← Book details Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 34

Sashe 13

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta kai kallan ta ga Usman sam ba ta san da shigowar sa ba, tsaye ya ke jikin bango hannu sa harde a kirjin sa, yayinda hasken acibalbal ya haske fuskar sa, idanun sa har kyalli su ke tsabagen bacin ran da ya ke tattare da shi.

"Na'am?"

Ta mayar masa cikin rashin fahimta. Maimakon ya bata amsa, sai ya wuce ciki ya dauko wasu acibalbal har biyu, ya kunna haske sosai ya gauraya dakin, sannan ya dawo ya tsaya gaban ta, idanun sa cikin na ta ya furta

"Maza da ki ka fi so a rayuwar ki, akwai su ko? Na ga yanda ki ka kasa boye maitar ki sanadiyar ganin Tanko...."

"Tanko? Wanene Tanko?"

Zainab ta tambaya dan kuwa gaba daya kan ta ya juye ta kasa gane in da Usman ya dosa. Zainab na murmushi bayan ta gano bakin zaren ta ce

"Ya ba zan nuna maita ta ba bayan na ga namiji iya namiji? Ai wannan dajin kaf babu namiji da ya amsa sunan sa namiji kamar wannan....ya ma ka kira sunan sa?"
"Zainab!!!!"
Ya daka mata tsawa ya na mai kiran sunan ta na ainihi a karo na farko cike da gargadi, duk da hantar cikin Zainab ya kada ba ta fasa fadin
"Ga shi baki, ga faffadar ka fada....."
"Zainab!!!!!"
Ya kara daka mata tsawa tare da daga hannu kamar me shirin marin ta, har ta kai ga runtse idanu. Jin ba ta ji saukar marin ba ta bude idanun ta a hankali ta kai kallan ta gare shi. Idanun sa sun yi jajur sai huci ya ke
"Me ya sa ka fasa? Ka mare ni mana! Ka dake ni! Idan har ba ka daga hannu ka dake ni ba Usman ba ka isa namiji ba!"
Murmushin mugun ta ya sakar mata kana ya na mai ja da baya ya furta

"Idan har duka shi ne zai gwada mi ki isa ta namiji, Ni kuwa zan dake Abu, Amma duka mai dadi Abu ba irin wanda ki ke tunani ba, Irin wanda za ki dena maitar duk wani damiji face ni Usman..."

Ya na gama fadin haka ya fice da sauri dan kuwa yanda ya ke ji zai iya aikata abin da zai zo yayi dana sani.

*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2

7

Ta na mai nana ta maganar Usman cikin ran ta yanda ta ga rana haka ta ga dare, dan raban da ta sami ishesahen bacci tun ranar da aka wayi gari a Rugar Shehu.
Kamar yadda kowa ya kwanta da sanyi jikin zuwan su cangwai rugar da tsoron abin da Tanko zai iya aikatawa saboda korar da aka masa haka aka tashi washe gari, hakan bai hana mata dakan hura da zuwa tatsar nono asubahin fari ba. Bukkar da ke kusa da ta Atuwayye , matar taubashin Shehu ya sauke Rahila da Cangwai saboda aminta da yayi da ita sannan zaman da su ka yi a ƙasar Benue da mijinta lokacin da su ke ganiyar kaɗe shanu ya sanya ta ɗan fi sauran wayewa.
Duk wannan kai komon da ake yi da Rahila ake yi, sakin jiki tayi tana aiki tana lura da rugar sosai, cangwai kuwa tuni ta shige cikin yan mata sa'annin suna ta hidimar gaban su.
Ko da aka kammala girki, Raqiba aka kwalawa kira don ta kai ma Zainab nata.
"Iyalle barshi zan kai"

Rahila ta yi saurin faɗi don dama neman hanyar shiga sashin Shehu take.
"Ayi haka, tun safe kike aiki fa, Allah ya miki albarka" faɗin Iyalle ta na mamakin sauyin halin da ta gani a tattare da Rahila.

"Ba komi Inna, ai mu masu laifi ne, duk abin da zamu yi don mu rage nauyin zunubinmu za mu yi"

"Aikuwa dai Shehu na son debbo ma, ga ta Kaɗo maras daraja" .

Hansai ta caɓe tana mai taɓe baki

"Kinga ki iya bakin ki, ba da ni za a yi shari'a ba, in bai so ta ba wa zai so, da gani ai ka san yar birni ce"

Cewar Iyalle tana mai tashi daga wajen. Kalaman nan ne su ka ƙara sanya Rahila son zuwa ko don ta gane ma idon ta matar da kyau, gashi dai zuwan su jiya ta shaidi cewa yana kishin ta.
Da tunanin nan ne ta nufi hanyar sashin Shehu, da sallama ta shiga bukkar ba tare da ta jira an amsa ba duk da cewa zainab ba amsa sallamar su take ba.
Zaune ta iske ta ta baje kayan ta a saman gado tana ɗaga su, neman mai gwara gwaran da za ta sanya take yi kasancewar duk sun yi datti.
Buga wayar ta take a tafin hannun ta kamar hakan zan sanya ma batirin charji har ya kawo

"A ce mutum ya zama kurma a ƙungurmin dajin nan ta ina zai fara ga waya a kashe ba charji"
Tace tana mai jan tsaki daidai lokacin da Rahila ke kai bakin ƙofa za ta fice daga ɗakin. Jin haka ta juyo tana mai kallon hannun zainab, ko da ta shigo bata maida hankali ga hannun ta ba illa suturar da ta gani zube a gado musamman gajeren wandon zainab.

"Laaaaaaa!!! Wallahi irin abin da mai gidana ke magana da mutane in sun yi kinnafin, salla ko me ma sunan"

Tace tana ɓingere baki, duniya in akwai abin da ke birge ta yana bayan waya, don ta so Tanko ya bata ɗaya wata rana da ya shigo da su ya ce mata ai kudi ne maƙudai in ya siyar da su

"in sun yi mene? Ya aka yi ke kika iya hausa"

Zainab tace cikin firgici da farin ciki. Firgicin ambaton kidnapping da kuma farin cikin wacce ta ke jin hausa, hakan ya sa Rahila ankarewa da subul da bakan da ta yi, ta yi saurin gyara maganar ta hanyar fadin

"A'a wai in sun dawo daga wajen Sana'a na ke nufi..."

"Laaaa hausa ki ke min? Ki na jin hausa? Kin iya hausa?"

"Ai kusan rabin matan rugar nan in ba ma fiye da rabi ba suna jin hausa, Ce mi ki su ka yi ba da ji?"

Cewar Rahila ta na mai duban Zainab wacce alamar mamaki ya bayya na a fuskar ta, kafin bacin rai ya maye gurbin mamakin, murya kasa kasa ta ce

"Babu mahalukin da ya taba min, ko na mu su magana ba su nunawa sun gane bare su amsa, sai tsinannan dariya kamar mahaukata!"

"Hmmmm kadan daga cikin aikin Usman kenan!"

Cewar Rahila ta na mai jinjina kai na.

"Usman kuma, akan wani dalili"
zainab tace cikin ɓacin rai

"Zalunci! Ai babu azzalumi sama da Usman, Kinga da mahaifin Usman da na Tanko miji na uwa daya uba daya su ke, Amma Usman ya tunkude siriki na daga sarautar Rugar Shehu, haka kuma ya haye kujerat tare da haɗe dukiya gaba ɗaya, ya kada shanu kaf be bar mana ko daya ba ya tai dajin ga, ya bar mu ba cin yau bare na gobe, bakin cikin haka ya kar siriki na har lahira, dole ta sa mu ka bi sahun Rugar Shehu, gaban ki dai aka yi komai jiya....."
Ta kare maganar ta matsar kwalla. Cike da tausayawa Zainab ta furta

"Lalle ya cika azzalumi na gaske, tun da har ya iyayiwa jinin sa haka, ban yi mamakin abin da ya aikata gare ni ba......"

Nan ta kwashe komai ta fadawa Rahila, ta kare da

"Ni ban san yanda aka yi ba, zan dai tuna sanda na gama karatun jarabawar da zan zana, kawai sai wayar gari na yi na ganni kurgurmin daji hannun wannan azzalumin!"

"Surkulle kenan! Ai kiranye ya mi ki!"

Cewar Rahila ta na mai hango tarin dukiyar da Tanko zai samu ta sanadiyar Zainab, Dan kuwa kifi ne daga sama gashesahe, za su yi amfani da Zainab ta hanyoyi har biyu, na farko su kwaci Rugar Shehu ta hanyar hada baki da ita, Dan kuwa tun jiya ta gano Shehu na so da kishin Zainab, Zainab din ce dai ta kasa fahimta, haka kuma bayan sun kawar da Shehu su karbi kudi makudai na fansar Zainab, dan kuwa dai ba ta ga dalilin da zai sa Tanko ya ga Zainab ya mayar da ita salin alin hakan nan ba.

"ikon Allah, yanzu dai tun da na same ki baki munafunce ni ba kamar saura"
Maganar da ya dawo da Raliya daga wasikar jakin da ta fara. Jin Zainab na fadin

"ki min hanyar barin wajen nan ni kuma na miki alkawarin dukiya mai yawa sannan zan sa a kama azzalumin nan"
ya sanya Raliha murmusawa, kana ta bata amsa da
"In dai daga bangare na ne kar ki ji komai"

"Ni damuwata ma yanzu kaya na da duk suka yi datti, kazamai ne kaf dajin nan!"

Zainab tace ta na mai daga bumshort din ta biyu da su ka rage ma su tsafta.

"Laaaa wannan kamfai ne ko fatari?"

Yanda Rahila ta yi tambayar ne ya sanya Zainab dariya tare da fadin

"Bumshort sunan sa"

"Toh toh shi ma din a kasan tufa ake sawa ko? Kamar dai kamfe ko?"
"Ah ah, hakan nan din shi ake sawa, kuma kyau ya ke sosai, musammam in aka saka da yar riga kamar wannan..."
Ta yi maganar ta na mai daga shudiyar rigar ta, idanun Raliha har rawa ya ke tuni ta fara sakar zuci. Jin Zainab ta furta

"Ina ma birni na ke da na sa kin ga rayuwa, wannan dajin ma ina mutum zai saka...."

"Za ki iya mana!"

Rahila ta katse ta cikin farin ciki.

"Zan iya me?"

Zainab ta tambaya da zuciya daya.

"Sakawa, wannan hanya ce mafi sauki na tunzuru Usman, dan kuwa na lura ya na matukar kishin ki...."

"Mtswww kishin wa? Allah ya sauwake!"

Ta katse ta a fusace. Rahila na mai girgiza kai ta ce

"Na ce dai yanzun nan ki ka gama fadin na taimake ki ki bar dajin nan?"

Zainab ta girgiza kai alamar "eh"
Chapter 13 · 0% Book details