← Book details Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 12

Sashe 4

Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rayuwar sabit in akwai abinda yake so da badia be wuce ƙamshin ta da gayun ta ba ga uwa uba fara ce tas kamar jinin larabawa, ƙarasowa tayi cike da yanga da kuma shagwaɓa ya zauna kujerar da ke kallon tasa sannan tai narai narai da ido kamar me shirin yin kuka sannan tace

" gaskiya *SD* ka shanya ni, tun biyar nake ta jiran ka sai yanzu, kuma kasan dokar ka ta gama hira ƙarfe 08:00pm gashi yanzu takwas ɗin ta kusa" ta ƙarashe zancen ta tana kyakkyaɓe fuska kamar me shirin kuka

Wannan abun da badia take yi shine abinda yake ƙara hargitsa wa sabit tunani har yake ganin kamar bazai iya rayuwa ba tare da ita ba

Haƙuri ya shiga bata inda ya kuma kawo mata uzurin office ne ya hana shi zuwa da wuri, sai ya kawo mata zancen da yasan zatai farin ciki da shi na batun auren su

Nan ta nuna murnar ta kamar ba gobe bata da wani ragowar buri a rayuwar ta daya wuce ace ta mallaki sabit a matsayin miji, miji na nuna wa sa'a, mijin daya ke kallon ta ya daki ƙirjin sa cewar daga ita ba ƙari, mijin da a kullum zai dinga saka ta cikin farin ciki

Tattaunawar su suka ci gaba akan yadda za a gidanar da bikin da kuma shirye shiryen da zasuyi na bikin, har mahaifinta ya dawo sannan sukai sallama inda ya je domin su tattauna da shi akan magabatan sa da yake son turowa

Cikin hukuncin Allah sukai tsaida magana inda mahaifin badia yace wa sabit ya turo da iyayen sa sai a ƙarasa maganar tunda maganar ta manya ce

Sabit cike da farin ya koma gida inda ya sanar da mahaifiyar sa,

Mummy ta taɓe baki ta gyara zama, sarai ya san dalilin wannan abu mummy tana da wani aqida ne wai sai lallai mace ta iya girki, shi kuwa sabit ba shi da wannan tunani shidai kawai ya auri badia

"auta kana ganin wannan me rawar kan da kake son É—auko wa ta iya girki kuwa, ko in nemo maka wata in yaso dai ka haÉ—a biyu kamar Æ´an uwanka"

"mummy na ɗauka mun gama wannan maganar da ke,ni dai gaskiya bazan ƙara aure ba akan girki, kin yadda da wannan inda ni kuma na yadda bazan nemi aiki a ƙasar waje ba zan zauna kusa da ke"

Ya faɗa yana kallon ta don ya son ba abinda mahaifiyar sa ta ƙi jinin ji daya wuce yace zai fita ƙasar waje neman aiki takance duk abinda baka samu a ƙasar ka ba to bazaka same shi a waje ba

"to kuma me ya kawo wannan maganar, don kawai na tambaya ka a kan iya girkin ta"

"mummy ma'aikaciyar banki ce don haka ko aure mukai ba zama za mu dinga yi a gidan ba, ita tana wajen aiki nima haka don haka karki damu"

Taɓe baki tayi Sam ita ba haka take so ba, ta so ace sabit ya ɗauko macen da ta iya girki sosai tunda shi mutum ne me son girki different varieties amma wai ya ɗauko wani tsari wai aiki, duk cikin matan ƴan uwansa babu wacce take aiki sai matar shi kawai, lallai dole ne ta dakatar da wannan aikin taya ma za ayi ta iya kular mata da ɗanta bayan tana aiki

Sabit yadda yaga mommy ta zurfafa cikin tunani yasan tasa saƙa wani abunne don haka sai yace mata

"mummy i hope u r not thinking about any strategy don mun riga mun gama yarjejeniya da ke akan baza ki shiga maganar aure na ba"

"to me kaji nace, ni batun aikin nata ne kawai bana so"

"mum ki bar komai kawai mun riga mun gama tattaunawa da ita da aikin ta na ganta don haka bazan hanata ba, kuma aikin ta bazai hanata kula da ni ba" ya faÉ—a yana ficewa don yasan idan ya tsaya sai mummy ta kawo wani abun da bazai iya magance shi ba

*******************

Cikin hukuncin Allah aka kai kuÉ—in auren sabit inda da yake abin na manya ne aka saka wata biyu, ba abinda zamuce sai dai muce Allah ya kaimu

********************

Asmau an ƙara wayewa ta ɓangaren girki, kullum ƙara gogewa take yi ta ɓangaren sarrafa abinci kala kala, wannan ƙwarewar tata yasa ya ƙara jawo wa restuarant ɗin su customers sannan restuarant ɗin ya kuma yin suna lungu da saƙo an san shi kuma ana zuwa ko cin abinci ko yin order

Wannan iya girkin na asmau ne ya saka hjy munnira tura ta zuwa ga wani catering school don ta ƙara ƙwarewa, don duk wani abinci na zamani a restuarant ɗin sai a hankali sun fi siyar dana gargajiya

Domin a ƙara haɓaka restuarant ɗin ya kasance duk irin sunfarin abincin da kake so akwai sai hjy munnira ta tura ta catering school inda taje ta fara koyan abincin na garuruwa iri iri kama daga na turai, larabawa, chinese da dai sauran su

Shekarar asmau ɗaya tana karatu inda ta ƙware ta fi da ƙwarewa har ta kai duk restuarant ɗin itace chef de cuisine wato itace shugaban ƴan kitchen ɗin gabaɗaya duk da ƙanƙantar shekarunta

Girki take fesawa na kece raini, babu wanda zai ci abincin ta baiyi santi ba, wannan ya sa restuarant ɗin ya kuma haɓa ka har hjy munnira ta ƙara buɗe branches inda duk anan ake yin girkin sai ana gama duk sai akwasa akai can branches ɗin

Duk wannan ɗaukakar da Allah ya bawa asmau me sa ta ta fara kula da jikin ta ba, tana nan baƙar wuluk kamar da fuskar ta ake girkin, ga rashin fara'a wannan ɗabi'a ce sam a lamarin ta ba fara'a

Ga miskilanci sai ta wuni bata cewa kowa uffan ba, don haka da wuya kaji anyi faÉ—a da ita ko cecekuce, ita dai kawai tayi aikin ta ta koyi sabon girki sannan tayi kuma a yaba

Rashin fara'ar da sakin fuskar ta yasa duk mazan da ke cikin kitchen ɗin suke ganin girman ta duk da dai a kitchen ɗin har yanzu ita ce ƙarama, don har yanzu batai 16yrs ba, ga ƙaramin jiki sai ka ɗauka ma she is only 13yrs amma sai shegen basirar sarafa abinci kamar da wannan hikimar aka haife ta

******************

Ko da lkcn auren sabit da badia ya matso sai mummy ta zo restuarant ɗin hjy munnira akan tana son cooks waɗanda zasu dinga yi mata girki da bikin ko dan baƙin da zasu zo na kwana

Ganin yadda mummy tace wa hjy munniran zata biya su labour É—in su ne yasa hjy munnira amincewa har da saka asmau a ciki tunda girkin kwana uku kawai zasu yi anyi bikin an watse, don haka sai ta yanke hukunci tura asmau ita kaÉ—ai tunda mummy tace akwai ma'aikatan da zasu taya su aiki, ita kuma hjy munnira bazata iya barin iyayen kuÉ—in nan da mummy take da niyyar biya ba

Asmau bata san hawa bata san sauka ba kawai sai taji hjy munnira tai mata maganar tafiya gidan wata wai zata dinga abincin biki da taimakon wasu

Fuskar nan tata da kullum take cunkushe ba fara'a ta ƙara tsuke ta sannan tace

"hjy ban gane ba, ai ni aiki na anan yake"

"can ma aiki zaki yi na kwana uku ki dawo, biyan ki nake yi don haka ina da ikon tura ki duk inda na ga dama, sauran inkin je ki ci gaba da wannan turɓune fuskar taki" ta ƙarashe zancen ta tana ficewa tare da barin asmau ita kaɗai a ɗakin

Ran asmau yai mugun ɓaci wai taje wani gida aikatau duk da dai aikatau aka kawo ta amma yanzu ai ta wuce wannan matsayin amma shine matar nan take son kai wani gida wai ta zame musu cook ta biki, ƙara cunkushe wannan fuskar tata tayi sannan ta fito ta fara haɗa kayan ta

A cikin restuarant É—in taci karo da driver na gidan da zata yana jiran ta, inda bayan ta fito hjyr take ce masa

"gata nan ita kaɗai ce zata" bin asmaun yai da kallon raini inda ita kuma ta daka harara tare da ƙare haɗe ranta

"hjy madam fa mutane uku tace ya zaki haÉ—ani da wannan Æ´ar yarinyar" dariya hjy munnira tayi sannan tace

"kace wa madam wannan itace best chef ɗin gidan nan shigasa na bata aron ta" ƙara kallon baƙar yarinyar yayi sama da ƙasa yadda ta wani haɗe ranta kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa ga ƙanƙanta amma wai ace ta fi kowa iya girki lallai ashe ma girkin ba wuya, ya faɗa a ransa

"muje to da rabon madam ta dawo da mu"

"in bata yadda ba kace ta gwada giÉ—kin yarinyar kafin a dawo da ita" gyaÉ—a mata kai kawai yayi suka fice inda asmaun ta fice ba tare da tayiwa hjy munniran sallam ba don har yanzu haushin ta take ji

Sunyi tafiyar kusan minti ashirin sannan suka ƙaraso wani tafkeken gida, tunda muka fito drivern nan yake min surutu iskar da ta kwaso shi ma ban shaƙa ba balle zancen sa ko da ya ga alamar banni da niyyar tanka masa sai ya ja bakin sa ya tsuke har uka isa gidan layi guda ya cinye, a ƙofar wani makeken get driver ya tsaya inda suka fito tare

Tsayawa tayi tana ƙarewa gidan kallo dabadan hjy munnira ce ta ce mata ta biyo shi ba da ba abinda zai sata biyo shiva wannan gidan kamar na yankan kai

Sai da suka ƙwanƙwasaƙofar sannan wani turƙeƙen arne ya leƙo

"who's knocking" ya tambaya da wata muryar sa wacce zata iya sawa mutum ya zura a guje, ganin driver É—in ne yasa shi wangale baki wai yana murmushi

Shi kanshi murmushin ƙara masa muni yake balle kuma, buɗe mana get ɗin yayi muka shiga, inda muka tasamma tafiya kamar zamu wata unguwa ba acikin gida muke ba

Sai da mukai tafiya me nisa sannan muka isa wata ƙofa inda drivern ya danna door bell sai ga wat ƴar dattijuwa nan ta zo ta buɗe
Chapter 4 · 0% Book details