← Book details Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 34

Sashe 10

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sungumarta yayi ya aza bisa kafada. Ihu ta ke ta na kai masa duka da wayar hannun ta, da dayan hannun har ma da kafafun ta. Idan Usman ya na jin zafin dukan sam be nuna ba, tun ta na ihu har ta koma sirfa masa zagi, ko a jikin sa haka ya shiga Rugar Shehu, duk in da su ka gifta jama'a na gida da na waje kowa fitowa yake domin ya ka ga Shehu dauke da Kado, wannan lamari ba karamin mamaki ya ba su ba.

Ba shi ya sauke Zainab ba sai a tsakar bukkar sa, ta na mai mayar da ajiyar zuciya ta ke fadin

"Mugu azzalumi! Allah ya isa jiki na da ka hada da na ka!"

Rai bace ya ke duban yanda ta ke kabe jikin ta kamar wacce najasa ta taba ta, ta kara fadin

"Allah ya isa ka hada kazamin jikin ka....."

A fusace ya kai hannayen sa ya biyu bisa kafadar ta ya fizgo ta tsaye ya na mai hankado ta jikin sa ta fada kirgin sa, ya sa hannu ya rungume ta gam yanda ko kwakkwarar motsi ba za ta iya ba, haka kuma ihun da take son yi ya tsaya iya makogoro sanadiyar wani yanayi da ta tsinci kan ta, tun tana kokarin kwatar kan ta, har ta gaji, kan ta bisa kirjin sa ga mamakin ta duk da dai ba ta ji kamshin turaren da ta saba ji daga jikin abokan ta irin su Mike ko Bobo duk sanda su ka rungumi juna ba, Sam ba ta ji warin datti ko na hammata da take kyautata zaton za ta ji daga jikin Usman ba. Jin hanyen sa na shafa gadon bayan ta sai da ta ji yar tun daka yatsun kafar ta har zuwa gashin kan ta, ba ta san sanda ta runtse idanun ta ba yayin da bugun zuciyar ta ya karu, bakin sa dab da kunnen ta na dama ta na jiyo numfashin sa, ya furta

"Ni mijin ki ne! Jikin ki nawa ne ina da ikon hada shi da nawa duk sanda na ga dama, ku ma na san zaki sakar min jikin na ki, ji yanda ki ka saki jiki kina mayar da numfashi, ko da yake ba abin mamaki ba ne, tamakar karya ki ke kin saba sakarwa ko wani kare da biri jikin ki......"

Kamar wacce aka watswa ruwan zafi haka Zainab ta farfado daga shaukin da ta shiga na kankanin lokaci sanadiyar rungumar da Usman ya mata, kukan kura ta yi ta na mai ture Usman hakan ya sa shi sakin ta ya na murmushin mugunta, dama abin da ya ke so kenan ya gasa mata bacin rai, ran ta ya soyu shi ne farin cikin sa. Cike da bacin rai yayinda idanun ta ke fitar da kwallar bakin ciki ta ke fadin

"Ni Zee? Ni ka yiwa wannan cin fuska ka na almajiri mai gadin gidan mu? Allah ya isa! Abin da ka ke min Allah ya ma ka! Mugu azzalumi! Allah ya isa! Kai ne kare! Azzalumin! You will pay for this wallahi you will pay for this!"

Usman na murmushin jindadi da gamsuwar halin da ya sa Zainab ya sa kai ya fita ya bar Zainab zube ta na kuka. Kukan na ta biyu ne, na tsanar Usman da kuma haushin kan ta da har ta bari kaskantacce kamar Usman ya rungume ta, sannan ya kara mata da zagi tare da bakar magana, har ya kira ta karya!

Ta na cikin wannan tunanin ta ji alamar an bude assabarin daki an shigo, ba tare da ta daga kai ta ga wanda ya shigo ba ta ce

"Na tsane ka! Kada ka sake kai hannun ka jiki na domin kai ba ma ka kai darajar kare da birin ba! Wallahi da na hada jiki da kai gwara na hada da dabba...."

Jin shiru ba a tanka mata ba ya sa ta daga Ido ta ga wanda ya shigo, Nan ta yi Ido biyu da kyakkywar budurwa fara sol, wacce dudu ba ta wuce shekara goma sha biyar ba, hannun ta dauke da kwaryar nono, kamar yanda Zainab ta bude baki ta na duban ta, haka ita ma ta ke kallan Zainab cike da mamaki musammam da Zainab ta tashi tsaye da kyar, yarinyar ta ga tsayi da dirin Zainab, cikin ran ta fadi ta ce 'Babu shakka dole Shehu yayi duk abin da aka ce yayi akan Kadon Nan, ciki kuwa har da daukan ta da yayi a bainar jama'a'

Ta ji labarin kyaun fata da ido da Allah ya yiwa Zainab, amma ba ta taba tunanin Zainab din haka ta ke ba. Kumatunta yayi jajur sanadiyar kalaman da Zainab ke fadi tsabagen nauyin maganar, Abu daya ya mata dadi shi ne , wato kenan akwai kiyayya ta gaske tsakanin masoyin na ta da Kadon sa, ko ba komai wannan zai kara ba ta damar zama matar shi.....

"Wacece ke? Ki taimake ni na tsira daga hannun wannan azzalumin almajirin...!"

Maganar Zainab ya dawo da ita hayyacin ta, Har ta budi baki za ta bata amsa da ta san wanda ta ke magana akai kuwa? Sai ta tuna gargadin Shehu na kada su sake su nunawa matar shi suna jin hausa bare su mata magana da shi. Dan haka kawai sai ta aje kwaryar hannun ta ta juya ta fita ta na ji Zainab na ce mata dan Allah ta tsaya.

Jim kadan ta kara dawowa tare da wata kwaryar mai dauke da kwan zabi, Nan ma Zainab ta sake kokarin yi mata magana, yarinya ta nuna kamar ba ta gane abin da Zainab ke fadi ba, ta aje kwarya ta fita. Haka ta na kai kawo sai da ta aje kwarya har biyar, na naman zabi, sai ruwa, sai kuma 'yayan itatuwa.

Jin shiru ba ta sake shigowa ba ya sa Zainab tashi cikin dingishi, dan kuwa kamar yanda marar ta ta cika da fitsari haka hanjin ta ya cika da tutu, gashi gaba daya jikin ta ciwo ya ke mata ba ta daburin da ya wuce ta sami ruwan dumi ta yi wanka. Ta na tafiya da kyar ta fito waje yayinda ta ke ware idanu cikin fatan Allah ya sa Usman ba ya nan dan kuwa sam ba ta kaunar sake ganin shi. Ganin fitowar ta mata da yara kowa ya bar abin da ya ke ya na kallan ta. Cikin dauriya Zainab ta ce da su

"Ina ne toilet please?"

Kallan ta su ka tsaya suna yi babu mahalukin da ya san abin da ta ke nufi da "toilet" ganin haka Zainab ta kara da

"Mtswww na manta da jahilai na ke magana! Toh ina ne bandaki!"

Babu wanda ya tanka mata, hakan ya sa Zainab komawa bukkar Shehu, ta dauko butar da ta gani aje ciki ta ci sa'a akwai ruwa, da ta fito ta tarar suna nan dai tsaye kamar masu jiran tsammani, Zainab na mai musu alama da butar ta kara fadin

"Bandaki....wanka...ina zan yi?"
Duka su ka sa mata dariya, iya kulewa Zainab ta yi, ta na shirin juyawa ta koma daki sai ga Bello ya shigo da sallamar sa, ganin shi Zainab na mai yi masa alamar wanka da hannun ta ce

"Wanka, ina zan yi?"

Bello ya mata nuni da wani fili da ke zagaye da kara can gefe, ganin yanda Zainab ta zare idanu ta na kallan wajan shi kan shi Bello sai da dariya ta kusa subuce masa, ga tausayin ta da ya ke ji.

Ta na mai dawo da hankalin ta ga Bello ta sake fadin

"Oh my God! Yanzu fisabilillahi wancan zagayen shi ne toilet din ku? Ni Zee ni ce zan yi wanka cikin zagayen kara?"

Shi ma Bello tsayawa yayi ya na kallan ta kamar sauran yan gidan. Hakan ya sa Zainab juyawa ta nufi bandakin ta na fadin

"Na manta duka sokwaye ne a dajin nan! Ace rasa mai jin hausa sai wannan azzalumin! Kai wannan masifa da me ta yi takama! Bari dai na je na gani ko zan iya wanka, Duk Daddy da Ammy su su ka ja min wannan masifa! You will not get away with this! Wallahi you will not bari na tafi gida!"

Cikin tashin hankali da tsoran dattin da kazantar da za ta je ta tadda ciki ta yi adduar shiga bandaki ta kusa kai. Wayam ta gani, kasa ne shimfide a filin Allah, sai dan zarni da ke tashi sanadiyar rana da ya daki kasar, sam babu ko da masai ta tsugunno bare na tangaran da Zainab ta saba hawa, gashi a zahirin gaske a matse ta ke. Har za ta koma ta sake tambayar su ko dai sun yi kuskure ne ba su gane abin da ta ke nufi ba, idanun ta ya sauka kan wani dan roba mai dauke da sosan waya na wanka, ta tabbatar bandakin ne, kila sun bambamta shi da na ba haya ne.

Cike da kyamkayami ta sami gefe ta yi fitsarin cikin dabara ba tare da ta tsugunna ba, hakan ya ba ta damar ruke tutun da matse ta, Da niyar neman wajan yin tutun da wanka bayan ta idar da sallah. Da ta gama ta dauraye kafafun ta da ruwa sannan ta fito daga bandakin tana kakkabe kakkabe yayinda ta ke jin wani iri a jikin ta tsabagen kyamkayami da tashin hankali.

Har ta yi alwala ba su dena kallan ta ba, ta na idarwa ta yi sauri ta shiga ciki hannun ta dauke da butar ta ke fadin

"Mayu kurwa ta kul sai dai ku ci kan ku!"

Dankwalin ta ta shimfida kan ledar dakin, ba tare da ta tambayi ina ne gabas ba dan ta san ma babu mai amsa mata matukar ba Usman ba ta tayar da Sallah daga zaune, ta rama Asuba sannan ta gabatar da azahar. Ta idar ta na tunanin wanda za ta tambaya ina ne bayan gidan da za ta kasayar da tutun da ke cikin ta, ji ta ke tamkar zawo ne ke shirin kama ta, gashi Rugar kaf babu wanda ke amsa mata in ban da Usman.
Chapter 10 · 0% Book details