← Book details Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin kiri kiri za a aurar da yan uwan na ta biyu ga mazaje na gani na fada ne ya hana Zainab sukuni. Haka ta saka su Anty Sauda gaba da kuka, ta dena cin abinci ta dena walwala cewar ta da ta zauna da auren Usman gwara ta rasa ran ta. Ammy kuwa ta ce ba ita kadai ta haifa ba, idan mutuwar ta ce alkhairi gare su toh Allah ya sa a tafi a sa'a.

Duniya ta yi mata zafi, cikin kwana uku kacal ta rame ta fara lalacewa. Ganin haka Anty Sauda ta yanke hukuncin daukar mataki, gidan Malam ta je, ta saka Ammy gaba tare da Zainab, ta ce lalle ta kira gidan Kano ta ce Usman ya zo Maiduguri ta na san ganin sa.

Ammy na girgiza kai ta ce

"Ah ah ba zan kira shi ba fa, toh na kira shi ma akan me? Na fa fada mu ku wallahi babu yawu na cikin lamarin auren Yakura, gwara ma ta hakura ta zauna da mijin ta...."

"Na gaji da yin wannan maganar da ke Aleesha! Taurin kai gare ki kamar mutanan farko! Toh tantabara! Tunda masoyin ki ya daura ke kuma ba ki rabawa ko? Toh bari ki ga mu yi mai gaba daya, ni nan zan kira shi kuma sakin yarinyar nan ne sai yayi!"

Ammy na mai zuba mata idanu Anty Sauda ta kira numbar wayar da Malam ya aje bangaran masu gadi, wayar na kara ba a dauka ba, ta na shirin katsewa aka daga tare da yin sallama.

"Sunana Hajiya Sauda daga gidan Malam nan Maiduguri, ina son magana da Usman Maigadin"

Cewar Hajiya Sauda cikin dakiya. Shiru ne ya biyo baya daga bisani ta aje wayar ta na mai fadin

"Toh madallah, ke Yakura ai sai ki kwanatar da hankalin ki, Almajiri dai ya hade kayan sa yayi gaba, abin da abokin aikin sa ya sheda min kenan!"

"Yanzu haka ya tafi be sake ni ba? Toh wallahi ko da wasa kar a kara danganta ni da shi! Kada a sake cewa ina da aure...."

"Idan kuma ba haka ba fa?"

Cewar Ammy cikin tsawa, ta na mai nuna ta da yatsa ta ce

"Sai me za ki yi? As far as I'm concern Yakura ke matar aure ce ko kin ki ko kin so!"
Kuka Yakura ta saka wanda hakan ya sanya Anty Sauda fadin

"Sai ki kashe ta ki huta, ko kuwa ki janyo ta gudu ta bi duniya ayi biyu babu. Ke dena kuka na ce dai kun kusa komawa makaranta?"

Cikin muryar kuka ta ce

"Registration ma mu ke, na fadawa Ammy ko kudin registration din ma ba ta ba ni ba"

"Kudin registration dai? Ai kuwa a dangin uwar ki ba matsiyaci! Ki zo gida na ki karba gobe zan baki kudin registration da ma na kashewa"

"Waya ta ma ta lalace Anty Sauda"

Cewar Zainab cike da shagwaba.

"Toh kar ki damu sai a siyi wata ai, ki duba duk wacce ki ke so I got your back. Haka kuma ki hade na ki ya na ki ki koma makaranta, idan ma kin so kar ki halarci daurin auren gidan nan babu lalle ba tilas!"

Jin abin nema ya samu Zainab ta share hawayen ta tare da yiwa Anty Sauda godiya dan kuwa sai a sannan ta dan ji sanyi cikin ran ta, ta fice ta bar Anty Sauda da Ammy su na musayar magana kan ta, har sai da ran Anty Sauda ya baci sosai, cikin fushi su ka yi sallama ta tafi.

***

Washagari da sassafe Zainab ta nufi gidan Anty Sauda, Nan ta yi karin kumallo. Anty Sauda ta ba ta kudi masu yawan gaske domin registration da na kashewa har da na siyan wayar sanan ta kai ta super market ta mata siyayya sosai irin wanda Dady ya ke mata duk sanda za ta koma makaranta. Hatta tiket din jirgi Anty Sauda ce ta siya, Ammy ta sa mata idanu kawai. Wayewar gari Anty Sauda ta zo ta tisa ta gaba, Hajja Kilishi na fadin ba za ta jira a yi auren yan uwan ta ba? Anty Sauda ta ce
"idan lokaci yayi ta dawo, ai ba wani abu ba ne"

Ta yiwa kowa sallama amma ban da Halitta wacce dama idan ba dole ba magana ba ta hada su. Anty Sauda ce ta kai ta Airport, sai da ta tabbatar jirgin su ya tashi sannan ta juya gida.

Haka ma da jirgin su ya sauka birnin Yola Anty Sauda ta kira ta shedawa, Sai Anty Sauda ce ta sheda ma Ammy diyar ta ta sauka lafiya, ta kuma koma makaranta. Ammy da har ranta ba ta jin dadin halin da Zainab ke ciki ba addua ta yi, Allah ya shirya mata ita, ya sa ta gama makarantar nan lafiya ko Allah ya sa ta dawo gida gaba daya sai a san wani matsayi auren ta ya ke, idan kuma kafin nan Usman ya dawo a tura shi can makarantar ya je ya same ta.

***
A Rugar Shehu kuwa jama'ar Rugar na kan shiri na barin dajin falgore. Duk yanda Baffa Mudi ya buga surkullen shi jama'a ba su fasa shiri ba dan kuwa shiri su ke haikan, tare da taimakon Usman wanda cikin kankanin lokaci ya sami soyayyar jama'ar Rugar yara da manya. Iya kwanakin da ya rage mu su a kulli yaumin ya kan ziyarci kabarin Iyar sa, ya ke shafe awanni ya na hawaye ya na mata addua.

Ana sauran kwana daya su tafi aka kwana ana ruwan sama mai karfi a Rugar Shehu wanda ya hana kowa runtsawa, saboda tsoran rushewar gidagen su. Kusan awanni biyar aka dauka kafin ruwan ya tsaya, ruwa na tsayawa kenan ihu da kururruwar Bello ya karaɗe Rugar Shehu.

Usman da sauri ya isa gare shi, ga mamakin sa sai ganin Bello yayi ya na birgima kasa yayinda wani irin bakin abu ke fita daga bakin sa.

"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Cewar Usman yayinda ya tallabo Bello, be tsaya bata lokaci ba ya shiga karanto masa ayoyin rukiyya da ya koya wajan Malam dan ya tabbatar halin da Bello ya ke ciki ba zai wuce ko dai aikin sihiri ba ko kuma jinni. Sai da su ka kai kusan minti talatin cikin wannan hali, makota duk sun shigo suna tsaye bakin rumfar cike da al'ajabi, cikin su har da kawo Iliya. Bello ya saki nannauyar ajiyar zuciya sai kuma shiru jikin sa yayi sanyi tamkar matacce.

Ganin haka Usman ya rikici yayinda ya shiga jijjiga Bello ya na mai kiran sunan sa da karfi, jin haka Kawo Iliya ya shigo dakin da sauri ya na kokarin duba Bello ta hanyar saka kan sa bisa kirjin Bello. Cikin kaduwa Usman ya furta

"Shikenan Muhammadu Bello ma ya bi Iya! Muhammadu Bello ya tafi ya bar ni ni kadai Kawu Iliya...."

"Babu in da Muhammadu Bello ya tafi, a raye ya ke dan kuwa har yanzu zuciyar shi na harbawa"

Cewar Kawu Iliya ya na gyara kwanciyar Bello, be gushe ba ya kara da

"Kome aka yi Muhammadu ya shiga yanayi ko dai na sammu ko kuma makarin sammu da aka taba yi kan sa, zai fi kyau ka zauna nan tare da shi ka na masa tofi, in Sha Allah zai farfado cikin koshin lafiya"

Usman na mai kokarin saka zuciyar shi da ta amince akan bayanin da Kawu Iliya ya masa su ka yi sallama, Nan ya zauna tare da Bello ya na masa addua kamar yanda Kawu Iliya ya umarce shi, haka har ladanin Rugar Shehu ya kira sallar asuba Usman ya fita Sallah.

Bayan an idar da Sallah Usman ya dawo ya ji abin al'ajabin da ya zaci har ya koma ga mahallicin sa ba zai kara ji ba, wato muryar Bello da ta daki kunan shi ya na mai fadin

"Shehu......Shehu.....ka na jin murya ta kokwa dai a zuci na ke ma ka magana kamar yanda na saba?"

"Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu alaihi wasallam!"

Cewar Usman yayinda ya zube kasa ya na mai sujjada ga Allah. Ko da ya dago rungume Muhammadu Bello yayi, ya na hawayen murna ya ce

"Muhammadu Bello muryar ka na ji! Muhammadu Allah ya dawo ma ka da muryar ka! Ashe zan kara jin muryar ka? Ina ma Iya ta na raye Muhammad! Yau ga burin ta ya cika amma babu damar sanar mata"

Kamar yanda Usman ke hawayen murna haka shi ma Bello ya ke, fadi ya ke

"Zan sanarwa Iya, gari na haske zan je na sanar mata, zan yiwa Iya addua a zahiri ba a zuci ba, Zan yiwa Iya sallama, Allah ya sa za ta ji ni Shehu"

"Za ta ji ka Muhammadu Bello! Za ta ji ka da yardar Allah"

Cewar Usman cike da so da kaunar dan uwan na sa. Gari na wayewa labarin dawowar muryar Muhammadu Bello ya zagaye Rugar Shehu, labarin ne ya sanya Baffa Mudi ziyartar makabarta Rugar Shehu cike da tashin hankali domin neman amsar tambayar da ta addabi kwakkwalwar sa,

'shin ya aka yi maganar Muhammadu Bello ta dawo alhalin yanda ya birne layar da ya masa asiri da shi tare da gawar ladan matukar ba tono gawar aka yi ba Muhammadu Bello ba zai sake magana a doran kasa ba'

Ile kuwa nan ya sami amsar tambayar, ashe daminace ta yi gyara a tsohuwar makabarta da ta dade da cika, ruwan da aka yi daren jiya ne yayi ambaliya makabarta har ya bude wasu daga cikin makwancin mamata, in ban da farin yadi babu abin da ke yawo.

"Lalle damina baki mugunta, na tabbata ruwan nan shi ya tono asirin da na rufe shekara da shekaru, matukar ban nemo layar nan na sa an sake rufe wani mamaci da shi ba toh fa asiri zai tonu!"

Cewar Baffa Mudi yayinda ya cire rawani ya aje gefe, sai gashi tsome tsome da shi cikin ruwa da cabi ya na neman laya. Yana cikin wannan yanayi ne Usman da Bello su ka karaso. Cikin kwalla kira Bello ya ce

"Kawu Mudi! Halan wannan ka ke nema?"
Chapter 2 · 0% Book details