Sashe 14
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin sitting room din. Zakin muryar Kiki mai amo kamar na marokiya da taji kamar cikin mafarki yasa ta juyowa da sauri daga gaban talbijin, sai idanunta suka sauka cikin na Kiki-Ruqayyat. Kiki saura kadan ta koma baya da gudu, don kuwa ba karamin tsorata tayi da ganin Aisha a gidan Uncle dinta Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni ba. How dare she came here? Ta ina tabi tazo har Argentina kuma gidan Uncle dinta? To me tazo yi? Me ye gaminsu? Kodai-kodai Aisha aljana ce bata sani ba, tukunnama meye hadinta da Uncle AK da zata dawo gidansa da zama? Iyakar tsorata da shiga rudani Kiki ta shigesu ta kuma firgita, mamaki ya kusan kasheta daga tsaye, sai ta koma daga bayan Prince ta dan rike rigarshi ta baya, tana buya tana lekowa kadan. “Uncle AK boyeni, kawata Aisha-Siddiqah ce take yi min fatalwa a gidanka ba don ta mutu ba”. Watakila tun zuwan Aisha gidan Prince batayi dariyar data fiddo fararen hakoranta waje ba sai yau. Da kyar Prince ya zaqulo Kiki daga bayan sa yana cewa “bana son shirme Kiki, kina nufin baki santa ba ko yaya ne? Mutuwa tayi da zata yi miki fatalwan?” Da gudu Aisha ta taho ta janyo Kiki ta karfi daga bayan Uncle ta rungumeta. Kiki na kokarin zamewa tana dojewa tana cewa. “Ba wani hugging dina da zakiyi. Ba wannan a tsakaninmu yanzu. Nayi fushi, nayi fushi sosai Siddiqah. Ki gayamin kawai saboda Allah me kike boye min haka tuntuni?” Kiki ta juya ga Baban nata cikin rudewa tace “Uncle AK, ku fiddani duhu, I am perplexed, that means Aisha-Siddiqah is your wife since?” Prince rasa amsar da zai baiwa Kiki yayi, don sosai yaji nauyin ‘yar tasa ta yadda zai ce mata kawar tata da basu fice shekaru daya ba matarshi ce ta sunnah, ba wani (age gap) ma tsakaninta da Kiki. Duk da haka yayi mamaki da bata sani din ba. Sai kawai ya zuba hannayenshi a aljihu yana kallon Kiki tana murje ido wai dai ta tabbatar ba mafarki take yi ba, Hamma ya samu hannun kujera ya zauna, ya mika mata hannu yace. “Come on my darling daughter, zo ki zauna kusa da ni, ki gayamin yaya hanya? Uncle missed you for long!”. Kiki taki zama, ta soma kukan dadi daga tsaye, tana bubbuga kafa a kasa na shagwaba don zuwa yanzu duk da bai furta ba ta gama gane komai. Cewa Kiki take daga inda take tsaye cikin kukan da ya wuce da dariya, “wayyo ni Kiki! Wayyo ni Ruqayyat! Uncle AK kawai kace min kayi aure, ashe inada rabon ganin wannan ranar? For how long akayi toh da har ni ban sani ba??? Auren ma kuma da Aishata! Itace na dade ina yi maka sha’awa fah!” Ta koma Yarbanci ziryan tana fadin “God so kind, yau da wace kalma zan godewa Ubangijina? Uncle dina yau da matar aure a cikin gidansa a Ranch dinsa?” Sai ga hawayen farin ciki na gudu daga idanun Kiki-Ruqayyat. Siddiqah ta kamota tana tirjewa ta zaunar da ita a gefenta, sai Kiki ta matsa can nesa da ita tana zumburo baki. “Daga yanzu ai nasan irin zaman da kike dani Aisha, baki daukeni aminiya yadda na daukeki ba, tunda har kika iya rufeni a bai-bai irin haka. Ni me aka dauke ni? Hayagaga rariya uwar Magana ko? Ko kuwa Aku-Kuturu sarkin zance ko? Shi yasa baza’a gaya min wannan abin alherin ‘officially’ ba aka yi ta yawo da hakalina? Aisha abokin kuka ba’a boye masa mutuwa”. Kiki mita da korafi da kyasci kamar ta ari baki, nan dai Aisha duk ta karbi laifin ta shiga baiwa Kiki hakuri itama kamar ta ari baki, tace “ai ba ni ya dace in gaya miki ba Kiki, nima kunya nake ji, a inda ya kamata a gaya miki daban Kiki ba’a nan ba. Kiyi hakuri kada ki ga laifina, to me zan ce miki ni a lokacin da kika zo Lagos? Bayan ni kaina bansan matsayina a gidan Nenne lokacin ba? Ina dai zaune ne kawai tareda Nenne. Ban kuma taba ganin Baban naki ba ko a hoto, saboda Allah me kike tsammanin zan iya ce miki akai a lokacin banyi azrbabi ba?” Kiki ta yarda da kariyar da Siddiqah ta baiwa kanta. Amma tace da Uncle dinta daga yau itama ta saka shi a bakin littafi. Tace itama daga yau ta daina masa zancen Tosin, tunda shima ya boye mata soyayyarsa da matarsa kawarta Aisha. Kiki ta ce “daga yau Aisha kece Uncle dita, kece kuma Aunty na, nayi fushi na daina Uncle da Uncle AK!”. Kai yau Hamma yaga boni da rigima iri-iri daga Kiki. Sai murmushi yake kansa a sunkuye yana latsa wayar hannunsa. Da ya gaji da mita da korafinta ya dago kai a hankali ya dubeta da manyan idanunsa tamkar ruwa ya kwanta a cikinsu. Don duk korafinnan da mitar nan da Kiki take yi kan Hamma Prince yana duke akan wayarsa ko dagowa bai yi ya kale su ba, amma tsaf yake jinta. Yana kuma murmusawa tarin kuruciyarta. Muryar Aisha dake ta kare kai kuma tana masa dadin saurare. Da kyar yace. “Kiki kinsan Uncle dinki care for you koh? Ba abinda zan boye miki wanda yakamata ki sani. Na aza kin sani. Yanzu dai duk kiyi mana uzuri, nida Uwar taki, ni banida say! Sannan banida uzurin baki”. Kuma har zuciyarsa har ga Allah hakane, ya zata ta sani, da gaske bashi da say akan lamarinsa da Aisha, tunda shima rana daya kawai ya ganta a Argentina. Bai san ta ina zai fara gayawa Kiki hakan ba, shiyasa ya kashe maganar da cewa baida abin cewa. Haka dai suka samu suka yi ta lallabata, har suka samu ta daina kuka da korafin an boye mata din. Ta koma kallon Aisha da Hamma tana ta murmushin farin ciki. Aisha ta dauki kayan Kiki zuwa dakinta, don Uncle yace ma Kiki ga mukullin nata dakin ta share kamarbata ji shi ba, tana tafiya zuwa dakinta da kayan Kiki yace “ko baki ji bane Aisha?” Aisha tace ba tareda ta juyo ba “a’ah, nawa dakin zai ishemu, a dakinta Kiki zata sauka”. Sai ya rabu dasu kawai. Da suka shiga dakin Aisha, Kiki ta kama kugu tana kallon ko’ina na dakin, taga ba’a canza masa komai ba daga yadda ta san shi, dakinda Mamanta da Nenne ke sauka a gidan ne, yana nan yadda yake sai kace ba sabuwar amarya aka kawo ba. Aishah bata lura da me Kiki ke sakawa a ranta ba a lokacin, wato dole ma Uncle ya saka ma Aisha sabbin furniture, ta tambayi Kiki ko me take son ci ta dafa mata sharp-sharp? Ko itama order din za’a yo mata irin wanda ake yiwa Babanta kullum?” Kiki ta kama baki tace “ban gane ba? order kamar yaya? Kina nufin ba ke kike dafa masa abinci ba tun da kika zo?” Aisha ta girgiza kai tace “Kiki to meye abin mamaki a ciki? Watakila ya riga ya saba dana inda yake sawa wannan Pareto din yake ko wa ya karbo masa nan kusa da mu. Maiyuwuwa ko yafi jin dadin wanda ya riga ya saba dashi dinne, bai fi sau uku ya taba cin abincina ba shima sama-sama, ko na dafa tare dashi na masa tayi cewa yake min “ya gode, he is okay!”. Kiki tace “tab! Ke kuma kika kyale shi yana cin abincin restaurant alhalin kina cikin gidansa? To zaman me kike? Meye amfaninki? Ai kawai Aisha tashi mu shiga kitchen in ma baki iya Yoruba cuisines ba daga yau ki fara koyo, don kuwa Uncle maso abinci ne baya wasa da cikinsa. Kinsan yana Polo. Duk mai Polo kuwa na bukatar abinci mai fa’idah. Daga yau kada ki kara bari a shigo miki da abincin sayarwa gida, haba Sidddiqah kada kiyi saken da Uncle zai raina min ke. Ko kin iya ko baki iya ba haka zai daure ya dinga ci har hannun ki ya fada”. “Balle ma Kiki na iya fa, duk yawancin abubuwan da ake sayo masa dinnan ba wanda Nenne bata koyamin ba”. Kiki tace “wallahi to da sake, sai mun gyarawa Uncle zama”. Sosai ta baiwa Aisha dariya. Kiki ko hutawa bata yi ba, sallah kawai tayi ta aje mayafi tace da Aisha suje su shiryama Uncle abincin dare. Wani nau’in abincin Yarbawa Kikin ta ce su yi mai suna Ewa Agoyin, da ake yi da wake, tace tasan Uncle AK na matukar son shi tun yana yaro, musamman idan yaje Ilorin sai yace Aunty Murja tayi masa shi. Kiki ce karfin aikin don Aisha bata san yadda ake yin Ewa Agoyin din ba, ta bude ido sosai tana koyo, don Aisha is a fast learner, sannan suka dora ‘Ofada rice’ da zasu hada ‘Ewa Agoyin’ din da ita. Suna girkin Kiki ta gaya mata da niyyar yin kwana biyu ta zo Argentina, amma saboda ita yanzu kwana bakwai zata yi sannan ta wuce makarantarsu a Los Angels. Siddiqa don murna kamar ta yi yaya, da jin cewa Kika zata yi mata sati. Suka kammala girkin suka kai suka jera a dining, suka gyara wajen abin gwanin ban sha’awa duk kamshin spices ya turare gidan, lokacin Uncle ya fita, ba su ci nasu ba duk da suna jin yunwa. Kiki ta ce su jira shi komai dadewar da zai yi, ta ce. Ta dinga cin abinci tare da Uncle zai zame musu hanyar samun karin shakuwa da fahimtar juna don ta fahimci dukkansu wani baya – baya suke da juna. Suna nan zaune a ‘sitting room’ suna jiran dawowar Prince har karfe takwas na dare bai dawo ba, Kiki ta soma hamma saboda gajiya, sai sannan suka jiyo motsin shigowar motarsa gidan. Prince ya shigo rike da ledar take-away dinsa na abincin dare, ga ‘Ice-Cream’ a wata ledar daban ya riko ma Kiki don ya santa da son Ice-Cream. Aka ce albarkacin kaza kadangare kan sha ruwan kasko, sai ya kasa sayo daya, ya sayo musu duk su biyun, a sannu ya isa ga dining ya dora ledojin hannunsa da ya shigo dasu. Nan ya ga abincin da aka shirya a wurin cikin tsari mai ban sha’awa. Ga kamshin turaren wuta na tashi a falon ya hade da kamshin