← Book details Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 12

Sashe 10

Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dady sai yace
" to shikenan dama gobe zani kano ɗaurin aure sai kawai mu ƙarasa can garin su yarinyar sai a ɗaura mata tunda kince ya dawo kike son ayi"

Mummy sai taji daÉ—in yadda sam dadyn be yi tambayoyi akan auren ba

Aka gama shirye shiryen auren duk mutanen gidan suka dunguma sai kano auren sabit da asmau har da asmaun wacce sai a mota sannan mummy tai mata bayanin auren

Da yake da ƙuruciya a tattatare da ita sai ta yadda, lfy suka isa kano suka sauka a hotel ɗin tahir guest palace suka kwana

Kashegari suka kama hanyar azore, kasancewar ba a san da zuwan su ba don haka suna isa suka sauka a gidan me garin na fulanin

Suka gabatar da abinda ya abinda ya kawo su sam me garin be gane asmau ba sai da tayi bayani sannan ya gano ta

Nan da nan yasa aka kira kawun na tan ya zo shima aka gabatar masa da maganar auren

Mummg tayi mamaki da taji cewar basu suka tura hjy munnira ba da maganar auren suka ce musu su rabon da hjy munnira ma ta bada kuÉ—in aikin yarinyar har sun manta

Ko kaÉ—an dady be ji daÉ—in wannan abun ba yarinya tana aiki amma sam iyayen ta basa samun ladan aikin ta, sai da ya biya su kuÉ—i a madadin na aikatau É—in ta sannan suka kuma gabatar da aurawa É—an su asmau

Babu wani ja'inja wan mahaifin asmau ya yadda inda atake a ka ɗaura auren sabit da asmau akan sadaki mafi ƙanƙanta

Baffa wan mahaifin asmau shi aka ba sadaki amatsayin sa na uban ta, daga nan daddy ya shiga rabon kuÉ—i

Mutanen gari sai turuwa suke suna ƙara ƙaruwa kamar sallah ana cewa ai asamau ta je binni ta haɗu da me kuɗi

Baffan ya so su kwana amma sai suka kawo masa uzurin zasu koma ne kasancewar kashegari ake sa ran tasowar ango sabit 😂

Amma sai da suka ƙarasa gidan baffan suka ga gidan sannan suka kama hanyar kano inda suka sauke daddy a kano sannan suka kama hanyar abuja

Mummy kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ganin ta mallaki asmau yanzu asmau ta zama mallakin ta, kuma babu abinda zai raba ta da ita

```ni kuwa mmn walid nace anya kuwa sabit zai yadda ya zauna da baƙar mace amatsayin matar sa mutumin da baya son baƙi```

******************

Cikin hukuncin Allah sabit da badia suka dawo gida lfy sai da mummy ta kwaɓi dukkan ƴaƴan ta akan kar wanda ya faɗa masa maganar auren

Don haka ko daya sauka sam be sani ba hidimar sa kawai ya ci gaba tare da kwasar girkin wacce a yanzu take a matsayin matar sa

Itama mummyn ko da suka dawo bata ce asmaun ta bar inda take ba tunda auren ai kamar suna ne, don kawai asmaun ta zauna a nan wajen su

Sai da suka huta suka nutsu sannan mummy ta kira shi da matar sa badia da kuma asmau dukkan su ta tara su a falo

Sabit da badia da mummy suna zaune a kan kujera inda asmau take zaune a ƙasan carpet fuskan nan tata sam ba annuri don kuwa tasan kiran menene

Sai bayan da kowa ya nutsa sannan mummy tace

"sabit bayan ka tafi matsala ta taso ta yadda dole ne a aurar da asmau don haka sai nai mata aure"

Kallon mummy yayi

"yo mummy ina ruwana da auren ta ai aiki aka ɗauke ta kuma ake biyan ta idan zata iya aikin da auren to idan kuma baza ta iya ba ta ƙara gaba ai ba ita kaɗai ce ta iya girki ba sai mu nemi wata"

"ai kai ne mijin" tsab sabit yaji abinda mummy tace amma sai yake jin kamar kunne sa ne yake masa kuwwa

"mummy me kinace" bata maimaita ba face idÆ™ da ta zuba masa

"kamar naji kince nine mijin wannan abun koo" ya faÉ—a yana nuna asmau

"ashe kaji kuma wallahi da wasa ka sake ka furta mata kalmar saki wallahi sai nayi mugun ɓata maka wallahi sai kaga ɓacin raina tunda auren ka da asmau babu wanda zai taimaka sai kai

Tunda de duk Æ´an uwanka kowannen su yana da mace biyu kuma acikin biyun akwai wacce ta iya girki amma kai kana zaune da É—aya É—ayar ma wacce bata san darajar aure ba balle wani miji"

Faɗa mummy ta dinga yi ta inda take shiga ba tanan take fita ba tsab ta san halin sabit in tak masa lako lako sai ya watsa mata ƙasa a ido gwanda tai masa ta ruwan zafi in yaso duk a dafe a tare

Sabit shiru kawai yayi yana saureran mummy wannan shine wai a dake ka a hana ka kuka, ita kuwa badia tana zaune a gefe ta cika tayi fam kamar zata fashe wannan shine ga mari ga tsinka jaka

Ga kishiya ga kuma kushen ta da mummy take yi wai bata iya girki ba

"amma mummy duk a gidan nan a rasa wanda za a haɗa da wannan halittar sai ni" ya faɗa ran shi a ɓace kalmar nan ta daki asmau sosai wai halitta

Ɗagowa tayi ta maka masa harara sai kace ita cewa tayi tana son sa ai ko maza sun ƙare a duniya ya rage daga ita sai sabit baza ta so shi don ta fahimci ɗan renin hankali ne

"mummy kin san tsari na na mace ɗaya sannan kinsan ni ba me son mu'amala ne da baƙin abu ba balle wai ace matata ce baƙa" ya faɗi kalmar ```matata``` kamar wanda yake da kashi a baki

"gaskiya mummy da sake ya za ayi in shigo in kalli wannan baƙin abun a ɓangare na ai wannan ma sai ta saka ni in ta firgita cikin dare, in matsala bata sa zuciya ta bugawa ba wannan halittar zai sakani" ya faɗa yana ƙara nuna asmau cikin tsana

Asmau iya ƙulewa ta ƙule ƙarshe ita tunda take ba a taɓa ci mata mutunci ba kamar yadda sabit yai mata *shin wai baƙi muni ne* ta tambayi kanta

shiyasa fa ita tunda taji da wannan É—an rainin hankalin za a haÉ—a ta dashi shi taji sam bata san abun amma kasanceqar bata da mafita yasa ta yadda da lamarin

Sabit ya cigaba da kushe asmau kamar ba gobe inda mummy ta tsaya ta barshi ya gama faÉ—in abinda yake son faÉ—a sai daya zage ta tas sannan yai shiru yana huci

"to in banda abin auta ai na faɗa maka dalilin auren ko ba haka ba, kuma ba wani da zai haɗa ka da asmau tana can boys quaters tana aikin ta kai kuma kana ɓangaren ta me zai haɗa ka da ita, da matar ka ta iya girki shi kenan sai in raba auren itama taje ta auri wani"

Jin cewar akwai lkcn da auren zai yi expire ne kuma ga yadda tsarin auren yake na asmaun baza ta dinga zuwa ɓangaren sabit ɗin ba ya sa shi kwantar da hankalin sa

Ya kakkafa asmaun doka na in ta ganshi ta canza hanya don baya son yana cin karo da mummunar fuskar ta sannan kar ya sake ya ga ƙafarta a ɓangaren sa duk aka gama maganar kowa ga san matsayin sa sannan mummy ta sallami kowa

Sam badia ba haka ta so ba taso ace sabit ya bijirewa mummy amma sai taga saɓanin hakan

Ko da suka koma ɓangaren su sai faɗa, wai dama ƙila ya so auren ne shi yasa ana faɗa masa ya hau borin ƙarya in da da gaskene ai da sai ya saki asmau

Yai mata bayani yai mata rantsuwa amma ina sam ta ki yarda kawai sai ya share ta yayi wucewar sa É—akin sa shima yaje yaji da abinda ya dame shi
[4/17, 4:50 PM] 🥦: 👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳

*brown rice served with liver and egg sauce, Apple milkshake*

*brown rice*

*ingredients*
-shinkafa
-man gyaÉ—a
-maggi
-curry
-green beans
-carrot
-peas
-attaruhu
-albasa
-tafarnuwa

*method*

1) ki wanke shinkafar ki tas sai ki shanya ta don ta bushe, idan ta bushe sai ki É—auko tukunya ki zuba mai sosai sai ki saka tafarnuwa da albasa amma kaÉ—an

2) idan suka É—an É—auko soyuwa sai ki zuba shinkafar ki ki ci gaba da soyawa, kina yi kina juyawa har sai tayi brown sosai sai ki sauke ki tsane man

3) ki yanka attaruhu da albasa yankan cubes, sai ki zuba a tukunya da É—an mai, sai ki cigaba da soyawa, idan sun dauko soyuwa sai ki zuba ruwan da zai dafa miki shinkafar ki

4) ki zuba maggi, curry thyme da duk wani seasoning da kike so, idan ya tafasa sai ki zuba shinkafar ki tafasa É—aya sai ki zuba carrot, peas, green beans ki rage wuta, idan ya dahu sai a sauke

*liver and egg sauce*

*ingredients*

-tomatoes
-attaruhu
-albasa
-hanta
-kwai
-curry
-thyme

*method*

1) ki wanke sai yanka hanta ƙanana sannan ki tafasa ta da maggi, thyme, tafarnuwa, albasa

2) idan ta dahu sai ki sauke, ki jajjaga attaruhu, tomatoes albasa da tafarnuwa

3) ki zuba mai a kasko sai ki É—an saka masa albasa ko tafarnuwa don yayi zafi, idan yai zafi sai ki juye jajjagen nan a ci gaba da suya, a zuba maggi a cigaba

4) minti É—aya biyu sai ki zuba hanta a ci gaba da miya, idan miyar ta É—auko soyuwa sai ki matsar da miyar gefe ki zuba kaÉ—aÉ—É—an kwai a gefen da ba komai ki barshi sai ya É—auko soyuwa sai ki fara dagar gaza shi

5) idan ƙwan ya soyu sai ki haɗe shi da miya ki ɗan ƙara bata tsoro sai ki sauke sai a ci da brown rice

*Apple milk shake*

*ingredients*
1)apple
2)dabino
3)cardamon powder
4)sugar

*method*

1) ki yanka apple ɗinki ƙanana, ki cire ƙwallon dabinon ki, idan dabinon bushash she ne ki jiƙa shi

2) ki haÉ—a apple, dabino, cardamon powder amma kaÉ—an, madara da sugar sai ki markaÉ—a

3) ki saka ƙanƙara a jug ko cup ɗin da za ayi serving ki juye milk shake ɗin ki

👩🏽‍🍳 *Bon appetit*👩🏽‍🍳

*ASMA'UN SABIT*
🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛

👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳

🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠

ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)

P⃗a⃗g⃗e⃗ 9🌹
Chapter 10 · 0% Book details