun tuba ku yafe mu! Mun tuba!"

"Kar ku raga mu su! Kar ku tausaya mu su! Sun jefa min Usman a ruwa! Sun kashe min Usman!"

Cewar Zainab cike da tsana yayinda su Muhammad Bello su ka dada tsage dantse wajan jibgar su Tanko da gora, gaba daya su ka mu su jini da majina amma hakan be sa Zainab ta tausaya mu su ba, sai ma dada cewa ta ke a kara mu su. Ana cikin wannan halin ne daya daga cikin wanda su wanda su ka je kaiwa Usman ne ya cimma su ya na mai ihu

"An dauko Shehu! Muhammad Bello an dauko Shehu!"

Ya na fadin haka ya juya a guje. Zainab ce ta fara yin gaba cikin gudu gudu sauri sauri, yayin da Muhammad Bello ya ba da umarnin daure su Tanko a taho da su, shi ma ya bi bayan su Zainab.

Nan bakin ruwa su ka tadda an fito da Usman, ana kokarin fitar da ruwan da sha. Ganin Bello da Zainab tuni aka dara mu su hanya wasu da ga cikin jama'ar na fadin

"Allahu akbar ruwan Rugar Shehu ba ya ci Shehu ba! Shehu ikon Allah! Allahu akbar!"

A tsorace Zainab ke kallan Usman da ke kwance tamkar matacce yayinda Muhammad ya cigaba da matso cikin sa, sai da yayi hakan kusan sau uku sannan ruwa ya fito daga bakin Usman cikin karfi, hakan ya sa Usman tari ya na mai bude murfin idan sa cikin magagi, jama'a aka sa kabbara, haka kuma mu su ihu da sowa na yi. Cikin kankanin lokaci ya sake mayar da murfin idanun ya rufe. Cike da tashin hankali Zainab ke fadin

"Kar ku bari ya rufe idanun shi! Kar ku bari ya mutu ya bar ni! Na shiga uku na lalace!"

"Ba zai mutu ba, ki kwantar da hankalin ki"

Cewar Muhammad Bello yayin da ya cincibi Usman ya aza a kafada. Babu wanda be tausayawa Zainab ba ganin yanda ta ke cikin tashin hankali. Ta na biye da Muhammad Bello har su ka koma bukkar Shehu. Da kyar su Iyalle su ka ja ta gefe lokacin da mai magani ya ke duba Shehu. Allah ya so babu karaya, in aka dauke raunin da Tanko ya masa akai, sai kuma ciwon jiki sanadiyar dauri da dukan da aka masa.

Sai da ya tabbatar Usman ya farfado ya bashi magani sannan ya kara bari ya koma baccin azabar da ke daukar sa. Su Tanko kuwa cikin garkon Shanu Bello ya sa aka daure su, ba dan halin da Usman ke ciki ba da tuni ya gama da su.

Murna da farin cikin biki ya koma bakin ciki, Rugar Shehu ya koma tamkar ana makoki. Washagari da sassafe Rahila ta saci hanya ta gudu, babu wanda ya damu da tafiyar na ta saboda Zainab kadai ta san wainar da su ka toya.

Kwana uku Usman yayi sai dai a kwantar a tayar, duk wani abin da ya shafi karfi su Bello ke masa amma fa a kan idan Zainab, ta kasa ta tsare ita take jinyar sa dan kuwa gani ta ke idan har ta matsa Tanko zai iya shigowa ya karasawa mata shi. Haka shi ma Usman din tsakanin sa da Zainab sai ido. Kuka kuwa ta yi har ta gaji, tun su Iyalle su na ba ta baki, har su ka gaji su ka sa mata idanu.

Da yammaci Zainab zaune bakin bukka ta yi uban tagumi gaba daya duniyar ta mata zafi. Kamar daga sama ta ji muryar Usman ya na kwallawa Bello kira, fadi ya ke

"Muhamadu! Muhammadu! Muhammadu!"

A zabure Zainab ta tashi ta shige dakin. Ta tarar ya na yunkurin tashi tsaye ya hada zufa sosai. Zainab ta karasa gare shi da sauri da niyar taimaka ma sa. Yanda yayi saurin janye hannun shi sa'ad da ta kai hannun ta jikin sa, da kuma irin kallon da ya bi ta da shi ya sa Zainab ja da baya jiki sanyaye, yayinda Muhamadu Bello ya shigo cikin sassarfa. Ganin Usman na kokarin tsayawa ya karasa gare shi da sauri, ya taimaka masa ya tsaya ya na fadin

"Hankali Shehu, ya aka yi ki ka bari ya tashi Uwargida?"

"Ina Tanko? Ina Tanko na ce??"

Usman ya fada a fusace ya na mai raba idanu.

"Ya na can cikin shanu tare da yaran nan, dama jira mu ke ka sami sauki sai a san yanda za a yi da su"

Cewar Bello cikin shakkar yanayin bacin rai da ya lura Usman ke ciki.

"Ba na son ganin Tanko, wallahilazim ina iya kashe shi har lahira...."

Cewar Usman ya na mai danna kwayar idanun sa cikin na Zainab, wacce ta ke duban shi cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Usman be gushe ba ya kara da

"Idan akwai abin da na koya cikin rayuwa ta da wannan baiwar Allah (ya nuna ta dan yatsa) shi ne rashin faidar ramuwar gayya, domin kuwa yakan jefa dan Adam ga halaka, ku kai Tanko da duk wanda ya rabe shi ga hukuma dama sun jima suna neman shi"

"Toh Shehu"
Chapter 23 · 0% Book details