← Book details Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 12

Sashe 9

Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lkcn asmau ta fara girki a gidan breakfast lunch dinner kullum ba fashi, da farko daga mummy sai ɓangaren sabit kawai take wa abinci amma da ragowar ƴaƴan suka gano daɗin abincin sabuwar cook ɗin duk sai hutash she da matan su

Tun daga lkcn duk abincin gidan asmau ce take yi, kowa ya saba da cin daddaÉ—an girkin ta me sanya mutum santi, kafin kacr meye wannan sabit ya murmure yayi Æ´ar kiba yai fresh da shi abin shi kamar ba shi ba wannan abun yasa kullum mummy take godewa Allah daya haÉ—a ta da asma'u a matsayin cook É—in su

Ba sabit ba gabaɗayan yaran ta duk sun saba da wannan girkin da baiwar Allahn nan take yi sam babu wanda ya taɓa sawa a ransa cewar wataran zata bar gidan kunji ɗan adam

*BAYAN SHEKARA BIYU*

Ba abinda ya canza a rayuwar gidan su sabit sai lalacewar matan gidan, yo lalacewa mana don yanzu kowacce ta sakankance da asmau

Duk wani abu da suke so daga sun É—aga waya sun kira kitchen sun faÉ—a nan da nan za a kawo musu

Ta ɓangaren sabit kuwa sau biyu badia na kuma samun ciki yana zube wa inda daga ƙarshe aka gano cewar indai har suna son ciki ya zauna a marar badia sai da ta ta samu cikin ai mata ɗaurin mahaifa

Ga sabit da shegen son Æ´aÆ´a duk inda yaga É—a sai ya É—auke shi barin ma ace É—an fari ne, shi dai yana son mutum fari duk munin farin mutum baya gani

Haka zalika duk kyan baƙin mutum sabit baya gani sai yace ak shi wai baƙin ne yake kare masa ganin kyan, sai yayi taji ana cewa black beauty black beauty amma shi sam be taɓa sanin me kyau a baƙi ba

Har musu suke yi da abokan sa musammam masu baƙaƙen mata akan ɓaƙi ma yana da nashi kyan amma sabit sam be gane wannan karatun ba shi dai in kai baƙi ne to kawai kallon muni yake maka

Duk da dai yana da son yara amma baya son baƙin ɗa gashi mataɗ shi Allah ya haɗa ta da matsalar haihuwa inda suke ta fafutuka, Har yanzu a wannan halin suke inda sabit ya biya musu ummara suka kama hanyar ƙasa don su roƙi haihuwa

Ita badia sam abin be damun ta dama can ita ba child person bace ita ba mace bace me son yara ba don haka abin ko a ƙarƙashi takalmin ƙafarta wai rashin haihuwarta sam be dame ta ba

👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳

*cornflakes crispy cake, miyar gyaÉ—a with tuwon shinkafa, coconut drink*

*cornflakes crispy cake*

*ingredients*
-corn flakes
-chocolate bar
-butter
-sprinkles (ko wane iri)
-marshmelow (optional)
-vanillah extract
-salt

*method*

1) ki narka chocolate da butter ko a micro wave ko a kan wuta amma pls kar a sakar masa wuta

2) idan sun narke sai ki juye su a roba sannan sai ki zuba vanilla da É—an gishiri kaÉ—an

3) ki rugurguza cornflakes ɗinki da hannu ƙanana sannan sai ki zuba ki juya sai kasance kamar tuwo ne, irin zasu cure ne waje ɗaya amma duk da haka cornflakes ɗin zai kasance da ƙarfin sa

4)sai ki É—auko cupcake case É—in ki ki dinga É—iban haÉ—in nan kina sawa kina ajiyewa, idan kin gama sai ki bi kowanne da marshmelow sannan ki watsa sprinkles ki saka a fridge domin yin sanyi sai aci

*tuwon shinkafa served with migar gyaÉ—a*

*ingredients*

- farar shinkafa ta tuwo

-gyaÉ—a
-tomatoes
-attaruhu
-albasa
-tafarnuwa
-citta
-wuyan rago
-curry
-alayyahu
-thyme
-maggi & salt

*method*

1) ki haÉ—a naman,maggi, gishiri, albasa, tafarnuwa sai ruwa a cikin tukunya ki dora ki barshi yaita dahuwa

2) soya gyaɗa sama sama ta yadda ɓawon gyaɗar zai fita, sai ki surfa ki cire ɓawon sai ki daka ko kiyi blending, ki haɗa tomatoes da attaruhu kiyi blending shima

3) idan naman ya É—auko dahuwa sai ki zuba kayan miyar ki da soyayyan man da kike so amma kaÉ—an kasancewar gyaÉ—ar itama zata fitar da nata man

3) idan sun ɗan tafasa sai ki dama dakakkiyar gyaɗar ki da ruwa ki zuba, ki ƙara ruwa iya irin ƙaurin da kike son miyar sannan ki ƙara maggi in baiji ba ki rufe ya ci gaba da dahuwa

4) idan ya dahu kin tabbatar da komai ya dahu, sai ki É—auko alayyahun ki ki wanke sannan ki yanka sai ki zuba a miyar ki gare mata wuta ki bashi minti 1 sai ki sauke

5) ki wanke shinkafar tuwon ki ki jiƙa ta

6) ki zuba ruwa a tukunya wanda zai ishi shinkafar sannan sai ki rufe, idan ruwan ya tafasa sai ki tace jikakkiyar shinkafar ki ki zuba ki rufe don ya dahu

7) idan shinkafaɗ ta ɗauko tsotsewa sai ki rage mata wuta ya koma low saboda ta ƙarasa tsotsewa a hankali,

8) idan bayan ta tsotse sai kika ji bata dahu ba sai ki ƙara mata ruwan zafi amma karki taɓa ta ki barta haka akan low heat har ta shanye ruwan sai a tuƙa a kuma rufewa akan low heat ɗin

9) idan ta turara sai ki kwashe

*P S* ki sani dahuwar shinkafa ko ta ci ce ko ta tuwo ce ta fi son wuta kaÉ—an kaÉ—an da ta É—auko dahu

*coconut and banana milk shake*

*ingredients*

-ruwan kwakwa
-ayaba
-ice cream ko madara
-sugar
-ƙanƙara

*method*

1) bayan ki markaÉ—a kwakwar ki kin tace ruwan to ruwan kwakwar shi zamuyi amfani da shi

2) ki yanka ayaba ƙanana ki haɗa da ruwan kwakwa ice cream ko madara sai sugar sai ƙanƙara sai kiyi blending ɗin su

3) idan suka marƙadu sai ki juye a cup ko jug sai ki ƙara yanka ayaba a kai ayi serving

👩🏽‍🍳 *Bon appetit*👩🏽‍🍳

*ASMA'UN SABIT*
[4/17, 2:24 AM] 🥦: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛

👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳

🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠

ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)

P⃗a⃗g⃗e⃗ 8🌹

Mummy tana zaune rannan da yamma sai ga hjy munnira sam mummy bata kawo komai ba, suka zauna suka gaisa sai hjy munnira tace

"hjy takakkiya nayi, wallahi iyayen asmau sunce a dawo da ita lkcn aure yayi"

Mummy ji tayi kamar hjy munnira ta soke ta ita sam bata taɓa kawo wa cewar wai asmau zatai aure ba, ta gama sakankan cewa kaji san kai

Gyara zaman ta tayi don wannan magana ce da a za yi ta sosai asmau zata tafi bayan sun gama sakin jiki da girkin ta ai da sake

"hjy munnira ya baki taɓa min wannan maganar ba sai yau" inji mummy

"yo hjy sai na gaya miki ai kema kinsan mace ce kuma wataran dole ne tayi aure ko ba haka ba" shiru mummy tayi don kuwa zancen hjy munnira gaskiya ne

Tattaunawa suka shiga yi inda daga ƙarshe aka yanke hukunci mummy zata neman mata miji a cikin ma'aikatan gidan tunda ko taje can ma sai Allah ya haɗa ta mijin

A haka sukai sallama akan idan mummy ta samo mata mijin zata kira hjy munnira

Mummy ta tara ma'aikatan ta maza sannan ta musu albishirin akwai yarinyar da take son aurar wa cikin su ko akwai me so

"kar ku damu sadaki da kayan aure duk ni zanyi"

Kusan mutane biyar suka amsa suna so amma tunda mummy ta ambaci sunan asmau sai kowa ya janye

Mummy ba yadda batai da ma'aikatan ba amma kowa sai ya ƙi, kowa sai ya dinga kawo uzurinsa

"wa zai auri wata asmau ga baƙi ga rashin fara'a" inji driver, babu yadda mummy batai ba amma fafur suka ƙi haka ta sallame su suka watse

Duk wannan abun da ake yi asmau bata san wainar da ake toyawa ba, hankalin mummy ne ya kuma tashi don duk yadda ta É—auki abun ba haka yake ba

Shawara ce ta faÉ—o mata sai ta tara Æ´aÆ´an ta ko akwai wanda zai auri asmaun in yaso sai ta zauna amatsayin cook É—in daga baya idan ta girma ta mallaki hankalin ta a san yadda za a yi

Bayan duK sun taru amma banda sabit wanda yake ƙasa me tsarki shida matar sa, mummy ta gabatar musu da maganar da kuma hukuncin da ta yanke na ɗaya daga cikin su ya aure ta in yaso daga baya a san abin yi amma yanzu wannan shine kawai shawara

Shiru sukai kowannen su na jimamiba wanda yake son auren asmau, da babban É—anta tafa ra

"isma'il me kake tunani"

"gaskiya mummy bazan aure ta ba saboda kwananan zan sake aure Æ´ar meduguri ce magabata kawai zan gabatar a fara shirye shirye"

Ako koma kan na biyu sulaiman shima ya kawo uzurinsa, mummy tana kallon muktar É—an ta na uku yace

"gaskiya bazan iya ba matana sun iya girki"

Tooooo faaaa abu ya taru ya haÉ—ar wa mummy

"yanzu duk cikin ku babu wanda zai auri yarinyar nan na wani ɗan lkc haka kune son yarinyar nan ta tafi, a banza a wofi" ta faɗa ranta a ɓace

Kowannen su É—auke kansa yayi mummy ta dinga faÉ—a kamar ta ari baki dukkan su suka tsuke baki can sai sulaiman yace

"mummy ai mu mun matan mu sun iya girki, É—an autan ki ne matar sa bata iya girki ba kuma yarinyar nan kamar saboda su take zaune me zai hana ki aura masa ita"

Dukkan su suka amsa da haka ne kam shi kaÉ—ai ne ma mata É—aya

mummy shiru tayi tasan halin sabit da rigimar sa zata iya lanƙwas kowanne su amma banda shi,

"kun san halin sabit zan iya lanƙwasa ku amma banda sabit taurin kansa yafi komai"

"mummy ba sai ayi auren ba kafin ya dawo sai dai kawai ya dawo ya tarar da amarya" muktar ya faɗa yana d ariyar mugunta don ba ƙaramin rigima za a sha da sabit ba idan ya dawo ya tarar da ya angwance 💑

Babu yadda mummy ta iya haka ta É—auki shawarar Æ´aÆ´an ta dole ne ta aurawa sabit asmau kafin ya dawo in yaso idan ya dawo ayi duk waccd ayi da shi ita dai ta riga ta gama

Bata ɓata lkc ba taje ta faɗawa mijinta batun auren sabit ɗin da asmau amma bata faɗa masa dalilin auren ba
Chapter 9 · 0% Book details