← Book details Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 34

Sashe 11

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Can birnin Kano kuwa tun washagarin tafiyar su Usman labari ya iski Ammy bayan ta bayar da abinci a kai masa. Ta yi mamakin dalilin tafiyar na sa ba sallama, amma ba ta kawo komai cikin ran ta ba. Hankalin ta be fara tashi ba har bayan da ta kira Zainab ba ta dauka ba, sai ma sakon txt da ta tura mata, ta yi tunanin rashin da'ar Zainab ne ya tashi kila Falmat ta sanar mata da zuwa Usman. Kiran ta da aka yi daga makaranta aka tabbatar mata da rashin ganin Zainab a dakin jarabawa ne ya tada hankalin Ammy, musammam da ta lissafa tafiyar Usman da kuma ranar karshe da aka ce an ga Zainab a makaranta, sai ga Ammy ta na kuka wiwi, haka ma Falmat wacce ita ce ta kira Anty Sauda ta fada mata halin da ake ciki. Sai da ta tabbatar mijin ta ya raba hotunan Zainab bariki bariki, check point na kowani hanya, haka kuma aka fara kokarin bincike ta hanyar kididdigar wayar salulun Zainab, sannan ta hawo jirgi ta tawo garin Kano.

Fada sosai ta rufe Ammy da shi fadi ta ke
"Kukan me ki ke Aleesha? Ba abinda ki ke so ba kenan? Kun cuci yarinya kun lalata mata rayuwa! Ga irin ta nan ai! Gashi na dai za ki yi biyu babu cifar gafiyar baidu! Shi mijin na ki dama babu shi, diyar ta ki ma Allah kadai ya san halin da ta ke ciki a raye ko a mace!"

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Dan Allah Hajja Sauda ki dena fadin haka, ke ma kin san uwa ba za ta cutar da diyar ta da gangan ba! Oh ni Aleesha Yakura ko a ina ki ke? Ya Allah ka kare min Yakura! Kai amma yaran nan be yi halacci ba! Be Kuma yiwa Malam adalci ba! Be min adalci ba!"

Cewar Ammy cikin kuka. Anty Sauda wacce ta dau zafi matuka ta kara da cewa

"Ku Kuma fa? Kun mata adalci ne? Gashi kun jawo ya dakile mata karatun ta dan wallahi ko yanzu aka ga Yakura kun gama cutar da ita, she missed two exams, talk more of halin da ta ke ciki, kai Aleesha ba ku yiwa yarinyar nan adalci ba!"

"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Cewar Ammy yayin da maganar Anty Sauda ke dada rura zuciyar ta. Wayar Anty Sauda ne yayi kara, ta yi saurin dagawa ta kara a kunnan ta ganin mijin ta ne mai kiran wayar. Nan ya sheda mata cewar sojojin da ke check point sun tabbatar da wucewar Yakura ranar da ta baro Yola zuwa Kano, haka kuma ta sake biyo hanyar a washagarin ranar a karo na biyu, Amma kada su damu in Sha Allah su na kan yin bincike.

Bayan ta aje wayar ne Anty Sauda ke fada ma Ammy halin da ake ciki. Ammy na mai daga hannu sama ta ce

"Ya Allah ba dan halin mu, Allah ka bayyana mana Yakura! Ba a ce an gan ta tare da Usman din ba?"

"Cikin motar haya wai zai san ko tare da wani ta ke tafe? Dama dai kuna da hotan almajirin ne da da sauki...."

Anty Sauda ta amsa mata ta na mai tabe baki cikin jimami.

"Yanayin shigar shi fa? Ai shigar sa daban ta ke da na mutane? Kai ta ya ma aka yi Yakura ta yarda ta bishi? Anya kuwa ba asiri ya mata ba kuwa?"

Cewar Ammy ta na sharar hawaye.

Anty Sauda ta amsa da

"Amen Ashe dai kuna kaunar ta kuka cuce ta"
Auren Shehu 2

5

Ko da ya isa gidan Hansai ba ta dena kuka ba, Iyalle ce ta masa bayanin rashin darajar da Zainab ta aikata musu, da kuma kwashe ruwan shan gidan da ta yi ta ja zuwa bukkar Shehun, Allah kadai ya san abin da ta yiwa Hansai sa'ad da ta leka dakin dan kuwa har lokacin Hansai ba ta dawo hayyacin ta ba. A fusace ya wuce bukkar ba tare da ya tambayi Hansai baasi ba, ya na sa kai cikin bukkar kafar sa ta sauka kan sauran ruwan wankan Zainab mai jirwaye da be gama shanyewa ba, haka kuma idanun sa ya sauka kan dan fantarin ta da ta wulgar gefe.

"Me ya faru a dakin nan?"
Cewar Usman a fusace.

"Au dama wannan bukkar daki ne? Caf ai ina na gane? Bayan hada jiki da irin ka ai sai an yi saukar dauda, wanka na yi......"

Wani irin mugun kallo da ya jefe ta da shi ne ya sanya ta dada gyara zama tana mayar masa da martani da irin kallan da yake mata. Tsiwar da ta ke masa be sa ya kasa ganin kyawun ta ba, duguwar rigar jikin ta ya mata kyau sosai musammam yanda ya bi jikin ta ya zauna daram. Haka kuma da niya ta yiwa bakin ta ado da jan janbaki duk dan ta boyewa Shehu halin kunci da ya saka ta ciki, dan ta lura ya gan ta cikin bakin ciki shi ne babban burin sa.

"Wanka ki ka yi cikin dakin nan? Yanzu fisabilillahi dakin nan ya miki kama da wurin kwana?"

Ta na mai daga gira ta ce

"Wallahi kuwa wanka na yi, ka fa san tsatona, ko bandakin masu gadin gidan mu ya fi bukkar nan daraja, bare na Zee, ka manta daga in da ka sato ni ne?"

Ya na jinjina kai ya kara da

"Da ruwan shan gidan nan gaba daya ki ka kashe ki ka yi wanka?"

Ta jinjina masa kai alamar
"Eh wallahi"

Usman yayi shiru kamar mai nazari, sannan ya furta

"Abin da aka yi bayan gida...."

"Kashi? Eh shi ma ni na yi wallahi!"

Yanda ta yi saurin katse shi duk bacin ran sa sai da dariya ta kusa kwace masa, wato lalle ya gane so ta ke ta tunzura shi ya yanke hukunci a kan ta, lalle 'yaro yaro ne' cewar Usman cikin ran sa, ya na mai murmushi ya furta

"In dai kashi ne ai mu muna maraba da shi, gwamnati ba ta ba mu takin zamani, dama da kashin mu ke taki, daga na dabbobin har na mu na mutane, Nan gaba in za ki yi sai ki min magana ni zan raka ki har daji yankin shukar mijin ki, kin ga sai ki saki jikin ki ki kasayar da hujja, yanda shuka za ta fito mu sami amfanin gona, yanzun ma ba ta baci ba na sa yara su kai daji....."

Yanda Zainab ta yi da fuska kamar mai shirin yin amai ne ya kara kawata nishadin Usman, be dena murmushi ba ya kara da

"Hansai kuma fa? Me ki ka mata?"

Zuciyar ta na tashi tsabagen tashin hankalin da furucin da Usaman ya saka ta, Ganin yanda idanun sa ke rawa jikin ta ya bata murmushi ya ke, cikin rashin fahimtar dalilin annushuwan sa duk wannan aika aikan da ta masa ta ce

"Ka tambaye ta mana! God you sting!"

"Abu duk lalacewar ki sai na tankwasa ki, idan ba haka ba ban Isa Shehu Usman ba, kin ci darajar amanar da mahaifin ki ya bani da kuwa sai kin kwashe kashin ki da hannun ki, haka kuma zan tambayi Hansai, matukar wani abu ki ka mata mai muni wallahi sai na aika kwatankwacin shi kan ki sai dai ita din ce ta ce ta yafe...."

"Allah ya sa kar ta yafe! Na tsane ka! Na tsane ku! Wallahi da ni ke da kai na da tuni na kashe kai na da wannan rayuwar azaba da ka saka ni....."

Shiru ya mata ya juya zai fita, har ya daga assabarin ya sauke, kana ya juyo ya na murmushin mugunta yayinda ya ke duban Zainab da idanun ta su ka cika da kwalla, ya ce

"Alhamdulillah, Alhamdulillah wannan shi ne kwatankwacin bakin cikin da na ke so na dasa zuciyar ki, ki sani wannan sumin tabi kenan domin kuwa nan gaba ba ni kadai za ki tsana ba Abu, na mi ki alkwarin kamar yanda ki ka tsani rayuwar wannan Ruga har kina tunanin kashe kan ki, sai kin tsani kan ki fiye da yanda ki ka tsane ni, wannan shi ne buri na, dan haka duk wannan abubuwan da ki ke aikatawa sun yi kadan su sa na karaya, ki sake sabon shiri..."

"Allah ya sa! Allah ya sa! Macuci! Allah ya isa"

Cewar Zainab cikin gunjin kuka. Yana dariyar jin dadi ya fita ya bar ta tana kukan takaici. Zuciyar sa fara sakamakon halin da ya bar Zainab ciki ya koma wajan Hansai. Wanda sai a sannan ta masa bayanin ganin Zainab da ta yi ba kaya ta na wanka tsakar daki, fadi ta ke

"Wallahi Kado batta mutunci, haka tibi tibi na gan ta..."

Cikin rarrashi Usaman ya mu su jawabi da

"Ku yi hakurin zama da Abu matukar kuna so na zauna da ku, idan kuma hakan zai zama da takura ku yi hakuri ku bari na hada nawa ya nawa na dau iyali na mu koma can birni....."

"Ah ah za mu zauna da ita Shehu, me yayi zafi da mu ka samu ma Allah ya dawo da kai, ai hakuri ya zama dole!"

Iyalle ce ta yi saurin katse shi. Cikin goyan baya sauran ma su ka yi alkawarin hakurin zama da Zainab, ita kuwa yar budurwa wacce ake kira Raqeeba zuciyar ta ce ta dada cushewa, lalle auren Shehu matukar yana tare da Kadon nan tasa ba karamin abu ba ne, ta yanke hukuncin lallba gyatumar ta Hansai cikin azanci ta bijirowa Usman da maganar auren.

Kamar yanda ya shedawa Zainab, yara ya sa suka kwashe kashin su ka kai daji, wanda da su ka dawo ko wanke hannu ba su yi ba su ka cigaba da hidimar gaban su.
Chapter 11 · 0% Book details