Sashe 8
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
‘yar kadan ba kafafunta har mintsininta suke, ba abinda take bukata a lokacin irin ruwa mai zafi a kwami ta shiga ta wartsake wannan gajiyar zaman data kwaso, sannan ta samu ta sauke sallolin farillar dake kanta don lokacin duhun dare ya fara shigowa. Prince bai tsaya a sitting room din ba balle ya gane halin da take ciki, da bukatarta na yada kafada, tafiyar awanni 22 Siddiqah tayi a jirgi daga kasar Najeriya zuwa Ajantina. An raine shi da zama mutum mai karrama dan adam ko yaya yake, don haka tuni yasa Pareto ya shirya mata abinci mai rai da motsi a dakin tun kafin fitarsa. Kusan koda ace Prince bai da duka halin humility din mahaifiyarsa Nenne Sappa, to yafi duk sauran ‘yan uwansa mata kamanta halinta na kirki da kyautatawa mutane, yana da kula da humanity din kowanne dan adam dake zaune karkashinsa. Kai ba dan adam kadai ba har dabbobinsa da yake kiwo sun shaida karamcinsa da kulawarsa garesu. Wannan ne dalilin da yasa bai ji a ransa zai iya wulakanta yarinyar nan ba, in anbi salsala meye laifinta? Bata san shi ba, bata taba ganin shi ba ko a hoto, aka je har gaban iyayenta aka aurota da kima don haka inma da wanda zai yi blaming dalilin zuwanta katsahan cikin rayuwarsa ai iyayensa ne ba itaba. Su din kuma ya tabbata masu cikakken iko ne a kansa, sunada ikon canza masa rayuwa zuwa wacce hankalinsu yafi kwanciya da ita. Don haka ya shanye komai na damuwarsa a fuskarsa, haka ya boye bacin ransa a cikinsa, ya dawo daukan abu a kitchenette ne ya ganta har zuwa lokacin a inda ya barta, mamaki ya kama shi, ita komai sai an mata umarni? Sai ya nuna mata dakin dake gefen nasa yace. “Kiyi amfani da wanan dakin”, ba tareda yace komai ba ya bude mata dakin suka shiga, ya nuna mata wajen kunna wuta da wajen kunna room heater, da yadda zata kunna shower da tap na toilet sannan ya fita, ya dauki snacks dinda da ya fito dauka a firij yasa kai ya koma master bedroom dinsa. Yana shiga dakin tun bai kai ga zama ba kiran Dade ya shigo wayarsa. Da rashin kuzari Prince ya zauna a gefen gadonsa yana amsawa Dade, suka gaisa, ya gayawa Dade ta iso lafiya, kuma har ya daukota, tana tare dashi a ranch house already. Dade don farin ciki hamdala ya saki a fili kuma da karfi, har abin ya baiwa Prince mamaki. Sai ga Dade yanata shiwa Prince albarka kwando kwando, yana roka masa alkhairori na rayuwa, zuria mai dayyiba da falalar Ubangiji. A karshe yace “yadda yayi musu wannan biyayyar Allah ya bashi masu yi masa ninkinta da gaggawa”. Jikin Prince Abdulrasheed ya idasa macewa murus, dan sauran shirin silent protest dinsa akan zuwan Siddiqa ya karasa tsiyayewa, ya rasa wane irin son yayi aure ne haka a zuciyar iyayensa, irin addu’o’in da Dade yayi ta jero masa yau, bai taba yi masa irinsu ba, Dade ya umarceshi da ya karbi wayarta ya hada mata layi ya loda mata credit don ta rinka kiran kowa nata a Gombe dasu Nenne. Prince yayiwa Dade alkawarin tunda yanzu dare yayi tana bukatar ta huta, gobe in sha Allah zai bata daya cikin wayoyinsa dake hade, ba sai ya karbi ta hannunta ba. Ina zani Dade ya goya Prince! Don farin cikin sa ya gaza boyuwa. Bai san sanda yace. “That’s my son Kehinde! Master of all my children, the great Prince of the Ilorin Emirate!”. Ya kare wayar tasu da cewa cikin harshen yarbanci. “Nenne mhi Iya agba opeo toba se die”. Ma’ana Nenne da Kakarsa Nani sunaso zasu kirashi yanzu domin su bashi tasu albarkar. Suna gamawa da Dade kuwa Nenne ta kira, ko daga yadda take magana yau dashi a sake kasan cikin farin ciki take. Cewa take cikin Fulfulde. “Allah wanne albarka Hammansu!”. Wato (Allah yayi albarka Yayansu). Shikuma ya amsa da “Amin Nenne, Allah beddu sabbungo!”. Wato Allah ya kara girma. Sannan tace “na baiwa Aisha WARA mai yawa ta taho maka da ita, tana cikin kayanta a duba a cire a dumama”. “Godiya nake Nenne, madallah!”. Uwar da Dan cikin shaukin juna suka yi sallama, ko ince Nani Oummana ta amshe wayar ba tareda ta barsu sunyi cikakkiyar sallama ba. Cikin fulatanci Nani Oummana ta shiga koda masa halayen kwarai na AISHA-SIDDIQAH wadanda ta nakalta a dan zaman da tayi tare da ita na gajeren lokaci. Tace "bafullatanar usul ce don haka bata da tsoro saidai kunya. Kada kayi tsammanin zata dinga jin tsoronka duk shekarun nan naka idan ka uzzura mata, amma idan ka tausasa mata zata yi maka biyayya sannan zata ji kunyarka". Da wannan sukayi sallama shida Nenne da Nanin Gombe. Wayar gabadaya ya kashe ya jefa ta a tsakiyar gado, kansa har sarawa yake kasancewar yayi Magana mai tsayi, a karshe yace da kansa “so Oummana ma na son Siddiqah kenan”. Dama can bata son ya auri kabilar Babansa, ta sha fada masa yazo wajensu yayi aure ya more mata. Yanzu kuwa tunda ta samu an aura masa 'yar Gombe ai shikenan kuma kaya ya tsinke a gindin kaba. Gara ya kashe wayarsa gabadaya don yana so ya zauna ya nutsu, ya saurari zuciyarsa, ya nemi zabin Allah sannan yayi tunani mai kyau akan zuwan Siddiqah rayuwarsa, ba wanda zai sa shi nadama daga baya ba. Wanka ya fada ya sakarma kan shi shower mai dumi. Yana wanka amma yana zufa, don iyayensa sun gama daureshi da jijiyoyinsa. Da ya fito daga wankan ya zabi kayan barci farare marassa nauyi ya saka ya sha zazzafan chamomile tea dinda ya saba sha kullum kafin ya kwanta, don chamomile din yana bashi barci na nutsuwa duk daren daya sha shi. Prince ya kwantar da kai a wuyan kujerar da yake zaune yana tunanin me ya kamata yayi akan zaman Siddiqah tare dashi a gidansa? Ya duba ya hanga ya ga ko ta ina babu wata mafita bayan mika wuya ga hukuncin Ubangiji da Kuma abinda iyayensa ke so yayi, hukuncin su na karshe kenan akansa, don ga dukkan alamu basu dauki al’amarin rashin aurensa da saukin da yake zato ba, ta yadda zai tunanin mayar da ita ba tareda sunyi mummunan sabawa shi da su ba. To amma shi ina yaga lokacin zama da mace a rayuwarsa. Abar ta tsanarsu da ya riga yayi bakidayansu, da kudin goron da ya riga yayi musu na maha'inta, marassa godiya, marasa tarbiyya, marasa tsoron Allah, mazinata, masu kwadayi da rashin halacci, sannan (gold diggers). Kullum a tafe yake kamar tsuntsu daga wannan kasa zuwa waccan, in ba jela zai mayar da Siddiqah ba yaya zai yi da ita? Yadda Prince Abdulrasheed yayi kwanan zaune yana tunanin mafita da wadda zata fishsheshi, haka Aisha Siddiqah ma tayi kusan rabin kwanan zaunen akan kujerar sofa kwaya daya dake dakin da Hamma ya sauketa. Ta kusan kwana a zaune dangargar tana kewar gida da iyayenta da Nenne. Amma a karshe ta lallashi kanta ta baiwa kanta baki tunda bakin alkalami ya riga ya bushe, gata ga Hamma Prince a cikin gidansa. Ta baiwa kanta shawarar daina takura zuciyarta akan komai ko asarar hawayenta, ta fuskanci reality din dake gabanta kawai, wanda shine zaman aure na fisabilillah tsakanin ta Abdulrasheed Kehinde wanda shi Allah ya zaba mata madadin Ishaq, iyayenta suka ga shi yafi mata alkhairi akan nata kabilan, alhali sun san bata son wannan kabila ta Yoruba ko digo. Tace tunda iyayenta shi suka zaba da saninsu na cewa Yoruba dinne, ta kuma gane ko su waye kabilar yarbawa yanzu a dan zamanta dasu a Lagos da makaranta, it will be easier for her to live with this arrogant Prince. Ya kamata ta baiwa kanta farin ciki ta maida komai ba komai ba, ta kuma baiwa kanta ‘yanci a zama da Prince. Abu na farko kada ta yarda ya raina ta wai don ita yarinya ce sosai a kansa, ta girmama shi yadda Allah yace a matsayinsa na mijin ta kuma babba sosai a kanta, ta shiga duk inda take so a gidannan ai gidanta ne da aure ya riga ya bata, ta kuma cire duk wani tsoro-tsoron nan nasa wanda take dan ji a baya dalilin rashin sakin fuskarsa gareta. Zata fara rayuwarta cikin sukuni da walwala daga safiyar gobe, ta daina bari kwarjinin Prince Abdulrasheed yana yi mata dabaibayi. Saka kai a damuwa kan abinda baka da maganinsa aikin banza ne, gara ma ta nemowa kanta farin ciki da sukuni a cikin gidan, ta hanyar yin duk abinda taga zai bata nishadi. Tunda auren Baban Kiki yanzu aka fara, kuma ya zama dolen da bazata iya gujemawa ba har illa masha Allahu. Aisha Siddiqa ta mike bayan gama wannan tunanin, ta shiga bathroom ta daura alwallah sai ta kintaci inda hakalinta yafi kwanciya da cewa shine gabas, ta tada sallah, ta sauke duk sallolin da suka risketa a hanya. Sannan ta koma tayi wanka da ruwa mai zafi sosai ta sanya wata doguwar rigar barcinta sabuwa kar mara hannu da dan kauri. Ta zauna taci abinci ta koshi don yunwar cikinta kadai ta isheta kasancewar bata ci abinci a jirgi ba. Data kammala ta dauko wayarta ta saka a caji, ta ce ita kadai "bari in roki Baban Kiki ya karba ya hada min network". Amma koda ta fito don duba shi babu shi a falo bata tadda shi a sitting room din ba, ya dade da kashe wutar lantarki da duk kayan wutar dake falon ya shigewarsa dakin barcinsa. Komawa dakin tayi ta maida wayarta ta saka a caji, ta cigaba da kallon ko’ina a dakin tana tazbihi, don ita dai bata taba ganin gida mai shan kai irin Ranch House din Hamma Prince ba, wanda tun saukarta ta kudire daga yau ta daina kiransa Hamma sai Uncle AK. Ba don komai ba sai don kwana daya da sukayi yau a gida daya yasa kwarjininsa da kamalarsa sun karu a idanunta. An kashe dukiya da lokaci wajen tsara wannan gidan gonar Dawakan nashi ba kadan ba, komai na gidan daban yake daga wanda ta sani, ko ta saba gani a Gombe da Lagos. Ga caji ta samu waya ta cika full, kuma bata jin