← Book details Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 12

Sashe 11

Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har garin Allah ya waye sabit da badia basu daina fushi da junan su ba, haka kowa ya shirya ya kama hanyar office cike da jin haushin É—an uwan sa

Sai da suka dawo badia taga sam sabit bashi da niyyar lallashin ta kamar yadda yake mata ada idan sun yi faÉ—a yasa ta zuwa ta tsara wanka da kwalliya irin wacce sabit É—in yake so

Sai da akai sallah magariba ya dawo daga masallaci ya zauna a falo yana kallon news sannan ta fito tana karairaya

Ɗago ido yayi yakalle ta sai ya kasa ɗauke kanta, badia ta gama karantar sa tsab wani, dai da taje har kusa da shi sannan ya ruƙo hannun ta ya zaunar da ita akan cinyar sa

"ya dai my only wannan wankan yayi da me zan biya ne" ya tambayeta yana kashe mata ido

Fari tayi da idon ta wanda ya sha lashes na kanti

"haba *SD* sai kace baka san matsalar da muke ciki yanzu bane na auren ka da wannan yarinyar" ta faÉ—a fuskar ta kamar me shirin kuka

Sabit jinta kawai yake yi amma gabaÉ—aya ta gama da shi

"yanzu don Allah *SD* na dace zama da kishiya kalle ni fa"

Ta faɗa tana miƙewa tare da jujjuya jikin ta gaban sa ta yadda zata ƙara rikiɗa shi,

"only wannan salon naki yana ƙara rikita ni, zo nan in ji ɗimin jikin ki da nai missing jiya" ya faɗa yana kai hannun sa don ya jawo ta, sulalewa tayi ta ƙara nesa da shi inda shi kuma ya koma kan kujerar ya zauna yana kallon ikon Allah

" *SD* kalle ni fa so kake friends ɗina da ƴan uwana suyi min dariya kayi min kishiya ni me kurin baza ka ƙara aure ba" ta faɗa tana jujjuga jikin ta ya yadda zai ƙara ƙare mata kallon, sabit dai yana zaune kamar mutum mutumi sai kallon ikon Allah

"only ki zo nan muyi maganar mana zan fi ganewa" ya faɗa yana me niyyar kamo hannun ta wanda ta miƙa masa sannan ta taho da cat walking sai girgiza take yi inda gaba ɗaya duk wani lissafin sabit ya gama kwance wa

Sunkutar ta tayi sai bedroom É—in su,

Tana kwance akan gadon su inda ta rufe jikin ta da bed cover, a haka sabit ya fito daga toilet ya same ta,

"only dia na ɗauka zakiyi joining ɗina a toilet ne" ya faɗa yana goge kansa, ɗan ƙaramin tsaki taja sannan tace

" *SD* naga alamar kamar wannan auren da akai maka da sanin ka kana so shiyasa sam baka son mu samu mafita"

Ajiye towel ɗin yayi ya ƙaraso inda take zaunawa yayi a kusa da ita inda ya riƙe mata hannun ta sannan yace mata

"haba only ya zaki dinga abu kamar baki sanni ba, dia kin sam taste É—ina kin san koman da nake kin san yarinyar nan gabaÉ—ayan ta ba taste É—ina bace

Mace me kamada namiji namijin ma kamar É—an prison, me zanyi da ita sam bata da girly personality, kuma kin san nafi son mace me koman ta na mata ne, amma wannan kamar wani namiji fa haka nake ganin ta"

Badia taji daɗin yadda ya kushe asmau sai ta ƙara narkewa sannan tace

" yanzu *SD* yaushe zaka sake ta"

"dia kin dau ji abinda mummy tace sai kin iya girki don haka sai ki dage ki koya"

A firgice ta ƙwace hannun ta daga cikin nasa wanda hakan ya barshi da sakin baki

" *SD* kana nufin kana goyon bayan in koyi girki kenan, kuma kasan ni am not a kitchen person" riƙe ta ya ƙara yi

"na sani only dia amma kinga abinda mummy tace idan kin koyk girki mun huta nima sai ki koya min in yaso sai mu dinga sharing duty yau in kikai girki gobe sai inyi kinga mun huta da cin abincin da bamusan tsabtar wanda yayi ba ko"

Ya dinga kamale ta yana rarrashin ta har ta yadda zata fara koyon girki, suka gama haɗa plan cewar a waje zata je koyon girki ta yadda sai dak kawai mummy taga ta iya girki haba ai da ta ƙware da wannan ƴar iskar yarinyar tayi waje va sakinta kawai sabit zaiyi ba sai ta saka shi ya kore ta ma

*******************

Hjy badia ta je ta sai form a wani cooking class zata ta fara koyon girki, ranar da ta fara zuwa ta ga yadda ake abinci kamar tayi amai

Babu abinda yake tayar mata da hankali kamar nama ɗanye, tunda ta bar cooking tace bazata ƙara komawa ba saboda basu da tsabta

Sabit sam be damu ba don haka sai ya kuma samo mata wani cooking class É—in shima duk sammakar ce wai basa wanke nama ya fita tas suke É—aura wa

Cikin wata ɗaya sun zageye kusan dukkan cooking class ɗin da suka sani amma duk cikin su babu wanda ya iya girkin irin wanda badia take son yi babu yadda ta iya haka ta haƙura da koyon girkin

Sabit ne ma ya dinga matsa mata akan ta kuma dubawa, ko da faɗa masa matsalar ta na ƙyanƙyamin naman da basa wankewa sai yace mata

"me zai hana ki nemi wannan yarinyar ta koya miki kinga ita ta ƙware kuma daga gani tana kula da tsabtar abincin ta"

Sam badia bata yadda da wannan shawarar ba ai bada kaine ma yarinyar da aka aura mata mijinta itace zata ce ta koya mata girki ai ta faɗi ƙasa ba nauyi

Ƙiri ƙiri tace bata yadda ba inda daga karshe har ta kai su da faɗa wai sabit yanzu ya fara son asmau, shi kuma ya dinga rantse mata ba abinda yake haɗa shi da ita, faɗa sukai da gaske

Ganin sabit bashi da niyyar sakkowa ne ya sa badia shiryawa domin zuwa wajen asmau koyon giki ```tirƙashi koyon girki wajen kishiya amma an faɗi ba nauyi```

Asmai tana zaune ta gama lunch kenan duk an rarraba kowane ɓangare tana shirin hutawa kenan sai taji wata yarinya asabe da ke aiki a kitchen ɗin gidan ta shigo

"anty asamau wai inji wannan farar matar me iyayi tace kije" tsayawa nayi ina tunanin wace farar mata ce ko dai mummy ai asabe ta san mummy

Tashi nayi na É—auko hijabi na na fito, ina fitowa naci karo da badia sai wani yatsine fuskar tar take yi kamar wacce taga kashi

"ke da a wannan ƙazamin wurin kike mana girki kina aiko mana da shi, meye amfanin ɗauko ki aiki ko ba biyanki ake yi ba, don me yasa baza ki dinga sakawa ana gyara wajen ba" ta faɗa

Ƙarewa wajen kallo nayi babu abinda ya same shi yanzu yanzu nan suka gama share wa amma ƴar rainin hankalin nan zata wani ce wai datti

Samun gefe tayi ta kyafe sannan tace

"ki dauko tsintsinya ki ƙara share wajen don nazo ne zanyi wa sabit girki bazan iya ciyar da mijina abincin da aka dafa a wannan ƙazamin wurin ba"

Ban ce mata komai ba kawai nai shigewata ciki nai kwanciya ta har yanzu bata san wace asmau ba bata san ko wannan koÉ—aÉ—É—an mijin natan bai isa ya sani ba balle ita

Ganin na daÉ—e ban fito ba ya sata shigowa É—akin ganina a kwance ya sata fara masifa

"lallak ma yarinyar nan kinci kin ƙoshi shiyasa har na saki aiki amma kika ƙi yi"

Iskar data kwaso ta ma ban shaƙa ba balle ita, masifa ta dinga yi tana gaya min magana wai ƴar ƙauye ta zo birni, ganin bazan iya shiru ba yasa nace mata

"to wai in girki zakiyi na É—auka part É—in ki ma akwai kitchen meyasa ba zakiyi a can ba" na faÉ—a kaina tsaye

Masifar dai ta ci gaba da yi kamar ba gobe sai da ta gama sannan ta É—auko wayar ta ta fara dailing

Ana É—auka na ga tafara magana

" *SD* ai ma faɗa maka yarinyar nan ƴar rainin hankali ce kagan ni a kitchen ɗin amma tana kwance sam ban san me take nufi ba" ban san me yace mata ba sai kawak ganinai ta miƙo min wayar

Daga ita har wayar na doka wa wata harara sannan na kuma mai da kaina na gyara kwanciyata ta,

Wani zagi na ji ta É—ura wanda sai da na toshe kunne na saboda tsabar girman sa

" ikon Allah *SD* wallahi ta ƙi karɓa," ban san me ya faɗa mata ba sao dai naji ta kashe,

Intercom ɗin da ke kitchen ɗin aka kira ban da niyyar tashi sai dana ga dama har ta kusan tsinkewa sannan naje na ɗauka, ashe mummy ya kira shima mummy's boy 😁

Ana take gaya min wai in koya wa badia girki ban musa mata ba kawai dai na dawo nace wa gwanar ta zo muje kitchen É—in

Dagewa tayi wai bazai tai girkin ba har sai na saka yara sun ƙara gyara kitchen hmmm lallai baki san wace asmau ba na faɗa, neman wuri nayi na kuma kwanciyata

sabit ta kuma kira ta kuma faɗa masa ai na kuma kwantawa shi kuma ya kuma ƙara kiran mummy ko da mummy ta kira tsab nai mata bayanin abin da ke faruwa bata ce ko mai ba kawai ta kashe wayar

Allah ne kaɗai yasan me tace aa sabit ɗin sai gashi ya kira ta wai muyi girkin a haka wannan abun ya bala'in ɓatawa badia rai

shigewa tayi kitchen É—in inda na bita a baya don fara girkin fatana dai Allah yasa har mu
gama bamu ƙona kitchen ɗin ba don na fahimci ƴar rainin wayo ce to nima duk all d same ne ai

*Parpesun naman kaza zatai masa da jollof rice sai cole slow da kima fruit salad* ```recipe yana ƙarshen page ɗin in shaa Allah```

Ita me koyon girkin tana zaune akan wani stool na kitchen É—in nice nake komai, naman kazar nan an wanke shi ya fi so goma

Ni dama tunda na wanke tace be mata ba sai na dangwarar mata da shi,

"kiyi irin wanke war da kike so idan kin gama na É—aura" na faÉ—a mata na cigaba da haÉ—a ragowar abincin
Chapter 11 · 0% Book details