← Book details Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 12

Sashe 7

Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da yamma tayi kowa ya dawo daga aiki duk an hallara wajen cin abinci za a fara ci sai mummy

"to amaryar sabit dai bata iya girki ba kuma mijinta ya É—aure mata gindi yace shi ba komai ai ba sai lallai mace ta iya girki sannan za a zauna da ita ba"

" haka ne mu ba kowacce mace ce akayi ta domin kitchen ba" maganar nan tayi bala'in ɓatawa mummy rai inda ta kai masa harara

"to daga yau sai ku dinga cin abinci a part É—inku in cook zaku É—auko bismillah amma mun daina ciyar ku"

Babu wanda ya kuma cewa komai mummy ta so daddy ya mara mata baya amma sai taji yayi shiru dama shi mutum ne me bin ra'ayin Æ´aÆ´an sa

Sai da suka gama cin abincin ne sannan mummy ta kuma nanata musu akan su nemi me ciyar da su don ta tsame su daga waÉ—anda zata dinga ciyar wa, ko a jikin su daga badiar har sabit É—in suka kama hanyar part É—in su

Kashegari badia ta kira mmn ta ta faÉ—a mata abinda yake faruwa da kuma hukuncin da suka É—auka na É—auko cook,

Mmn badia ta sha alwashin sai ta nemo musu cook É—in da ita kanta mummyn ma a wajen su zata dinga kwaÉ—ayi

Cikin hunkuncin Allah aka samo musu wata agnese kafira ce, amma tsohuwar cook ce abincin ta da daÉ—i kasancewar ta daÉ—e tana yi

Kafin su tashi da safe ta haɗa musu breakfast haka ma kafin su dawo da yamma ta ajiye musu lunch haka ma dinner akan lkc wannan ne ya kwantar da hankalin ma'auratan ya kasance ba abinda suke yi daga aiki sai soyayya 😍

Ana haka ana haka badia ta samu ciki, me shegen laulayin tsiya ga miyau, ga shegen kwaɗayi, rannan da sassafe ta na tashi wa alala zata ci, don haka sai sabit ya sauko ƙasa don gayawa agnese tayi mata alala

Me zai gani agnese ce a kitchen hannun ta a hammat sai faman susa wa take yi, tana gamawa ta saka shi a hanci ta shinshina yana gani yadda ta ɓata rai daga dukkan alamu bata ji daɗin warin da hammatar ta take badawa ba sannan ba wanke hannu kawai ta koma ta ci gaba da girkin ta

Jun shi yayi kamar zai yi amai tunanin girkin ta daya dinga ci yayi, ji yayi gabaɗaya zuciyar shi na tashi, be yi ƙasa a gwiwa ba yana zuwa ya gayawa badia abunda ya gani

Aikuwa itama sai amai anan inda take, abu goma da ashirin ya haÉ—u ya haÉ—ar wa sabit, shi yayi aikin aman sa don ba ba komai a aman sai ruwan da tasha

Badia da kanta ta kori agnese sannan ta kira mmn ta akan a nema musu wata sabuwar cook É—in ko da mmn ta tambaye ta ina agnese sai ta faÉ—a mata abinda sabit ya faÉ—a mata

Ita kanta mmn ta koka da wannan abu inda tai mata alaƙawarin sake neman wata me aikin, too fa aiki ya dawo sabit sabo, ya je aiki a hanyar shi ta dawo wa doƙe ya tsaya a restuarant ya sai musu abinci kafin ya dawo

Wani lkcn in ya makara sai dai ya kira badai ta siyo musu haka suka dinga jaurar siyan abinci sune shiga wannan restuarant fita wancan don siyan abinci

Rannan sai ya kama ranar da badia zata siyo abinci ne amma sai ta manta sabit ya dawo gida gajiye ga yunwa ko da ya tanbayi abincin sai tace masa ba kak bane da siyowa

Ranshi ne ya ɓaci don abun nata kamar da rainin wayo,

"so nawa zan siyo jiya ba ni na siyo ba" ya faÉ—a ranshi a bace, É—aga kafaÉ—ar ta tayi alamar bata damu

"na manta na ɗauka kai ne yau ma" ranshi ne ya ƙara ɓaci wato ita sam bata ma san laifi tayi ba ko, nan da nan ya hau masifa inda itama ta biye masa sukai ta bala'i

Wannan shine faɗan mu me girma na farko tun aurensu amma sun yi faɗa kamar ba gobe daga ƙarshe kowa yayi zuciya ya kama hanyar ɗakin sa baza a kwana tare ba, a daren badia tai ɓari

Sabit be sani ba sai da safe da ya fito ya ganta a falo da akwati tana ta ja ita zata tafi gidan su kamar ya share ta sai kuma dai ya tambaye taa

"ina zaki da akwatin nan haka"

"gidan mu zan koma tunda wanda ya ajiye ni be damu dani ba har nayi miscarriage be sani ba"

Kalmar miscarriage ce kawai ta dawo da shi daga tunanin da yake

"what, me kika ce" ya faɗa yana kara matsawa kusa da ita cike da tashin hankali maimai ta masa tayi tayi ɓari

Jikin shi har rawa yake ya sunkuce ta sai mota yana ta adduar Allah yasa ba gaskiya bane cikin daya ƙwallafa rai da shi za a ce ya zube subhanallah

Gudu kawai yake falfalawa domin son zuwa asibiti sai da badiar tai masa magana ma akan ya rage gudun sannan ya rage burin shi su je asibitin ace bai zube ba

Cikin ikon Allah suka iso asibitin da badia ke awo suka shiga wajen ganin dr. binciken farko ya nuna ciki babu shi

Sabit kamar yayi kuka a rayuwar shi yana son yara barin ma ace yadda badia ke da kyan nan a haÉ—a da nashi ai Allah ne kaÉ—ai yasan irin kyan da Æ´aÆ´an su zasuyi

Hankalin sa ne ya tashi sosai inda duk ya bi ya tsagwami kansa don shi a tunanin sa faÉ—an da sukai jiya ne ya zubar mata da cikin

Badia sam hankalin ta be wani tashi ba kamar yadda sabit ya tashi nashi hankalin daga ƙarshe ma sai ita ce ta koma tana lallashin sa

" haba *SD* kar ka damu in shaa Allah we will try again, kuma cikin be fi wata biyu"

"only kin kuwa san yadda na ɗaura raina akan cikin nan wallahi nagi nake yi kamar fault ɗina ne da bamuyi faɗa ba da ƙila cikin bai zube ba" ya faɗa da alamar tausayi a tattare da shi

Lallashin sa ta dingayi, bayan an basu magani an sallame su sai ta saka rigimar ita gida zai kaita har ta warke

Ba haka ya so yaso ace ta dawo gidan sa tayi jinya amma ganin bata da lfy ya shi ƙin cewa komai kawai yai hanyar gidan su da ita

Yana ji yana gani ya kai badia gidan su ya baro ta acan don ta samu ta ɗan huta, kuma ta samu sauƙi, ko da ya dawo gida ya faɗawa mummy abinda ya sameta

Sai mummyn ta jajanta masa sannan tai masa ƙorafin zuwan badia gida, kyakkyaɓe mata fuska yayi kamar zai yi kuka, wannan ne ya sa ta jan bakin ta tayi shiru

********************

Sai da badia tayi wata guda a gida sannan ta dawo shima sai da sabit yai ta safa da marwa yana roƙon ta sannan ta dawo anna wannan karan ma da sabuwar cook ɗin su

Me suna kulu, to ita matsalar klu bata iya kowane abinci ba sai tuwo da dai dangin na gargajiya bayan kuma su sabit Æ´an zamani ne ba son tuwon suke ba

Wannan dalilin ne ya sa kulu bata daÉ—e ba suka sallame ta, suka koma take away daga restuarant

Duk abinda ke faruwa a part ɗin sabit mummy tana sane ta ƙyale shi ne kawak don taga iya gudun ruwan sa

A ka ci gaba da yin take away har Allah ya kuma haɗa su da wata sabuwar cook ɗin, ita kuma sata duk abinda ta gani sao ta ɗauka ta ɓoye da taga lkcn ba mutane sai ta fice daga gidan

Rannan sai ta É—auki agogon sabit ya ajiye akan dinning table yana breakfast kawai ya shiga É—aki ya fito ya nemi agogo ya rasa

Tun yana nema shi kaɗai har badia taji suka shiga nema tare, abu kamar wasa agogo yayi ƙafa ya gudu

Sam basu kawo ita ta ɗauka ba don har da ita ake ta nema, sai badia ce kamar ance ɗaga idon ki ki kalle ta sai taga gefen zanin ta yayi wani ƙulili

Tambayar ta tayi

"ke meye a jikin ki haka" nan da na sa jikin yarinyar ya É—aurawa, badia kuwa ta kwacume ta ta kwance mata zani sai ga agogo

Shidai sabit tunda ya É—auki agogon sai ya fice ya barsu inda badiar ke ta dura mata zagi, daga nan ita ma ta kore ta,

Abinfa ya fara isar sabit wai duk masu girkin da aka samo musu sai sun samu matsala ne me yasa baza su samu cook É—aya ba mtsss Allah dai ya kyauta

Kuma neman wata cook É—in sukai inda aka kawo musu wata tivi, kana ganin ta kaga rashin tsabta, har wani tashi take don tsabar tsamin da ke fita daga jikin ta

Sabit sam hankalin sa be kwanta da ita ba don shi mutum ne me shegen ƙyanƙyami don haka ko tayi abinci baya ci sai dai yai ta raɓe raɓe yau shine cin abinci anan gobe a can

A maimakon shi da yake da mata a ganshi ya murmushe sam sai ma wani ramewa yake yi, ya ya bazai rame ba sam baya samun kulawa ko ta ɓangaren cin abinci balle kyakkyawan kula daga matar sa

Sun tashi da safe sun fice gabaÉ—aya idan sun dawo da yamma kowanne su a gajiye yake don haka kowa ta kai ta kai yake balle badia ita bata san wani wahala da wani ba balle tace wannan mijinta ne ai ba yaro bane zai iya kula da kanshi haka take cewa

Tun mummy na É—auke kai har abin ya zo ya fara damunta ta kasa shiru kun san tsakanin É—a da mahaifi balle kuma mummy me shegen son Æ´aÆ´a

Don haka rannan da ya shigo da safe gaishe ta sai ta gabatar masa da abinci be ji komai ba ya zauna ya takr cikinsa kamar wanda ake wa horon yunwa
Chapter 7 · 0% Book details